← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 211

Sashe 126

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Bazaki ba".
Haka kawai ya fa'di atakaice sannan ya juya ya gyara kwanciyar sa ya juya min baya.

Ni kam jiki na sanyi 'kalau na shige ciki, da uniform 'din na fa'da kan gado ina hawaye..bana so ya ji 'karan kukan nawa ballantana ya daka min tsawa...danbhaka sai.kawai ma ringa hawaye ina sjare abina.

Sam zama cikin gidan nan ya ishe ni sosai, ban kuma san yaushe zan gama ba, ban san amfanin kawo ni nan da akayi ba aka hanani zuwa ko ina, bansan laifin da nayi da yasa hukuncin takunkumi irin wannan ya hau kaina ba....gani nake yanzu kowa ya daina so na ne ma shiyasa suka share ni.

Hatta Baban mu inaso inyi magana da shi amma duk babu dama.
Bacci ne ya yi agaba dani a hakan cike da 'kuncin zuciya.

*****
     *Bayan wasu kwanaki*
Tun da muke da Yah Deen bai ta6a ko kwatanta nema na da wani abu ba balle yaga 'kwazo na ko kuma lalaci na ba...amma abin takaici ina cikin barci ranar wata Lahadi tsakanin sallar azahar da la'asar kamar ance da ni in farka sai ji nayi yana fa'din"....No karki damu gidan ai akwai mace yanzu, babu wanda zai zarge ki".

Ban san me akace dashi daga 'daya 6angaren ba haka kuma bansan farkon maganar tasu ba sai ji nayi kawai ya ajiye wayar.

Ban wani sa maganar tasa aka ba balle inyi tunani akai, ina nan ina kwancen kafin nayi wani yun'kuri sai naji motsin sa har ya shigo bedroom 'din.

Maida idanu na nayi na lumshe kamar mai bacci...ban bu'de ba kuwa har ya gama abinda zaiyi ya fita.
Sai da na tabbatar ya fita sannan na tashi nima na cire kaya na na fa'da bayi dan 'dauro alwala.

Sai da na sallaci La'asar da naji ana 'kira kafin na nufi kitchen dan neman abinda zan sawa ciki na cuz na fara jin yunwa a lokacin... maganar da naji yana yi 'din bai kuma zuwa kaina ba.

*****
    Yah Deen sai yamma ya dawo gidan lokacin ina 'ko'karin ha'da mana abincin dare...daga sannu babu abinda ya sake ha'da ni da shi ya wuce ciki.

Daf Maghrib sai muka ji sallama daga 'kofar gida.

Jin muryar kamar ta manya ne ya sani saurin fitowa ina amsawa yayin da Yah Deen dake parlour ma ya fito da sauri jin muryar abokin sa Imrana dan sam bai sanar da shi cewa zai zo ayau 'din ba.

Da ganin Yah Deen Imrana sai ya saki dariya sannan ya waiga ya kallo wa'danda ke tsaye gefe da gefen sa...sannan ya kalle ni...kan YahcDeen ya maida idanun sa daga 'karshe.

Ni dai bance da su komai ba ganin ba ni da ala'ka da su ya sani kowa cikin kitchen na cigaba da aikin dake gaba na.

Yah Deen na shirin 'karasawa gaban su dan su gaisa sai Imrana da rikitacciyar muryar sa irin ta 'yan wiwi yace" Bahba ashe fa sa'a ce da mu...ya akayivhakan ta faru banda labari?...kasan da jimawa labari ya iske ni cewa an kawo gara gidan ka..shab sai na manta da batun, ko munyi waya da kai ban tunawa, haka kaima baka yi min zancen ba, yau da dawowa ta su shadow ke sake tunamin maganar al'kawarin da muka yi da kai kasan harda su na yiwa magana a lokacin da kace in gayyato abokaina, ashe su sun saka rai sosai shine fa suka saka ni gaba wai sai munzo yau ashe kuwa gaskiya ne da zuwan mu sai gata...."
Ya 'karashe maganar yana 'yar dariya.

Turus Yah Deen yaja ya tsaya yana wani 6ata ransa...ji yayi tamkar ya hau Imrana da duka saboda takaici, take yaji ransa ya 6aci har canza launi idanun sa suka yi.

Cike da takaici yace" Ban son hauka ni Imran, hala ka manta ne ko? ba ni da kai muka samu labarin an fasa auren bane...ko tsabar ka raina min hankali ne ya sanya ka 'debo min wannan shirgin kuka zo min gida dan ka tabbatar min da cewa baka da hankali ko?..idan auren zanyi zan 6oye maka ne...dallah ku fice ku bar min gida...".

Zaiyi magana Yah Deen yayi saurin 'daga hannu ya dakatar da shi" Wannan 'din ce baka gane ta ba ko me? yarinyar Ammi ce fa kuma amanar ta Alhaji ya bani"..

" Kenan kai 'din darasi kake 'daura mata ko?"
'Daya daga cikin su ya fa'di wanda ganin sa ka'dai ya isa ya tabbatar ma da cewa a bige yake 'dif bada wasa ba.
" Ban sani ba mahaukatan banza kawai".
Wannan karan a fusace ya bada amsa.
Imran ma zai sake magana yana nuna kitchen 'din da nake ciki kafin fitowar maganar tasa Yah Deen sai ya cusa hannun sa 'daya cikin aljihu tare da dakatar da shi cikin tsarewa da fa'din" Ku bar min gida".

" Gaskiya Deeni ka iya yawa...wallahi wannan yawane".
Fa'din shadow da tunda suka zo bai furta komai ba sai yanzun.

