Sashe 205
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shima Uncle Ja'afar hakan da yaji Saif na fa'di ne ya sanya shi saurin fahimtar halin da ake ciki, yana da tabbacin Mu'een ya farka ne shiyasa Saif ya 'kira shi domin shine da kansa ya tsara masa komai da zai ce.
Albishir 'din da yayiwa Alhaji Baba kenan nan suka shirya a hanzarce suka fito.
Saif cikin farin ciki yayi wayar tamkar babu wata damuwa tattare da shi...yana sau'ke wayar daga kunnan sa sai ya suka ha'da idanu da Mu'een domin tuni ya bu'de nasan lumsassun idanun ya zubawa Saif tunda yaji muryar sa kusa da shi.
Cike da murmushi yace" Yaya albishirin ka..! yanzun Uncle ke ce min an maida muku auren ku da Noor...gaskiya ka bani tukuici na..."
Idanu ya zubawa Saif na tsawon lokaci sannan a hankali ya maida idanun sa ya lumshe gami da juya kansa...hawaye Saif yaga yana tsiyaya daga gefe da gefen idanun sa..take kuma na'urar dake irga bugun zuciyar sa ta fara 'kara yana 'dan sau'ka a hankali...fisga jikin sa ya fara ka'dan-ka'dan...kana iya ganin hawa da sau'kan da 'kirjin sa ke yi.
Rikicewa Saif yayi da ganin hakan take ya fara 'kiran sunan sa, hannu ya sa aka yana ji tamkar ya 'kwala ihu saboda tausayin Yayan nasa, a rikice ya fara ja da baya da niyyan fita 'kiran likita, sai dai kafin ya kai ga isa jikin 'kofan ma sai suka riga shi turowa.
Da sauri suka yi kansa bayan sun bawa SAIF
umarnin fita sai suka datse 'kofan ko ta glass in window Saif ba ya iya hango shi haka duk sai yaji hankalin sa ya tashi sosai.
Bei iya ya ko 'kira su Alhaji ba tsaye yake yana safa da marwa da ka gansa zaka san cewa hankalin sa duk a tashe yake, wanda ba'a 'dauki tsawon lokaci ba sai ga su Alhaji ma sun iso nan yayi musu bayani a takaice yana nuna damuwar sa a fili 'karara.
Innalillahi kawai suke ta maimaitawa yayin da Alhaji ya samu wuri kawai ya zauna ya dafe kansa.
Kimanin awa guda da rabi kafin likitocin suka fito su kansu ba'a nutse suke ba..domin da 'kyar Allah ya taimake su suka ceto rayuwar sa cuz bugun zuciyar san 'kasa sosai ya sau'ka.
Albishiri suka musu akan cewa ba wani matsala su kwantar da hankalin su nan da wani lokaci komai zai daidaita da iznin Allah...nan Alhaji Baba ya saki wani ajiyan zuciya Uncle Ja'afar kam godiya ya ringa zubawa mahalicci.
Cike da farin ciki suka samu wuri suka zauna gaba 'daya...tsabar sauri ma duk wayoyin su basu taho da shi ba, a masau'kin sun suka baro shi.
Allah cikin ikon sa kuwa kafin sati guda har yana iya shiga bayi da kansa...sai dai har yanzun baya magana da kowa...sai da ido kawai.
Uncle Ja'afar ma jiya ya koma ganin jikin nasa da sau'ki kuma likita yace ba sai anyi masa dashen ba ma insha Allahu komai zai wuce.
Fatan su dai Allah ya 'kara lafiya ne ingantacciya.
Sai da Alhaji Baba ya dawo ne kafin su Ammi ma da Anty Zainab suka shirya zuwa can Zarian, sai dai Alhaji yace bai yadda su kwana ba a ranar zasu dawo dan haka sassafe suka shirya tafiya.
Tun dare Anty Zainab tace da Noor ta shirya zata raka ta wani wuri gobe kuma da sassafe zasu zo su 'dauke ta, da yake da motar gida ne so basu da matsalar komai.
Noor kam toh kawai tace da ita ba wai dan ranta na so ba..sai da ma suka fito kafin take sanar da Ammi cewa tafiyar fa wai harda Noor ne tun jiya na gayyace ta amma ban sanar da ita Zaria zamu ba.
" Ammi jim tayi kafin tace kar kuma taga kamar an takura ta fa?"
Anty cewa tayi
" A a ita da mijinta wani takura kuma yanzu, idan kika biye ta Noor fa har abada baza'a yi abinda ya dace ba".
Haka driver ya jasu zuwa 'kofar gidan Ummahn Saudah..shiga suka yi suka gaggaisa kafin suka fito dukkan su, Noor kam tun da taga harda Ammi sai taji hankalin ta bai kwanta da tafiyar ba, ai kuwa kamar wasa sai taga sun 'dauki hanyar Zaria ta kuma san can Mu'een ke kwance...shiru kawai tayi tana jin faragabar ganin sa a zuciyan ta.
Sosai su Ammi suka yi farin ciki da ganin sa zaune, magana ce ka'dai baya yin ta sai ya ga dama, haka ya dinga bin Noor da kallo bai iya yace da ita ko uffan ba, ko gaisuwa akayi masa baya amsawa sai dai ya lumshe idanu kawai.
Banda murmushin farin cikin ganin su Ammi babu abinda zaka gani kan fuskar sa.
Haka har suka baro Zaria magana bata ha'da su da ita ba..ita kam ko a hanyar komawar su ma jikin mota ta kwantar da kanta tana share hawaye a 6oye.
Tana jin yanda su Ammi ke bayyana tsananin farin cikin su a fili da ganin yanayin jikin nasa, amma ita bata iya sanya musu baki ba.
