← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 211

Sashe 30

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk abinda takeyi Noor bata ko bi ta kanta ba illah tsurawa inda Jas ke kwance kawai da tayi idanu, tana matu'kar tausayin Baby sosai..a inda take 'din sai ya kasance tana fuskantar fuskar Jasmine 'din ne, gani tayi yarinyar tayi fayau sosai, hasken ta ya 'karu fiye dana asali.

Kuka take jinyi a duk lokacin da ta kalli Jasmine ta tuno mummunan 'kaddarar da ya hau kanta, sosai abin yake ta6a mata zuciya.....amma sai take daurewa take bawa kanta 'karfin gwiwa da ya'kinin Allah zai yi mata jagora wajen kulawa da ragowar rayuwar Jas 'din har 'karshen rayuwar su.

Dawowa Hafsat tayi inda take zaune gami da dafa 'kafa'dun ta...Noor sai ta rintse idanu a hankali, 'dan guntun hawayen da ya cika cikin idanun ta suka gangaro sai tayi saurin share su.

'Dagowa tayi ta kalli Hafsat 'din yayin da ta 'dago Cup 'din tea 'din ta mi'ka mata ba tare da ta furta komai ba illah yanayin fuskar ta da juya zuwa yanayi na tsantsan tausayi.

Kar6a Noor tayi ba tare da 6ata lokaci ba ta kur6a, tana jin yanda 'dumin Tea 'din ke ratsa mata ciki kasancewar babu komai acikin nata tun safe...cigaba tayi da kur6an tea 'din yayin da zafin da cikin keyi yake 'kara yawaita mata, duk da haka kuwa bata fasa sha ba dan tasan ba komai ya jawo hakan ba face tsantsan yunwa.... ka'dan-ka'dan take sha har ta shanye rabin sa sannan ta ajiye cup 'din a gefen ta.

Babu wanda ya sake magana acikin su, shiru wurin ya 'dauka kusan na tsawon mintina goma, kowa da abinda yake sa'kawa cikin ransa, wanda cikin 'yan mintinan Noor ta danne zafin da take jin cikin nata na mata duk da kuwa yaso yafi 'karfin dauriyar tata amma sam bata nuna haian ba, kafin cikan mintina goman kuwa har ya 'dan sarara.

Ganin yanda Hafsat ta tsura mata idanu take kallon tane ya sanya ta tunowa da abinda Hafsat ke zaman jira daga gareta...wato labarin rayuwar ta.

Noor sama ta 'daga kanta gami da rintse idanun ta a hankali wasu siraran hawaye masu sanyi suka sake sau'ko mata.

Bata sharesu ba wannan karon sai ta barsu suka cigaba da sau'ka a hankali.

Hafsat kuwa ita kawai ta zubawa idanu take kallo gami da sauraron jin labarin Hudah daga bakin ta....amma ganin kukan da take yi sai itama taji wani iri jiki da zuciyar ta, gani take yi kamar Noor bata son tunowa da rayuwar ta na baya ne, sai take ganin tamkar takura mata tayi akan hakan.

Ajiyan numfashi Noor ta sau'ke sannan ta sau'kar da kanta gami da goge hawayen da ya gangaro mata....wanda tana cikin hakan ta tsinkayi muryar Hafsat na fa'din " idan da takura Huda ki bari sai wani lokacin babu damuwa ai muna tare....".

Murmushin gefen baki na 'karfin hali Noor tayi mata batare da ta bata amsar wancen tambayar ba taci gaba da fa'din.........

*****
Asalin suna na Nurul Hudah, iyayenmu mu biyar suka haifa, Yah Usman shine babba sai Addah Maryam, sauda, Amina (Nanne) sai ni autar mu da mahaifina ya sanya min suna *Nurul Hudah* .

