← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 211

Sashe 2

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jas shiru tayi kamar mai tunanin wani abu sai da uwar tasake tambayar ta a 'dan tsawace sannan ta bu'di baki tace bu'di baki tace
"Sa......."

Bata 'karasa ba ringing 'din waya ta ya 'dauki hankalin su gaba 'daya inda atake suka kai duban su kan wayar.

Cire hannun ta tayi daga fuskar 'yar yarinyar sannan ta kai hannu ta 'dago wayar.
Picking call 'din tayi ba tare da tayi magana ba kawai ta ha'da yarinyar da wayan tare da fa'din " Daddy kin ne"

Yarinyar najin haka tayi saurin kar6an wayan tace " Daddy.... i missed u when ar u coming back?"

Murmushi mai sauti yayi sannan yace " gobe insha Allahu Diamond zan dawo kinji? Me zan kawo miki?"

Ta6e baki matar tayi jin abinda ya fa'dawa Jas 'din, ita lokuta da dama tana mamakin Deen yanda ya 'dauki buri, kula da so gaba 'daya ya 'daura akan yarinyar nan, duk dama ita ta haifa abinta amma is too much...ace tana matsayin matar shi amma ya kasa sanar da ita cewa zai dawo gobe sai dai wa 'yar yarinyar nan nan zai fa'da...
"Hmm"
tace a fili tare da cigaba da sauraran su.

Jas kam cewa tayi
"Daddy ni dai ka dawo kawai"

Sai yace " zan dawo ai Jas da iznin Allah amma me kike so in kawo miki?"

Jas cewa tayi
" Ni ba komai Daddy... gurin Grandpa nake so muje kawai"

'Yar dariya yayi daga 'dayan 6angaren sannan yace
" To shikenan bari idan na dawo insha Allahu zamuje kinji Mama na?"

"To Daddy sai ka dawo"!

"Gud girl....ina Mummyn taki ?"

Mi'kawa Mahaifiyar ta wayan tayi tana murnar Daddyn ta zai dawo suje 'kauye fuskar ta cike da fara'a.

'Bangaren mahaifiyar tan kuwa tana ha'da wayar da kunnan ta taji shi yana fa'din
" Nuree i ll be back tomorrow kinji?"

"uhum" tace da shi a takaice.

Daga haka suka yanke 'kiran kuma sanadin da kenan ta manta da tambayar Jas 'din a salin me ya samu bakin ta saboda wayar da Deen 'din yayi gaba 'daya ya 'dauki hankalin su kowa da abinda ke ranshi .

Ita tana tunanin halayyar mijin nata ne yayin da Jas ke murnar zata je wurin su Granny.

Zuwa tayi ta watsa mata ruwa ajikin ta tare da 'debo mata abinci.

Sam koka'dan bata kishi da 'yarta domin bata da hujjan da zatayi hakan, amma wani lokaci abinda Deen keyi na matu'kar bata mamaki atimes kuma haushi yake bata yanda yake matu'kar fifita Jas a kanta bisa komai.

Yes tasan 'yar sa ce mafi soyuwa a gareshi musamman da yake ya 'dan yi shekaru a 'kalla biyu batare da ya haihu ba sannan ya same ta kuma daga itan har yau bata ko 'kara yin 6ari, amma hakan ai ba dalili bane da zai ce zai ringa fifita Jasmeen ya kuma fifita soyayyan ta akan na kowa ba, kuma ma har da ita data yi na'kudan ta ya maida ta banza a kanta, duk da tasani cewa ita kanta shaida ce akan irin son da Deen yake yi mata amma compare to soyayyar Jas kam tana ganin nata 'din ba komai bane, saveral times tana yi masa uzurin cewa dan itan gudan jinin sa ne shiyasa yake hakan, itama tasan cewa abin alfahari ne ace ka haihu kuma uban ya matu'kar nuna farin cikin sa game da abinda ka haifan tasan da akwai birgewa da faranta ran mahaifiya hakan amma atleast itama yana 'dan sauraran ta mana....bata da yanda zatayi dashi dan haka ko yanzun ma sai ta saka cikin ranta cewar Jasmeen gudan jinin sa ce kuma dole ya 'kaunace ta fiye da komai.

Abaki tayi ta bata abincin har ta 'koshi sannan ta sata agaba sukayo alwala suka sallaci azahar daganan sai ta fara gyara mata kitson rubber band dake kanta da haka hartayi bacci sannan ta barta.

_Comment_
_Vote_
_Share_

*Salmerh ce* 😍
[11/17/2019, 9:33 PM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Labarin nan 'kir'kirarre ne, banyi shi da sunan wani ko wata ba dan haka duk wanda yaji yayi kama da wani abu na rayuwar sa ya sani cewa co-incidence ne babba ma kuwa.... dan haka ayi amin afuwa dan Allah ba da niyya nayi hakan ba.*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *2*

'Karfe uku kusan da rabi Jas ta tashi a baccin, inda mahaifiyar ta tayi 'ko'karin ganin ta shirya ta cikin hanzari zuwa makarantar islamiya dake bayan layin su ganin ta makara lokaci yaja, bata fiya son tana missing makarantar ba da sai tace yau 'din ta bari kar tace amma kuma ba laifi yarinyar akwai 'ko'karin 'daukan hadda idan anyi musu, shiyasa uwar tafi so kar tayi fana yawan fashin zuwa sosai ta ke matu'kar 'ko'kari wajen ganin ta kula da karatun nata.

Jas 'din ce ma yau 'din take 'dan rigimar ita bazata je islamiyar ba, amma da ta ta lalla6a ta sai ta samu da 'kyar ta amince zata je 'din amma wai sai dai Maman nata taraka ta.