Tunanin ta ma tafiyar da ke gaban ta ne, dama tun lastweek ya kamata ta koma amma Anty Zainab ta dakatar da ita, yanzun wai zuwa jibi zasu koma har da ita Antyn.
Koda aka sau'ke su ita kam bata fita daga motar ba tace a wuce can gida da ita tana so zata 'karasa shirin ta ne...
Bayan kwana biyu da zuwan su Zaria suka bar Shuwarin ita da Anty Zainab amma sai da suka kwana kusan uku a Zaria kafin suka wuce dama ashe haka Anty ta tsara tafiyar shiyasa ta dakatar da ita.
Tunda suka koma kuwa sam ta kasa barin ta ta ci abinda ranta ke so, ci wannan sha wannan duk ta ishe ta da su, a 'yan kwanaki biyu zuwa uku da suka yi a Azare 'din ba 'karamin ha'da abubuwa Anty Zee tayi ba shiyasa a kullum bata zama a gida har sai ranar da suka taho.
Wani sa'in har mamakin ta Noor ke yi domin sarai tasan dan me Antyn ke sa ta gaba da shashayen abubuwan ita kuwa ranta ba so yake yi ba, a ganin ta duk 6ata lokaci suke yi abanza da wannan auren nasu bashi da darajar da har za'a yi masa shiri irin haka.
Bata manta lokacin da ta kunna wayar ta ta 'kira AbdulHakeem ba..lokacin da kanta tasan ta sanyawa Zuciyar ta dauriya, amma duk da haka sai da tayi kuka daga 'karshe kasa ma magana tayi sai text ta tura masa akan cewa an riga an 'daura mata aure.
Da farko 'kin amincewa yayi sai daga baya ya yadda dan yasan Noor bata yi masa 'karya.
Ya ji haushi sosai kam amma hakan bai hana shi yi mata fatan Alkhairi a auran ta ba...Abin mamaki sai ga shi harda kyautar ku'di yayi mata masu 'dan nawi a fa'darsa wai tashi gudummuwar kenan, sam be nuna alamun yaji 6acin rai ko wani abu ba duk da tasan dole abin sai ya dame shi amma yanda yayin sosai taji ya 'kara birge ta.
Sai take jin dama shine ta aura da babu abinda zai hana ta shan duk wani abinda ake sha da ku'din ta ma zata siya amma Mu'een kam wannan ba damuwar ta bane shi domin ko duniya zata ha'da ta shanye saboda shi tasan ba kwarjini zata yi a idanun sa ba, tunda hakan ba zai hana shi ya tsallake ta ya tafi wurin wasu matan ba.
*****
_Wai ya labarin Husnah ne?_
Husnah na can yanzu duniya tayi mata da'di domin babu mai takurawa rayuwar ta, tun rabuwan ta da Mu'een bata 'kara sashi a idanun ta ba, da yake ma ha'kura tazo tayi da makarantar ta koma Abuja wurin mijin ta ta cigaba da bautawa auren ta.
Duk yanda Hisham yaso yaji dalilin barin makarantar Husnah 'kin sanar da shi tayi, ta kuma canza layi ta daina amfani da tsohon layin ta abin duk sai yake bashi mamaki matu'ka.
Da farko abin damunta yake sosai a zuci, haushin yanda ta ringa biye masa tana yadda da bacin da auren wani namijin akanta.
Sam ta rasa me ya toshe mata 'kwa'kwalne ma da bata 'dauki mataki akansa ba, tasan hadda sakacin ta ma baya ga haka da be isa ya 'keta mata haddin auren ta ba.
Haushin sa sosai yanzun take ji ko tunawa da shi bata so tayi, Allah ma ya taimake ta tun ranar da Noor da gansu bata sake sanya shi a idanun ta ba.
Wani sa'in idan abin ya ishe ta sai taji kamar ta sanar da Hisham gaskiyar abinda ya faru amma wani 6angare na zuciyar ta sai yake yawan garga'din ta akan kar ta fa'di ma kowa domin idan kasan farkon fitina baka san 'karshen ta ba.
Sai daga baya duk ta watsar da komai ta cigaba da rayuwar ta kamar kowa sai dai har yau 'din nan bata daina istighfari da neman gafarar mahalicci ba.
Hisham mutun ne mai tsananin ha'kuri da kawar da kai, ga sanin ya kamata ga shi sam baya 'dagawa kansa hankali a kan komai.
Zaman su lafiya suke da ita yana kuma kulawa da duk wani abu da yake hakkin ta ne.
Alhaji Maman mahaifin sa kuwa tun lokacin da wani hatsari ya rufta da shi jinya ya kasa 'karewa sai amaryar sa ta wawashi iya abinda taga zata iya sannan ta je har asbitin da yake jinya ta tsaya akansa wai ya sai ya bata sakin ta.
Ai kuwa sai da ya sake tan kafin tayi gaba tana ta6e baki gami da taunar chewingum tace bazata iya zama da miskini ba domin daga 'kugun sa zuwa 'kafafun sa duk sun yi damage basa amfani.
Haka tana yatsina fuska tayi gaba kowa dake wurin sai da yayi mamakin ta domin kaf cikin matan Alhaji Mamman ita yafi fifitawa sai gashi itace ta fara guje masa a lokacin da yake tsananin bu'katan kulawa.
Tun lokacin ya fara danasanin abubuwan da ya ta aikatawa dama kuma duk abinda ba'a shirya shi ta hanyar da ta dace ba 'karshen sa ba kyau yake yi ba.
Taimakon da Allah yayi masa ma shine be kai ga wula'kanta ba Allah ya kar6i ransa...domin dududu bai fi 3months da jinyar ba ya koma ga mahalicci.