Na taso cikin gatan Ummah na da Babana dan su ka'dai na bu'di idanu na ganni tare da su, cuz tun kafin nayi wayo aka aurar da yayuna mata biyu, Yah Usman kuwa ba zama yake yi sosai damu ba, shi ya kan ziyarce mu ne lokaci zuwa lokaci saboda yanayin sana'ar sa, daga ni sai yayata Amina da nake bi mata, haka muka taso gaban iyayen mu cikin so da 'kaunar juna.

Mahaifina asalin manomi ne tun a wancen zamanin, bashi da wata sana'ar da ta wuce noma, kuma Alhamdulillah ba laifi dan a hakan muke lalla6a rayuwar mu cikin rufin asirin Allah, bamu fiye neman abu mun rasa ba.

Da yawan mutane kan 'kira shi da Malam Mamman Jaji...mun kasance asalin fulani ne na garin bauchi, mahaifiyata 'yar asalin 'karamar hukumar Darazo ne yayin da mahaifina ya kasance haifaffen garin Shuwarin.....rabon aure ne kawai ya ha'da mahaifana lokacin da wata tafiya ta kai shi garin Darazo har Allah ya 'kaddara auren su.

Sana'ar Ummah ta shine kunu da suyan waina kullum safiya a 'kofar gidan mu....wanda ya kasance nice ke taimaka mata koda wani lokaci idan mun gama komai sannan sai inje inyi shirin makaranta ta shiyasa mafi yawan lokuta na kasance cikin lattin zuwa makaranta kusan mafi yawa daga cikin 'dalibai na riga ni isa makarantar.

Sam Ummah bata saka Amina Nanne cikin sabgar sana'ar ta harda ma ayyukan gida gaba 'daya, kasancewar bata da isashshen lafiya kamar ni.

Shiyasa Ummah bata fiya matsa mata akan komai ba sai dai ni duk da kuwa baya nake da ita.

Duk wani abinda ya kamata ace Nanne ce ke yi matsayin ta na wacce take sama dani to ni ke yinsa.

Hatta da wankin kayan mu Ummah da kanta ke mana da kanta, wani lokaci kuma ina taya ta da 'dauraya har mu kammala....tun tasowata ban tashi da 'kiyuya ko son jiki ba.

Na kan birge Baban mu a duk lokacin lokacin da yaga na bada himma ina ayyukan gida tun kafin shekaruna su suyi 'kwari...wanda har hakan ke sanya shi yawaita sa min albarka cikin matu'kar jinda'di.

Wainar Ummah ta yayi farin jini ba laifi domin da yawan mutane kanzo wurin ta dan ha'da abin karin su yayin da wasu ke ci a wurin batare da sun yi dakon sa zuwa wani wurin ba.
Akwai wa'danda har booking suke yi tun kafin ayi.....yayin da wasu ke zuwa su jjira har layi ya iso kansu.

Gurbin wainar Ummah ta baya ta6a rabo da masu siya har sai in ta kammala gaba 'daya.

Alhaji Baba ya kasance 'daya daga cikin masu siyan wainara Ummah ta, kuma babban abokin Baban mu ne, mafi yawan lokuta tare zaka gansu indai har babu wani uzuri dake gaban 'dayan su.

Ya kan siyi wainar Ummah ta da da 'dan yawa dan kullum yakan sawa ayi masa sadaka dashi sannan akai masa wani gida.
Tun ban da wayo nike zuwa gidan Alhaji Baba har na fara wayo kaina, domin kusan kullun sai ya siya an kuma kai masa gar gida.

Mutum ne shi mai matu'kar kamala da sakin fuska gami halin girma, ga faram-faram da jama'ah bashi da mugun hali sam.

Shi na fara sabawa da shi kafin kowa cikin gidan sa, domin duk ranar da muka ha'du na kan zauna da shi muyi ta hira abin mu shima baya gajiya da biyewa yarinta ta.

Abu 'daya dake kulle min kai game da shi shine yanayin rayuwar su...sam ba kamar yanda mu muke rayuwa bane, sosai tsarin rayuwar mu ta bambanta da su.

