Sashe 189
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko da ta jefa mata tambaya kuwa Jiddah bata 6oye ba ta sanar da ita domin hankalin ta ya riga ya tashi mafita take nema, hakan yasa bata ma san lokacin da ta furta" Mummy ni shi nake so amma yace wai kar in sake 'kiran sa...".
Salati mummyn Jiddah tayi tana tafa hannuwa tace" Yanzu wai duk akan namiji kike wannan uban kukan Jiddah?"
" Mummy zagi na fa yayi wai kar na sake 'kiran sa".
" Dama an gaya miki ana 'kiran saurayi ne haka sakaka? Ai in kina so ki 'kira namiji batare da wulakanci ya shigo ba to ki bari sai magana ta zauna tsakanin ki da shi".
" Ni dai Mummy ki taimake ni, ki ce Abbah ya ro'ka min shi dan Allah mummy wallahi idan ya guje ni mutuwa zanyi".
Abbahn ta dake tsaye bakin 'kofar 'dakin nata taji yace" Waye shi?"
Zabura tayi ta maida kallon ta gare shi da rawan jiki tace
" Abbah wani ne...sunan shi Muhammad..ni shi nake so Abbah please ka taimake ni.."
" 'Dan waye ne haka?"
" Ni ban sani ba Abbah, amman dai garin su ne jihar Bauchi..mahaifan sa na zaune a wata 'karamar hukuma Shuwarin.."
" Ki bari to gobe da safe ki kawo min photon sa in gani.."
" To Abbah Allah ya kaimu, nagode Allah ya 'kara girma".
Juyawa yayi ya koma inda ya taso zuciyar sa cike da tunanin wannan abin, Jidfah ka'dai ya mallaka ba zai so 'kunci yayai wa rayuwar ta 'kawanya ba, dama tare suke zaune da Mummyn Jiddah a palourn wanda jiyo kukan Jiddan yasa ta ta shi shima kuwa take yabi bayan ta dan jin meke faruwa da tilon 'yar sa da yake matu'kar so da 'kauna.
Ashe ma batun soyayya ne, sai dai shi a ganin sa babu 'dan wani ko wata a 'kasar nan da zai yi wasa da zuciyar 'yar sa, koma waye shi dole ya nemo sa yasan matakin da ya kamata ya 'dauka akansa.
Washegari Jiddah da sassafe tana idar da Sallah ta nufi 6angaren Abban ta fuskan ta cike da murmsushi cuz tasan tunda yasa baki to kamar anyi an gama ne ta zama matar Mu'een.
Gaida shi tayi tare da fa'din Abbah ga shi nan.
Comment
Vote
Share
*Salmerh ce*😍
💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)
By
*Salmerh MD*
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy, smile, educate nd to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU MUKE TUN'KAHO*
_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
🅿 *85*
Abban Jiddah murmushi yayi yana kar6an wayar yace" Ga dukkan alamu wannan muhimmacin sa na musamman ne, rabo na da ganin ki sassafe haka har na manta Jiddah".
Kunya taji sosai sai tayi 'kasa da kanta tana murmushi.
Kallo sosai ya 'kare wa Yah Deen, domin kuwa ya fahimci shima 'din yana mai ji da kansa ne, sittirar dake jikin sa ka'dai ma ta ishe sa amsa baya ga yanayin sa, domin kuwa ba'kin suit ne ajikin sa mai shegen kyau da tsada, ya rataye farar rigar sa ta aikin likitan ci bisa wuyan sa, yayin da 'dayan hannun kuma ya sanya shi cikin aljihun wandon sa yana murmushi aka 'dauki pic 'din.
Duba 'daya zaka yi masa ka tabbatar bai taso cikin babu ba domin bai gani a yanayin sa ba, motar dake bayan sa ma yasan taji ku'di ba na wasa ba.
Idanun sa kan wayar ya furta" Wannan ba mamaki babban aiki kika samo min Jiddah, takamar dama Naira ne kuma ga dukkan alamu shima 'din cikin ta yake, to da me zamu yi masa barazana kenan?"
