← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 211

Sashe 18

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hatsari na biyun shine ya faru ta sanadin rikicewar Sani sakamakon rashin gaskiya da kuma jin 'karar hatsari na farkon sai gashi mota tayi kaca-kaca 'kar'kashin gini bazaka ta6a zaton an rayu cikin motar ba, shi kansa mai ginin ba 'karamin tafka asara yayi ba.

Wanda suka gwabza da Sani ne ka'dai nashi da 'dan sau'ki domin kuwa gaban motar ne ka'dai ya lalace da yake shi cikin hayyacin sa yake so sai yayi saurin yin baya lokacin da suka yi karon, shi kuma Sani garin kaucewa ne ya karkace yayi gefen hanya, wancan bawan Allah kuwa da ya ka'de mai baro motar sa bata samu ko 'kwarzane ba amma azumi sittin da ya hau kansa matsayin sa na musulmi ma ka'dai ya ishe shi fargaba.

Dr. Safwan abokin Deen ne ke wucewa shima da shirin sa na zuwa aiki cuz aikin rana yake yi a lokacin, sai shima yaja ya tsaya ganin faruwar lamarin, wanda ganin mutane an taru da 'dan yawane ya sashi shima yayi parking domin ganewa idanun sa.

Har ya iso 'din kuwa babu wanda ya kai ko da farcen sa kan wanda aka ka'de 'din, tsayawa sukayi suna kallon yanda jinin sa ke malala a 'kasa kamar ba mutun ba.

Dr. Safwan na isowa ya kutsa tsakankanin mutanen wanda shine ya duba wanda aka ka'de 'din yaga tuni rai yayi halin sa sai ya jijjiga kansa tare da fa'di wa wa'danda suke wurin.

Kafin wasu 'yan mintina guri ya sake cika ma'kil da jama'ah na ban mamaki, inda wasu suka maida hankali kan motar da gini ya zubzowa.

Dr. Safwan kam shirin komawa mota yake yi cuz bai lura da 'dayan motar ba, jin hayaniyar mutane agurin ne ya sashi waigowa yaga mai suke wa hayaniyar.

Caraf sai idanun sa suka yi arba da motar Deen abokin sa wanda matu'kar yana gari to da ita yake zuwa ko'ina idan zashi.

Tsinkewa zuciyar Dr.Safwan tayi sai yayi hanzarin tafiya da gudu izuwa wurin motar ya tarar da mutanen dake wurin suna hayaniyar ta inda zasu fara taimakon mai motar.

Sanin da Dr. Safwan yayi cewa Deen baya gari ne ya sanya shi tunanin cewa Noor ce cikin motar sai da ya isa daf kafin ya ganewa idanun sa kasancewar tuni glashin ya tarwatse.

" Innalillahi Jasmine". ya furta a fili tare da 'ko'karin taimaka musu.

Da taimakon Dr. Safwan aka fitar da su duk daga cikin motar inda ya sanar da jama'ar gurin cewa 'yar sa ce tare da nuna musu I.D card 'din sa na aiki da addreshin asbitin da yake aikin saboda kada su zarge shi.

Cikin motar sa aka sanya Sani, yayin da shi da kansa ya rungumo Jasmine ya isa motar da ita, wani dake gurin ya ro'ka akan ya taimake ya ja su zuwa asbiti sai yace bai iya mota ba.

Wani aka nemo ya jasu zuwa asbitin cuz Dr. Safwan baya jin zai iya tu'ki a dai-dai wannan lokacin.

Dukkan su Emergency ward akayi da su inda aka rufu akansu ana basu taimakon gaggawa.

Har alokacin kuwa cikin su babu wanda ya farfa'do balle su san halin da ake ciki.

Dr. Safwan da kansa ya duba Jas yayin da wani likitan ya duba Sani.

Sosai suka yi 'ko'kari wajen ganin sun shawo kan lamarin, cikin sa'a kuwa komai ya dai-dai ta wanda sai a lokacin hankalin Dr. Safwan ya kwanta ganin cewa dukkan su suna da sauran numfashi.

Sani ne dai sai aka sanya masa oxygen, ga kuma mummunan raunin da hannun sa yayi harma suna tunanin sai an yanke hannun gaba 'daya.

Ajiyan zuciya Dr.Safwan yayi jin abinda ya faru da Sani sai yace " Allah ya bashi lafiya"
Nan yayi musu bayanin cewa ai 'yar Dr Mu'een ne da drivern gidan sa, yace ga dukkan alamu daga makaranta ya 'dakko ta sai hakan ya faru"

Likitoci uku dake tare da shi 'din sosai suka tausaya tare da 'kara bada himma sosai wajen kula da su.

*****

Noor dake can gida kuwa zuwa yanzun har ta fara gajiya da duba agogo, har ta gama shirin ta tayi sallah amma har yanzu shiru, lokacin da ta 'daya ta gota har da rabi ne sai ta ji wani tu'ku'kin ba'kin ciki ya 'karu mata akan na baya.

Yanzun kam tana ganin cewa rainin hankalin Sanin da gangan ya keyi, in ba haka me ya tsaida su har wannan lokacin basu dawo ba.

Tayi tunanin 'kiran sa amma kuma bata 'kaunar sake ganin wayar tama a idanun ta, tsakin da ta ringa ja yafi cikin container daga 'karshe sai ta fito parlour, amma instead ta 'dauki wayar tata ta 'kirashi " ah ah.....sai ta kauda kai daga kallon wayar ma gaba 'daya ta zarce waje.

Wurin Mai gadi ta nufa tace da shi " har yanzu Sani basu dawo bane wai?"

"Ehh Hajiya, gaskiya basu dawo ba nima ina mamaki yau 'din"
Yayi maganar cikin bata girma matsayin ta na matar ubangidan sa.