Yanayin sa shi kansa da yaran sa, yanayin gidan sa, tun daga harabar gidan, ciki da kuma abubuwan more rayuwa dake cikin gidan sosai suke bani mamaki, domin ni in ba agidan nasa ba ban ta6a ganin dayawa daga cikin su ba.

Komai na gidan Alhaji Baba na musamman ne...idan kana cikin gidan sa har manta cikin garin da kake zakayi in ba ka fito ba, domin zakayi tsammani cewa cikin babban gari kake.

Yanayin yanda yake dressing 'din sa ma daban ne ba irin na su Baban mu ba, domin shi Alhaji Baba kusan kullum zakaga kayan jikin sa sababbi ne masu kuma matu'kar birgewa.

Na rasa dalilin da ya sanya su 'din komin daban domin hatta da wankin kayan su da engine suke yin sa, kasa ha'kuri nayi da hakan har naje na tambayi Ummah ta.

Abakin naji naji ta'kaitaccen tarihin Alhaji Baba kamar haka.........

*~One Luv masoya na~* 🥰❤😍 *......yau dai ga NOORUL ta dawo fatan ha'kurin naku bai kammala* *'karewa ba* 😉

*Daga yau insha Allahu zaku cigaba da samun update akai-akai koda read more 'daya ne ma* 🥴 *....agafarce ni pls.*
*Kuyi manage da wannan kafin ku sake jina.* 👌🏻

😎😎😎
Deen 'dina na gaisuwa fa 🙋🤠

*Salmerh ce* 😍
[12/17/2019, 10:50 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *16*

Kafin Ummah ta fara magana sai ga Nanne ma ta zo inda muke zaunen ni da Ummah, zama tayi a gefena tayi shiru itama kamar yadda taga nayin muka cigaba da sauraran Ummah a tare....domin zuwan Nanne bai sa Ummah ta taka birki daga fa'dar labarin da tayi niyyan bani ba........

*****
Alhaji Taheer Manga.....haifaffen cikin garin Azare ne na jihar Bauchi....wanda yanayin aiki ya kawo mahaifin sa mai suna Mukhtar garin mu inda anan yayi katari da samun matar aure Fatima wacee itama ta kasance matashiyar malama ce a makarantar da yake aiki bata ko yi rabin shekara da fara aikin ba......batare a wani 6ata lokaci ba suka dai-dai ta kansu, iyaye suka shiga maganar akayi bikin Mukhtar da Fatima cikin farin ciki da 'kaunar juna.

Sunyi zama na tsawon shekaru wanda har ya kasance sun zama tamkar 'yan asalin garin ne, shima bai hanata fita aikin ta ba suka cigaba da fita abinsu atare har Allah ya azurta su da samun 'Ya'ya.

....Mahaifin Alhaji Baba bai ta6a samun matsala da kowa agarin ba, har yazo yayi dacen samun matsayin Headmaster na makarantar......ga shi kuma yana da kyakkyawar ala'ka da manyan cikin garin sosai suke girmama junan su.

Wanda har wa'adin Allah ya kasance akansa bai sake samun wata haihuwar ba duk kuwa da yana son samun 'ya mace amma Allah bai nufe sa da samu ba..... ya rasu ya bar yaran sa maza guda biyu wato Taheer (Alhaji Baba) sai mai bi masa Ja'afar da yanzu haka yake zaune can garin Kaduna da iyalan sa.

Lokacin da ua rasun shekarun Taheer goma shabiyu yayin da Ja'afar yake da shekara tara fa haihuwa.

Tun bayan rasuwar sa Fatima taci gaba da kulawa da yaran da karatun su da tarbiyyar su bisa jagorancin mahallici.

Bata sake tunanin sake yin wani auren ba duk da kuwa alokacin tana da 'yan 'karancin shekaru wanda hakan yasa mutane da da dama ne suka bu'kaci auren ta amma sam bata bawa kowa dama ba dole tasa kowa ya janye nasa 'kudurin
Chapter 30 · 0% Book details