Ya 'karasa maganar da kallon fuskar ta.
" Abbah ka ro'ke shi kawai 'kilan zai amince idan yaga kaine dan taurin kai ne da shi sosai, nuna ku'di bazai sashi ya amince da ni ba Abbah..".
Mi'ka mata wayar yayi yana fa'din" Yanzun dai ki bari zuwa next week muga abinda hali zai yi...".
Cike da shagwa6a tace
" Abbah gobe Allah yafi ai tambaya ne kawai..."
Idanu ya zaro yana duban ta da tsananin mamakin ta" Kina nufin tambayar auren ki zamu je a wurin mijin?"
Sai yanzu ma maganar tata ya sata kunya jin kunya, 'kasa tayi da idanun ta tana dan kwa6a fuska tace" a a Abbah I thought...maganar fahimta za'ayi...kaga sai asa ranar da za'a fara shirin tar6ar su..."
Cikin ransa yace ikon Allah..zama ni.
A fili kuwa cewa yayi
" Kar ki damu zan yi tunani akai tukunna inga ta inda ya kamata a fara"
Tuni farin ciki ya mamaye ta, fara'a ne sosai ya bayyana kan fuskar ta, tana murmushi ta furta" Thank u Abbah na, Allah ya bar min kai har 'karshen rayuwa ta".
*****
Washe garin zuwan sa da safe lokacin da zai je gaida Alhaji Baba sai ya tafi da takaddar sakin Noor da ya rubuta yana gaida shi ya amsa a tsanake batare da ya wani bada hankalin sa gare shi ba..Yah Deen sam bai jin da'din yanda iyayen sa suka 'dauki abin da zafi har hakan, a yanzu burin sa bai wuce yaga sun dawo kamar baya ba, rabon da yaga fara'a kan fuskar iyayen nasa har ya manta, 'kara ma idan suna tare da 'yan biyu ko kuma idan suna waya da su a lokacin ne zaka tsinci fara'ar ya'ke akan fuskokin su.
Kan ninkakkiyar takaddar dake hannun sa ya sau'ke idanu, sai yaji ya karaya sosai, yau ga takaddar sakin Hudah ri'ke a hannun sa, abinda ko cikin mafarki bai ta6a tunanin faruwar sa ba..." Allah ka bani ikon jurewa".
Cikin zuciyar sa ya furta hakan yana me sakin numfashi.
Ta shi yayi daga inda yake zaunen ya matsa kusa da Alhaji Baba da hankalin sa ke wani wurin daban, hannu biyu yasa ya ri'ke takaddar da shi sannan ya mi'ka masa yana sunkuyar da kansa yace" Alhaji gashi na rubuta"..batare da wani dogon bayani ba kawai yayi shiru daga hakan.
Alhaji Baba bai yi musu ba ya sa hannu ya kar6a yana sake duban fuskar sa lura da sauyin yananyin dake tattare da shi a lokacin.
" Takaddar mecece wannan kuma?"
Tambayar da yayi masa kenan yana yatsina fuskar sa kamar be san abinda takaddar take nufi ba.
Sai yanzun ya 'dago ya dubi Alhaji Baba, da raunin murya ya bashi amsa da fa'din" Takadda ce Alhaji...takaddar sakin...mata..ta".
Baki Alhaji Baba baki ta6e yanavmurmushin gefen baki, sai a wannan lokacin kuma ya fara warware takaddar yana fa'din" Kayi kyan kai ai...Allah ya ha'da kowa da rabon sa".
Daga haka yayi shiru idanun sa kan papern da alamu karanta abin ciki yake yi.
Baki ya sake ta6ewa yana ninke papern bai 'dago ya sake duban Yah Deen ba kawai ya mi'ke tsaye wanda ganin hakan yasa shi niyyan magana.
