← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 211

Sashe 109

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ma'u kam tasha wankan jumma'an ta da niyyar zuwa taya ni taron biki a gidan da nake kamar yadda tayi al'kawari, fuskar ta ba yabo ba fallasa ta fito jin wai ana 'kiran ta, zaton ma ko Ahmad ne ya dawo, dan zuwa lokacin tagama yanke cewa zata bashi ha'kuri kawai su dai-dai ta tunda wanda take haukan so 'din ma auren sa zai yi, sai dai ganin Imrana tsaye daga gefen gidan su ne ya sa ta 'dan 6ata ranta tana kallon sa tare da tura baki ita adole ya takura ta da yawa.

Murmushi imrana yayi irin na 'yan duniya batare da ya damu da yanayin da ta yi da ganin sa ba ya 'dan tako izuwa gaban ta sannan yace" Kwantar da hankalin ki hajiya Asma'u sarauniyar Deeni, yau 'din zuwan na musamman ne..kuma nasan zakiyi matu'kar farin ciki idan kika ji abinda ya kawo ni, wa ma kika ce min kina so kwanakin nan...?"
Ya 'karashe maganar yana duban fuskan ta.

Kallon sa kawai tayi itama amma bata bashi amsar tambayar sa ba zaton ta ma ko wani zagin zai kuma yi mata kamar yanda ya saba akan Deeni, ita kuwa yanzu da tasan yau akayi auren bazata sake fa'din tana son shi ba.

Shi 'din ne dai ya cigaba da magana ganin tayi shiru sai ya sau'kar da muryar sa inda yake fa'din"..Deeni kika ce kina so ko ba haka ba?"

Yanda yayi mata maganar kalan na masu hankali ne ya sanya ta d'age kanta sama ta bashi amsa alamar " Erh".
Sai yace
" Kin kuwa san yau ne 'daurin auren sa, amma yace ya fasa saboda ke ka'dai?"

Ido ta zaro tana kallon sa da mamaki, take fara'a ya bayyana kan fuskar ta tana washe ha'kora tace" Dagaske ya fasa auren?"

Yace
" Wallahi ya fasa shine ma ya turo ni yace inje in 'kira masa ke yana son ya ganki na yau ka'dai kawai...zamu iya tafiya yanzu ko a a".
Da hanzari tace
" Erh muje ai na shirya ma". Inda tayi maganar tana mai karka'da hannuwa saboda tsabar farin cikin da ya cika mata zuciya.

Gudun kar a gansu tare da shine gashi gari irin na ranar friday akwai jama'a sosai, hakan ya sanya yace da ita su raba hanya zai jira ta a 'kofar gidan Deen 'din in yaso idan ta iso sai su 'karasa shiga tare".

Take ta amince da batun sa batare da tayi wani tunani akan hakan ba.

Aikuwa basu 'karasa gidan tare ba, duk saurin da Ma'u tai ta zubawa sai da imrana ya riga ta isa abinku da namiji ga shi da dogon 'kafa.

'Kafar Ma'u kam duk tayi futu-futu da ita ga zufa shar'kaf, kwalliyar da tayi ma duk ta dame ta kwa6e mata a fuska kaca-kaca ta koma wata iri da yake da yawa ta shafa powdern gasu jan lipstick da sauran su.

kallo Imrana ya 'kare mata daga sama zuwa 'kasa sannan yace" Kina jina ko?"
Sai ta 'dage kanta sama.
Yace ciro 'dan kwalin kinnan ki goge fuskar ki, shi fa Deeni baya son mace mai yawan kwalliya..."
Ya fa'di hakan ne saboda ganin da yayi kwalliyar tata ta fita a hayyacin ta, kuma yasan matu'kar Deeni ya ganta cikin wannan yanayin ba zai amince da ita ba shiyasa yayi mata dabara.

Ma'u kuwa tana jin haka take sai ta fara goge fuskar ta, kafin kace Kobo har kwalliyar ta yi hanyar ta fuskar ta tayi fayau shine ya ringa nuna mata inda basu 'karasa goguwa ba duk ta goge su, take fuskar ta dawo dai-dai.

Duba mai kyau zaka yiwa Imran ka fahimcj murmushin mugunta yake yi, amma ga Ma'u da gankalin ta baj je can ba hakan sai ya sa bata fahimci komai game da shi ba, yana murmushin  yake fa'din" Yauwa koke fa 'yan mata, kinga ma kin fi kyau haka nan fiye da 'dazun.."

Murmushi Ma'u tayi yayin da Imran ya cigaba da fa'din" Idan mun shiga ciki ki natsu kinji, kuma ki tabbatar bakiyi masa gardama ba, duk abinda yace miki kiyi to kar kiyi masa musu sam baya son taurin kai shi ai ke da kanki kin sani ma ko? nima nan da nake abokin sa ai kinga bana yi masa wargi ko?"

Kai kawai ta 'daga sama alamar" Erh"
Duk da bata tabbatar da maganar tasa ba amma yanayin da tayi mata tambayar yasa she hv no choice than to ansawer him yes.

" Balle ma ke baki na son shi ba..?" Imrana ya sake tambayar ta.

Sai ta sake 'daga kanta sama kamar wawuya.
Sai yace" Kuma kema kina so ya so ki ya aure ki ko?"
Wannan karan kam ido ta zuba mishi tana kallon sa, sai da ya sake maimaita tambayar kafin ra bashi amsa da
" umm" 'kasan ma'koshi.

Sai yace
"Gud toh banda taurin kai, yau ranar ki ce yarinya kiji da'din ki kinji?"
" Uhumm"
Ta sake fa'di batare da tasan ainahin manufar sa kan fa'din hakan ba.

