← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 184 OF 211

Sashe 184

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji Baba bai sake tanka su ba har washegari wanda da safe bayan sunje gaida shi ya amsa sai ya 'kira sunan Safwan yace" Naga kamar kai in ka fishi hankali, dan Allah Safwan ka tattara abokin ka ku koma can inda kuka fito, daga yanzu zuwa 8:00 idan na ganku agida na ku tabbatar hukuma ce zata raba mu..banson damuwa sam dan Allah ku tattara ku tafi...".

Shiru Safwan yayi yama kasa fa'din komai, hankalin Yah Deen sosai ya tashi, dan ga dukkan alamu bazai samu abinda yake so ba, Ammi ta kore shi ga Alhaji ma haka, sannan da alamu ganin Noor ma wahala zai bashi, ina ta shiga ne? Ya tambayi kansa.

Tuno gidan Ummah da yayi ya sa ya 'dan ji sanyi aran sa da tunanin babu mamaki indai tana can zai iya ganin ta cuz yasan halin Ummah da kawaici bazata hana shi ganin ta ba....cikin ransa ya bari akan sai ya gama da 6angaren mahaifan sa kafin zai je gareta itama.

Alhaji Baba na gama bayanin sa ya tashi ya fice ya bar su a 'dakin.

Jim suka yi gaba 'daya, sun 'dauki tsawon lokaci ahaka bayan fitar Alhajin sannan suka tashi suka fita batare da kowa ya furta komai ba.

Safwan kam kansa ya kulle ne gaba 'daya jikin sa ya mutu, yana so yayi wani abin amma sai ya rasa ta ina zai fara, Ammi zai fara tunkara ko Alhaji Baba?
Dukkan su bai san suna da tsaurin ra'ayi irin haka ba...dalilin ma kenan da ya hana shi ta6uka komai kawai ya tsaya tunani.

'Bangaren Deen ma hakn ne domin kwata-kwata ya kasa sanin inda zai dosa, har tanga'di yake yi idanun sa na ganin bibbiyu, gani yake kamar rayuwar sa ne ta gangaro tazo 'karshe..."

Ganin ya nufi waje ya sanya Safwan bin sa abaya, wajen mota ya shiga ya kishingi'da yana tunani, sun 'dauki tsawon lokaci ahakan sannan yace sutafi gidan su Noor...ko yanayin maganar sa kadai ma sai yabaka tausayi domin duk ya saduda yayi sanyi gaba 'daya.

Koda suka je can kuwa basu samu kowa a gidan ba sai Ummie, Ummah bata nan sai Ummi ka'dai itace kuma ta sanar da su cewa ai Hudah tayi tafiya yau in nan da safe har da akwatin ta ma ta tafi.

Deen kansa yaji ya sara masa da 'karfi dai-dai da bugun da zuciyar sa.
Da mamaki ya kalli Ummie sai ma ya kasa fa'din komai.
Safwan ne ya tambaye ta sunan garin da taje Ummie tace ita kam ta manta.
" Ana wata ga wata"!
Safwan ya furta a fili yana shafo kansa.

Juyawa kawai Mu'een yayi ya fita yana jin tamkar ya zubda hawaye...Ko cikin motar Safwan ka'dai ne ke iya magana yana bashi baki.
Da kalamai masau sanyi.

*Darazau...* shine sunan gari na farko da ya fara zuwa cikin ransa saboda ta ta6a zuwa garin da jimawa kuma bai manta ba, amma kuma ko yaje in ma ai be san ta ina zai fara ba tunda shi ba sanin gidan da taje yayi ba, ya gwada 'kiran layin Noor yafi sau ashirin amma ko guda bai tafi ba _is not reachable_ ake ce da shi.

Yanzu kam yasan Allah ne ka'dai gatan sa...cuz bai san ta inda zai tunkari wa'danann abubuwan ba, wani bin.sai yaji tamkar ya sjare kowa kawai ya koma yayi zaman sa har lokacin da zasu sa'kko sai dai bazai iya ba, ya riga ya yiwa Noor al'kawarin zai zo ya bawa su Ammi hakuri so baya son ya sa6a alkawarin sa.
Sosai yayi danasanin rashin ajiye numbers in 'yan uwan ta cikin wayar sa, numbern Yah Usman ka'dai yake da shi wanda shima 'din ko da ya 'kira bai samu ta shiga ba.

Haka ya dinga gwadawa lokaci zuwa lokaci, duk ya fice hayyacin sa ganin kamar rayuwa na shirin juya mai baya.

Bai samu numbern Yah Usman ya shiga ba har sai kusan sha biyu na rana sannan, nan kuwa yayi 'karfin halin nutsar da muryar sa gudun kar ya fahimci abinda ke faruwa.

Numbern Addah Maryam ya nema kawai batare da yayi mai wani dogon bayani ba.

Yah Usman kam batare da wani tunanin ba ya tura masa numbern yana mai sake yi masa taazitan Baby cuz bai samu zuwa ba yayi wata doguwar tafiya ne zuwa 'kasar yarbawa, zuciyan sa cike da jin da'din yau Mu'een ya tuna da su.

Sai da ma ya kira Addah Maryam din jin layin nata na tafiya sannan ya tura masa...shima atake batare da 6ata lokaci ba ya 'kira ta jikin sa har rawa saboda farin cikin da ya lullu6e shi, ya'ki yin magana ne gudun kar ta san shine itama ta kashe wayar ta ko kuma ta hana shi ganin matar sa idan yaje, yafi son yayi musu bazata a ganin sa hakan shi zai sa ya samu sau'kin ganin ta.

Ajiyan numfashi Safwan ya sau'ke yana dawo da zaman kafafun sa dai-dai yace" Ina muka nufa yanzu?"
" Safwan Darazau zamu je, inaga can Noor ta tafi".