Kansa ya sosa sannan ya 'dan 'dago kansa" ...am dama Alhaji nace..." sai kuma yayi shiru.
Waigowa Alhaji Baba yayi yana duban sa da 'daurarriyar fuska yace" Me kace?"
" Alhaji dan Allah kayi ha'kuri ka yafe min 6ata ma da nayi, wallahi ni kaina nasan ban kyauta ba amma na tuba Alhaji dan Allah ka yafe min, bazan iya juran dogon fushi daga gare ku ba....".
Alhaji Baba bai ma bari ya 'karasa maganar ba ya dakatar dashi da fa'din" Ai dama ni ban ri'ke ka a raina ba...me ma yasa zanyi hakan? rayuwa ce kuma kowa shi ke za6ar ma kansa irin wacce ya ga dama..so waye ni da zan ce ga yanda nake kayi taka rayuwar..."
Yasan magana Alhaji Baba ya fa'da masa, duba da yadda yake fitar da maganar 'dauke da 'dacin zuciya, yana jin ciwon hakan cikin ransa amma ya daure ya basar.." Alhaji idan kace haka tamkar ka ware ni cikin 'ya'yanka ne..idan kace kai baka kai matsayin da zaka canza min rayuwa ba Alhaji to waye zai maye gurbin ka...na riga na gane kuskure na Alhaji kuma tsakani na da Allah na tuba, insha Allahu bazan sake baka kunya ba, da iznin Allah abubuwan da suka faru abaya bazasu sake faruwa ba..Ka dubi girman Allah Alhaji ka yafe min..ka ji 'kaina ka bani daman da zan gyara lahira ta tun yanzu..."
" Allah ya yafe mu gaba 'daya".
Abinda kawai Alhaji Baba yace kenan amma Yah Deen ya dinga zuba masa godiya yana yi masa addu'ar Allah ya 'kara girma da 'daukaka...cike da jinda'di.
Haka ya tashi ya fita yana jin wani sashe na 'kullin dake cikinvzuciyar sa na kwancewa, wani farin ciki yake ji marar misltuwa.
A lokacin Ammi na kitchen ne dan haka 'dakin sa kawai ya koma ya kishingi'da yana jin wani iri cikin jikin sa, godiya yake ga Allah daya nuna masa wannan rana, ranar da mahaifin sa ya sassauto fushin da yake yi da shi...a hankali tunanin sa ya gangara wajen Noor...lumshe idanu yayi yana tuno ta da yanayin ta, sanyin jikin ta, sanyin halin ta, komai nata mai sanyi ne ita, sosai yake jin wani sabon babin 'kaunar ta na sake bu'duwa masa...baya jin zai iya sake rayuwa da wata macen in ba Noor in sa ba....
Tuno cewa ashe fa yanzu ita ba matar sa bace ya sanya shi jin wani fargaba da tashin hankali.
Cikin ransa ya ayyana" Da hannu na na datse igiyar aure na da Nuree...yanzu ba matsayin.mijin ta nake ba."
Ya 'karashe maganar yana mai 'dago hannun sa na dama yana dubawa kansa ya 'dora hannun ya us cikin gashin kansa yana lumshe idanu..yayin da bugun zuciyar sa ke 'kara hauhawa fiye da baya.
Shiru yayi yana sake tunanin makomar rayuwar sa idan akace babu Noor a ciki.
Bai ta6a sanin girman 'kaunar da yake mata har ya kai hakan ba sai yanzu da yaga take neman kubce masa, yanzu ne yasan girman muhimmancin da take da shi cikin zuciyar sa.
Erh da kansa yasan yana son Noor da jimawa tun ba yanzu ba amma bai yi tunanin abin nasa ya girmama har haka ba, ashe ganin ta da yake yi kusa da shi ne ya sa ya kasa gane muhimmancin ta na asali da ke zuciyar sa.
Yana jin lokacin da Alhaji Baba ya fita, sai a lokacin shima ya tashi ya isa parlour wurin Ammi.