"Bismillah" yace tare da juyawa ya shiga gidan, a hankali ta 'daga 'kafafu ta bishi a baya suka shiga ciki.

Can cikin bedroom Deeni yake yana duba sake duba kayayyakin da Uncle ya 'din ka mai sai yaji sallamar Imrana.

Yana daga wurin ya amsa wanda hakan ya bawa Imrana damar 'karasawa ciki ya same shi, yana daga tsaye ya 'dage masa gira yana murmushi ya nuno parlour da babban 'dan yatsan sa yayin da sauran yatsun ya tan'kwashe su.

Yah Deen bai wani sha wahala fahimtar manufar sa ba dayake bai manta akan abinda suka rabu ba, dan haka sai ya mi'ke tsaye fuskar sa wasai saboda farin cikin da yake ciki na fasa auren sa da akayi da Husnah.

Murmushi ne ya bayyana kan fuskar sa yana kallon Imrana yace " Haba dagaske Imran ka kawo min?"

Kai ya jinijna masa tare da juyawa yake fa'din" Wancen ajiyar da kwanaki nake baka labarin nace, yarinyar na tsananin 'kaunar ka tun ba yau ba so ka more abinka, amma please kar ka yi abinda zai sa asirin mu ya tonu kasan wannan ba Husnah bace..ni zanje in dawo nan da 40mins".

Bai ce da shi komai ba har ya 'karasa fita illah bayan sa da yabi da kallo hannayen sa duk na ri'ke da 'kugun sa.

Dai-dai yaji 'karan rufe 'kofar parlour at sane time Ma'u ta bayyana bakin bedroom 'din sa idanun ta 'kasa, wanda shigowan nata ya samo asali ne daga umarnin da Imrana yayi mata kafin ya fita.

Taki uku tayi ta tsaya daga inda take tsayen bata 'karaso ba haka kuma bata 'daga kai ta kalle shi ba illah" Ina yini" da ta furta.

Yayin da Yah Deen ya dinga bin ta kallo kawai batare da ya amsa gaisuwar tata ba.

Sosai ganin ta gaban san ya sake tada masa tsimin sa, ya jima da mura'din yarinyar cikin ransa sai gashi yau Allah ya bashi dama har cikin gidan sa.

Kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya 'dan matsa baya ka'dan bayan ya cire hannayen sa daga 'kugun sa, da sanyin murya yace' 'Karaso mana ki zauna ko?"

Yayi maganar yana nuna mat bakin gadon sa.

Sai da ta kalle shi sai kuma ta kalli inda yake nuna matan, Mu'een kuwa 'dauke kabsa yayi tamkar ba shine yayi maganar ba kawai ya cigqba da abinda yake yi.

A hankali ta 'karasa ta zauna bakin gadon tana mai wasa 'yan yatsun hannun ta sam sai taji ta kasa sakewa..it kanta bata san me yasa take matu'kar son wannan mutumin ba.

Cigaba yayi da abinda yake yi, sai da ya kammala ya maida kayan mazaunin su bayan ya cire wanda yake son sanyawa ya ajiye gefe kafin ya dawo inda take.

Gefen ta ya zauna yana sakin sassanyar ajiyar zuciya.

" Ya sunanki?"
Ya tambaya yana kallon fuskar ta.
Kanta 'kasa tace" Ma'u".
" Miye kuma Ma'u? sunan ki Asma'u dai ko?"
'Kasan ma'koshi tace" Umm".
Sai yace" Gud!...kina sona wai dagaske?"
Ya tambaya still yana kallon ta.

Shiru tayi bata iya ta bashi amsa ba saboda kwarjinin da yake yi mata...Mu'een kam bai damu da shirun nata ba kawai ya cigaba da fa'din" Anyways..baki da matsala, ko da 'din ma bansani bane..amma kinga yanzu da na sani ai har aure na fasa saboda ke..fatan kin shiryawa jarrabawar da zan miki?"

Kai ta 'dage sama alamar " Erh".
Tsaye ya mi'ke sannan yace" Ki shiga ki watsa ruwa jikin ki..in kin fito zan gaya miki what is next".
Ya 'karashe da nuna mata bathroom 'din sa.

A tsare da furta hakan saboda baya son tayi masa gardama sam, ai kuwa sai ta 'daga kai ta kalle shi sannan tace " Nayi wanka a gida..."

Tun kam ma ta 'karasa yace" Banson musu ni..a haka ne zan aure kin?"

Tana jin haka ta mi'ke ta nufi bayin nasa kafin ta 'karasa shiga ne ya sake ce da ita" 5mins please ina jiran ki yanzu akwai inda zani".

Ranta fari 'kal ta shiga bayin, bata sha wani wahala wurin fahimtar yanda zata yi ba cuz akwai tap, taran ruwan tayi a bucket tayi wankan ta tasa ta maida kayan jikin ta sannan ta fito tana wani sussune kai 'kasa.

Ko da ta fito bata gansa cikin 'dakin ba danchaka sai ta koma inda ta tashi 'dazun ta sake zama tana rarraba idanu da tunanin jarabawar da yace zai mata...farin cikin ta bai wuce auren ta da yace zai yi ba.

Tana cikin tunanin taga ya dawo 'dakin direct inda take ya nufo yana binta da kallon sha'awa..." Kayan basa damun ki ne?"
abinda ya fara fa'di kenan lokacin da ya isa wurin ta.

Kai ta jijjiga masa alamar" a a basu damin ta.

Zama yayi daf da ita tare da 'dago 'kafar sa 'daya ya 'dora daga saman cinyoyin ta...cikin murya mai 'daukan hankali yace" Ni banson ganin ki da su to..ko baki son cin jarabawar tawa?"
Chapter 109 · 0% Book details