" k'ira min shi mana please Bala kaji ina suka tsaya"
Tace dashi cikin dakewa tare da 6oye damuwar ta.

Batare da 6ata lokaci ba mai gadi ya 'kira layin Sani amma switch off aka ce dashi " Hajiya wayar a kashe".
Ya fa'da tare da raba wayar da kunnan sa.

Noor sai tace
" Sake gwadawa mana dan Allah ba mamaki matsalar network ne"

Koda ya gwada 'din kuwa still baya tafiya wanda wannan karon kam ba sai ya bu'di baki yayi mata 'karin bayani ba, kasancewar a speaker ya sa wayar.

'Dan 'karamin tsaki Noor ta ja tare da yarfe hannu sannan ta juya ta koma ciki tana mita cikin ranta.

Tana shigan ta sake jiyo rurin wayar ta karo na abinda bazata iya tunawa ba.

Zaton ta ko Sani ne ya 'kira dan haka sai taje inda take jiyo rurin wayar ta kalla, ganin sunan wanda ke 'kira ne ya sanya ta ta6e baki tare da wucewa abinta ciki.

Deen kam tun safiyar yau daya gaisa da Jas bai sake jin natsuwa ba wanda hakan ya sanya shi yake zaune a office ko mutun 'daya bai iya ya duba ba.

Bai san dalilin da ya sanya ta 'kin 'daga wayar sa ba wanda da farko ya zaci ko bata kusa ne, amma daga baya da ya 'kara 'kira bayan kusan hour guda still yaga batayi picking ba, daga nan ne ya fahimci cewa da gangan ta'ki 'dagawa.

Dan haka sai ya cigaba da 'kira tare da tura mata text har guda uku amma shiru ba replay sannan 'kiran sa har alokacin bai samu response ba.

Ganin haka ne yayi tunanin ko de ba lafiya ba, dan haka sai ya 'kira mai gadi ya tambaye shi matar sa tatafi makaranta ne sai maigadi yace "a ah tana ciki"

Ro'kon sa yayi akan ya duba masa ko ba lafiya ba dan yata 'kiran layin ta amma ba'a 'dagawa.

Wannan abin ya faru ne bayan fitar Sani izuwa 'dauko Jasmine daga makaranta.......koda mai gadi yaje mata da batun ma 'kin amsan wayar tayi tace dashi ita lafiyar ta 'kalau wayar tata ce bata san inda ta jefa ba.

Mai gadi na 'ko'karin juyawa ya fita ilsai ga 'karan wayar tata daga kan kujera, kallon ta yayi ya kuma kalli inda wayar take......Noor kuwa kauda kai tayi tamkar bata san meke faruwa ba kawai ta koma bedroom abinta.

Fita mai gadi yayi wanda tun ma kafin ya gama barin cikin parlourn wayar sa ta sake ruri.

'Dauka yayi yace " yalla6ai tana nan lafiya...wai wayar tata ce bata gani ba amma yanzu ta ganta".
Ya fa'di hakan ne da tunanin babu mamaki yanzu ta 'dauki 'kiran.

Godiya Deen yayi masa tare da kashe wayar sa, bai sake 'kiran maigadi ba kawai yaci gaba da 'kiran nata wayar amma har yanzun dai bata canza zani ba.

Barin office 'din yayi kawai ya koma gida ya fara shirin tahowa Bauchi, abokin sa da ke aiki a airport ya sanya yayi masa booking cikin sa'a ma sai ya samu 'karfe 'daya da rabi jirgin zai tashi, sosai yayi murna da hakan kuwa wanda kafin kace kwabo har ya isa filin jirgin.

'Karfe 'daya da ashirin yana cikin jirgin har ma ya fara haramar kashe wayar sa, sai ga 'kiran Dr. Safwan ya danno.

Kamar ba zai 'daga ba sai kuma dai ya 'daga dan sun 'dan kwana biyu basu gaisa ba.

Jin abinda ya sami 'yar sa daga bakin Dr. Safwan ne ya sanya gumi karyo masa nan take ha'di da bugun zuciya.......a fili ya furta salati tare da tambayar yanayin jikin.

Dr yace masa da sau'ki sai godiyan Allah domin nata abin bai yi tsanani ba kamar na Sani"

Cikin ransa yayi hamdala tare da tambayar " Noor ko tana wajen ne?"

Sai Safwan yace " ah ah, bama ya tunanin tasan abinda ke faruwa"

Deen bai bi ta kan hakan ba sai ya tabbatar masa da cewa ai shima yanzu haka yana cikin jirgi zai sau'ka nan bada da'dewa ba, ha'di da yimasa godiyan kulawa da yayi da su.

"Haba bakomai kar kadamu da wannan please"
Safwan ya fa'di tare da tsinke wayar shi.

Tun lokacin hankalin Deen ya kasu gida biyu har ji yake tamkar jirgin ma ba ya sauri, duk kuwa da cewa shi da kansa ya san da bambamci in da ace mota ce.
Amma yanda ya 'kagu ya gansa gaban iyalin nasa ya sanya har yake raina tafiya irin ta jirgi.

Daga 'karshe rintse idanu yayi ya kwantar da kansa yana addu'an Allah ya takaita masa Allah ya bawa Babyn sa lafiya mai 'dorewa.

*Sani ya aikoni yace a sanar da ku cewa kunnuwan sa a toshe suke* 🎧 *haka ma idanun sa😎, dan haka* *ba zaiji komai ba kamar yadda ba zai gani da idanun sa* *ba.*

_Comment_
_Vote_
_Share_

*Salmerhn ku ce*
[11/24/2019, 1:09 PM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
Chapter 18 · 0% Book details