Juya wa sukayi duk suka fice suna tanga'di tare da buga 'kofar gidan da 'karfin gaske.

Yah Deen ya 'dauki a 'kalla kusan mintina goma yana tsaye idanun sa tun 'dazun na kan 'kofar da suka fita, ko a kwatance baya so ya 'kiyasta Hudah da wa'dannan 'yan iskan...dama Husnah ce ya tabbata ko kwana zasuyi zai iya bar musu ita amma wannan yasan da ya ta6a ta iyayen sa zasu ci uban sa...shi duk a kan haka ya bar maganar wai dan saboda gudun 6acin ran iyayen sa shiyasa bai basu ni ba, nan kuwa ba haka bane dan da 'kyar ya samu nastuwar zuciya, kusan sati guda abinvna cin sa arai, da ya tuna sai dai kiji ya saki tsaki, sai dai shi kansa bai san dalilin da ke sashi yin hakan ba, haushi yake ji sosai kawai amma ya rasa takamamman dalilin shin zuwan su Imarana yake jiwa haushin ko kuwa dalilin zuwan su?"

🌷 ~Happy Ramadan in advance~ 🌷

Comment
Vote
Share

*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

🕌🌙 ~RAMADAN MUBARAKH~ 🌙🕌

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *61*

Nima ina kitchen duk ina jin tattaunawar tasu amma sam ban fahimci inda maganar tasu ta dosa ba, hakan yasa ban wani sa zancen aka ba.

'Kiran sallahr Maghrib da akayi ne ya sa Yah Deen lumshe idanu ya kuma bu'de su nan take...da 'kyar ya iya motsi daga inda yake tsayen ya juya ya koma ciki, zuciyar sa ba'ki'kirin haka yake jin ta, alwala ya 'dauro duk na zaci zai tafi masallaci ne ma amma ga mamaki na sai banga fitowar sa ba.

Shiga nayi nima dan inyi tawa sallar nan na tarar da kan dadduma a parlour har ya idar da sallar sa agida, abu 'daya da zan shaidi halin Yah Deen da shi shine rashin wasa da lokutan sallah,  koda wasa baya wasa da 6angaren ibadar sa.
Ganin yana parlour ne ya sanyi ni shimfi'da nawa abin sallar a ciki na gabar da abina.

Haka ranar ko abinci ban ga ya ci ba...na kan ji dai time to time yana sakin tsaki da bansan dalilin yin sa ba...sai dai kawai in ta6e baki na...domin har a lokacin ko hira bama zama muyi da shi balle har in samu daman tambayar sa damuwar sa.

Har bacci ya 'dauke ni kan kujerer da nake bacci shi kuma yana cik amma bai daina zirga-zirga tsakanin parlour da bedroom ba kamar wanda allurar sa ta 6ace masa yake faman nema..ban da'de da fara baccin ba naji yana tashi na, firgigi nayi na farka take na mi'ke zaune ina micik-micik da idanuna, sai yace min in tashi in koma ciki in kwanta.

Da muryar bacci nace da shi" Anan fa nake kwan..."
" Shut up dallah...ni bansan me nake yi ba kenan ko?"
A tsawace ya fa'di hakan tamkar zai doke ni.

Ai kam da sauri na tashi ina 'kun'kuni na shiga cikin na kwanta...yayin da ya bi bayana da mugun kallo.

Ban kuma jin motsin sa ba cuz da shiga ta nayi bacci abi na.
Sai da na tashi da safe ne ma sai naga alamun a parlour ya kwana ranar.

Da safen kuwa da nagama ha'da masa breakfast 'din sa naci nawa sai na hau shirin  makaranta  sai da na kammala komai na fito kafin yace wai bazani makarantar ba sai gobe, kamar zanyi kuka na koma ciki ina tura baki na, haushi sosai ya kama ni, musamman da na tuno Ammi bata ta6a hana ni zuwa makaranta ba koda ta rana 'daya ce...haushin da ya bani.ne ya sanya ni shigewa ciki ban kuma fitowa ba shiyasa ban san ko yaci abinci ko kuma akasin haka ba.

Sai da rana dana fito nemawa ciki na abin ta6awa nan na tarar da nasa abincin Tea kawai yasha.

Baki.na ta6e ban wani damu ba kuma...haushin da ya bani ma a ranar ya sanya ko inda yake bana kalla, haka na yi ta sha'ani na.

Sai bayan kwana biyu kafin da 'kyar ya barni na tafi makarantar sai da yaga alamun zanyi masa kuka ma kafin ya amince inje, ni kam kwata-kwata sai na rasa dalilin wannan 'ketar... bacin ya san ba yau na fara fita school 'din ba me yasa sai yanzu zai tsiri yi min hali kuma.

Muna tashi daga makarantar ma gida na wuto cuz an hanani zuwa ko'ina, Ammi ta min warning tun ba yau ba haka shima ko yau ma kafin ya bar ni fitowa sai da yayi min garga'di sosai, shiyasa da an tashi a school nake kamo hanyar gida bana tsayuwa ko'ina.

Wataran ma ina tafiya ina jimamin hanya ta ta da da nake bi in tafi gidan Ammi yau gani ina yankan wani hanyan daban ba wanda nasaba bi ba.

Inajin kewar kowa da kowa gashi babu wanda ya ta6a zuwa gidan nasa dan dubani, bansan laifin da nayi musu ba sam...sau tari idan ina hanyar makaranta share hawaye nake yi na ba'kin ciki da takaicin zama na tare da shi.
Chapter 126 · 0% Book details