Kai kawai ya jinjina tare da yiwa motar key, cike da farin ciki suka kama hanyar Darazau da tambaya har suka isa.

Sai da suka je in kafin ya sake 'kiran Addah Maryam da wani layin daban wanda ya san ba kowa ne ya sanshi da shi ba.

Safwan ya bawa wayar gudun kar ta 'dago sautin muryar sa bayan ya shirga masa 'karyar da zai yi mata.

Murmushi kawai Safwan yayi cikin ransa yace" Rayuwa kenan".

Koda ta 'daga suka gaisa sai yace da ita 'dan aike ne shi daga Shuwarin amma bai gane kwatancen gidan ta da aka yi masa ba shiyasa ya 'kira.

Addah Maryam da mamaki tace" 'Dan aike kuma? waye ya aiko ka?"
Kallon Yah Deen yayi sai yayi saurin ha'da la66an sa yace" Ummah..Ummah" Batare da sauti ya fito ba.

Safwan da bai gane ba sai kawai yace mata" Mama ce.."
" Mama kuma? bangane ta ba, Mamar waye kenan".
" mamar ki mana..ina sauri ne please kiyi min kwatance da wuri".
ya bata amsa da alamun 'kosawa.

Ranta bai so ba amma haka dai ta kwatanta masa, sam bata ji batun ya kwanta mata ba dan Ummah bazata yi aike batare da ta sanar da ita ba.
Gashi wayar ta ba kati a lokacin balle ta kira Umman taji.

Ko data kwatanta musun ma da 'kyar suka gane gidan hakan ma sai da suka ha'da da tambaya tukunna.

Sun sha wuya sosai ga zafin rana amma Yah Deen duk bai damu ba matu'kar zai ga Matar sa bashi da damuwar komai.

Yasan ganin ta ka'dai can heal what he is feeling a zuciyar sa, dawo da Noor rayuwar sa kuwa yasan dai-dai yake da shiryuwar sa da iyayen sa, yasan zata shige masa gaba dan tana da kyakykyawar zuciya, bata biyewa son zuciyar ta ta 'kuntata wani.

Tarba mai kyau Addah Maryam tayi musu bayan fahimtar cewa Mijin 'kanwar ta ne yazo ashe".

Sai da ta sake yi mai gaisuwan Baby cike da nuna tausaya suka jimanta lamarin kafin ta tambaye shi lafiyar 'kanwar ta.
Sosai suka yi mamaki da jin abinda ta ce dan ko ka'dan babu alamun wasa tattare da maganar ta...duk da hakan cikin zuciyoyin sai suke ganin kamar wasa da hankalin su kawai take so tayi.

Ta fahimci sauyin yanayi tattare da su wanda ta lura tambayar Noor da tayi sai da yasa suka dubi juna amma bata wani sa akanta ba kawai ta 'karasa da tambayar su aiken da suka ce an turo su.

Sam Addah Maryam bata san abinda yake faruwa ba, tun bayan da suka dawo daga Bauchi gaisuwar Jasmine gidan ta taho saboda ta bar yara kuma tun daga ranar bata sake jin komai ba, ko Noor ma sukan yi waya da ita lokaci zuwa lokaci amma bata ta6a sanar da ita komai ba game da ita ba.

Safwan ne ya gyara zama da kyau yana duban ta yace" Antyn mu afuwa muka zo nema, dan Allah ayafe mana abinda ya riga ya faru...Anty ki taimaka ki ha'da mu da Noor ko na mintina uku ne dan Allah badan mu ba..."..

Zaro idanu Addah Maryam tayi tace" Noor kuma? Rabo na da ita tun bayan bari na Bauchi sati kusan hu'du kenan yanzu ban 'kara sanya ta a idanu na ba sai dai awaya".

" Ya salam!..."
Yah Deen ya furta gami da dafe kansa dake sara masa, zugum ya zauna yayi 'kasa da kansa yayin da Safwan ya furta Innalillahi wa innah ilaihi raji'un...ayanda suka ga yananin da ta shiga ka'dai ma ya ishe su fahimtar iya gaskiyar ta kenan.
" Wai me ke faruwa da ita ne ku gaya min?"
Ta sake tambayar su cike da damuwa dan ta fara fahimtar akwai wani abin daban da ita bata da masaniya akai.

" Kina nufin ba nan ta zo ba? Yau in nan fa akace tayi tafiya ta bar Shuwarin ina taje to? munyi tunanin nan tazo shiyasa muka biyo sahunta..."
Safwan ne ya fa'di hakan yana duban Addah me Maryam dan sake karantar yanayin ta.
tace
" Ikon Allah..bata iso nan ba wallahi...kuma mun kwan biyu bamu koyi waya da ita ba Ina Hudah ta shiga ni Maryamu...".
Ta 'karasa maganar cike da alamun rikicewa.

Wayar ta ba kati amma haka ta gwada layin nata kuma bai shiga ba...itama 'din rikicewa tayi sosai kuma sai bata yi tunanin ayi 'kiran Ummah ba...

Yah Deen ta shi yayi Safwan na shirin ce da ita ta tambaya musu Ummah ko ta sani...amma sai ya ga yacrike kai sosai yana shirin zubewa...da sauri Safwan ya mike ya rike shi suka fita.

Direct mota suka koma ko sallama babu wanda yayi mata suka kama hanyar Bauchi...numfashin Mu'een na fita sama-sama saboda tashin hankali.

Ko tsakanin su ma babu mai ce da wani 'kala domin duk tunani ne fal cikin rayukan su, Deen tunanin inda Noor ta shiga yake yi yayin da Safwan ke tausayawa halin da abokin nashi yake ciki.

Comment
Vote
Share

*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
Chapter 184 · 0% Book details