Kwafa tayi tana kallin ta sannan tace " haba Jas ni kuma in rakaki? Baki ga ko sallah banyi bane?

Kafa'da Jas ta 'daga da damamman fuska take shirin yin rigima.

Sai ta janyo ta jikin ta tace " yi ha'kuri mamana watarana zan rakaki kinji...ki bari yau zan dafa miki abinci kafin ki dawo wannan irin na T.Vn nan kinji?
Murmushi tayi tana kallon maman nata.

Sai ta sake fa'din
" Yauwa maman Daddy....Hauwa ta rakaki ko?

Sai ta 'dage kai sama alamar "ehh".

Murmushi matar tayi sannan ta 'kwala 'kiran mai yi mata aikin tace ta raka Jas makarantar islamiyar su inda ta 'kara da fa'din kar su 6ata lokaci a hanya saboda tayi late sosai.

Amsa mata yarinyar tayi tare da kama hannun Jas 'din suka fita daga parlourn.

Hauwa yarinya ce matshiya da bazata haura 15yrs ba ba laifi tana da kyaun ta daidai gwargwado sannan baza'a 'kirata ba'ka ba tana haske, ta kan 'dan taya Noor aikace-aikacen gida irin su Wanke-wanke, sharan cikin parlour da mopping har ma da haraban gida.
Sannan tana wankin uniform da socks 'din Jas kullum boko da islamiya duk dama Uniform 'din tana da kusan kala uku-uku amma bata son a dinga ajiye su da datti shiyasa take sawa a wanke su kullum.

Jas ba gwanar surutu bace sam, yarinya ce 'karama amma abubuwa dayawa takan bisu da idanu ne kawai, surutun ta yakan zo mata ne lokaci-lokaci, sai dai kuma ko idan tana tare da mahaifinta wannan kam har sai ka gaji da dajin surutun ta idan suna tare dan shi da kansa yake koya mata ma surutun za'ace cuz a kullun biye ta yake yi a komai baya takurata ba kuma yason ganin ta zauna shiru 'din nan, a fa'dar sa wai yafi son ya dinga ganin walwalar ta koda yaushe.

Sa6anin mahaifiyar ta kenan dan ita kam bata barin ta yawan surutun nan, itace mai yawan kwa6an ta sau tari zata bu'di baki da niyyan fa'dan magana amma sai uwar ta dakatar da ita wanda hakan yake tilasta mata yin shiru har abin ya wuce.

Suna fita daga gidan ta warware kamar ba ita ba suna tafiya hannun ta cikin na Hauwa suna 'dan hira ka'dan-ka'dan.

Daf da 'karshen layin nasu suna shirin fita daga layin suka ji an danno musu horn daga bayan su, a tare suka waiga dan ganin kowaye ke yin hakan.

Ga mamakin su sai suka ga Sani driver ne inda ya 'karaso gefe da su yayi parking yana wani murmushi tare da 'dagewa Hauwa gira.

Hauwa kam saurin kauda kanta gefe tayi a ranta tace " d'an iska kawai".

Ganin Hauwa ta kauda kai sai ya dawo da kallon sa kan Jas yace
" Jasmin makaranta za'aje ne?"

Kai Jasmin ta 'daga masa alamar "ehh"

Baki ya washe yace " babu nisa kun ma iso badan haka ba dana kaiki ko?"
Jas bata kula shi ba sai ta juya ta kallo makarantar kawai.

#20 ya ciro ya mi'ka mata yace " gashi ki sayi sweet ko Jasmin?"
Yana dariya ya mi'ka mata wanda yasa ta kalle shi tare da kallon ku'din.

" kar6i mana"!
Ya sake maimaitawa da 'dan 'karfi.

"Daddy ya hana ni ri'ke ku'di "
Tace dashi tana kallon shi.

Sai yayi dariya yace " kar6i abinki ki kashe.....ai Daddyn bazai sani ba kinji?"

A hankali ta matsa ta sa hannu ta kar6a tare da fa'din " nagode"
Hauwa matsawa tayi taja hannun Jas da sauri suka fara tafiya tana tuttura baki gaba suka barshi a gurin.

Kwafa Sani yayi tare da cizon lips 'din sa yabi bayan su da kallo.

Jan motar yayi zuwa saitin su ya 'dan tsaya tare da le'ko kai yace " ki yi mata a hankali fa Hauwa dan wannan da kike gani tafiki daraja ko awaje na ma balle a gun iyayen ta".

Yana gama fa'din hakan yaja motar yayi gaba abinsa yana sakin murmushi.

Hauwa hararar bayan motar tayi a fili tace " kai kasani ai banza 'dan iska kawai".

Bata bar Jas ba har sai da ta dangana ta da 'kofar shiga makarantar islamiyar tasu kafin ta juyo tana yi mata bye-bye ta dawo gida.

Koda ta dawo ma Sallah tayi tare da fara aikin ta na yamma wanda bata jima da da fara aikin ba sai ga Sani ma ya shigo da sallamar sa hannun sa ri'ke da leda ga dukkan alamu ma ashe aikan sa akayi shine ya tsaya yi musu iyayi a hanya.

Suna ha'da ido da Hauwa sai ya 'dage mata gira da yake ita ka'dai ce a parlourn lokacin tana kammala shara tana mopping parlour wanda jin sallamar tasa ne yasata 'dagowa sai kuma yai mata signa.

Ita kam 'kasa tayi da kanta taci gaba da aikin dake gaban ta tare da sakin tsaki cikin ranta.

Sai ji tayi yace mata
" ina matar gidan".

Shiru tayi kamar bata jishi ba.

Sai da yasake maimaitawa kafin tace masa " tana ciki"

'Kasa-'kasa tayi maganar kamar bata so.
Chapter 2 · 0% Book details