← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 211

Sashe 9

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Noor na jin haka ta bar jikin sa da sauri tare da marairai ce fuska.

Gira ya 'dage yana kallon ta da mamaki sai yace" ya akayi kuma? sai yaushe zaki saki jikinki a gidan nan please....kuma ma banda abinki wama zai an abinda ya faru tsakanin mu ko da ma an sani 'din ni ba mijinki bane?"

" Ni dai Allah kunya nake ji Yah Deen please kayi ha'kuri".

Murmushin gefen baki yayi tare da sake kamo hannun ta yace " kunyan wa kike ji a gidan Babanki ne fa da Ammeen ki ko kin manta?"

Pouching gefen cikin sa tayi sai yayi saurin dafe gurin tare da furta " awsshh ".

" ai na girma sosai yanzu".
Tace tana murmushi.

Sai yace " ni banga hakan ba gaskiya tunda kunyar su ma kike ji yanzun".

'Dago ta yayi daga jikin sa tare da fa'din " ni dai tashi kiji kinsan ban jurewa ko ya zakiyi dani to yanzu".

"Na yau ka'dai kam ka bini bashin sa amma ni bazan iya yin komai a gidan Alhaji Baba ba".

" Naji to....then kiss me".
ya fa'di kamar me irgo maganar.

Kallon fuskar tashi ta tsaya yi with smile on her face, a hankali ta matsar da kanta kusa da shi ta kama lips 'din sa.

Deen ba yau yasan halin ta ba dama matu'kar suka zo garin nan to baya sake samun kanta koda kuwa kwana nawa zasu yi, hakan ne ma yasa shima yake hanawa kansa bu'katar muddin suka zo tare har sai sun koma Bauchi, yau 'din ma bai san me yasa yake jin son kasancewa da itan ba.
Idanun sa har sun 'kan'kance jin yanda take sarrafa harshen ta cikin bakin sa da niiyar sa ba zai tayata ba amma tsabar shauki bai ma san lokacin daya fita za'kewa ba, sosai yake sumbatar da da dukkan iyawar shi tare da bin ilahirin jikin ta da shafa.

Ko lokacin data ji yaja mata Zip ma bata damu ba cuz tasan idan ba barin sa tayi ya rage zafi ba ba nutsuwa mata zai yi ba.

A zafafe yake romancing 'din jikin ta dan gaba 'daya hankalin sa a tashe take yama manta da cewar cikin mota yake.
Sai daga baya ne ya an kara da cewa a mota suke jin bai sake sosai ba, kuma ma a 'kofar gidan mahaifinsa Alhaji Baba.

Barin ta yayi da sauri amma still sai ya lafe a jikin ta kamar 'dan yaro a hankali yace " me yasa baki tuna min cikin mota muke ba?"

" ai nima mantawa nayi"
Tace da shi tana 'ko'karin gyara jikin ta.

Deen kuwa sai ya matsa ka'dan daga jikintan tare da jan hancin ta yace " kuma a hakan kike cewa kina kunyar su Alhaji bacin gashi baki yi acikin gida ba kuma kina shirin yi a 'kofar gida idan ya ganki fa".

Juyawa tayi ta kallo 'kofar gidan sai ma yanzu ta tuna da hakan.
A 'dan gagguce tace " Zipping min rigan to mu tafi da sauri ".

Murmushi Deen yayi sannan yaja mata Zip 'din ya rufe mata.
" muje to Yah Deen da sauri".

"Dan ma na tuna miki".
Yana maganar ne tare da 'ko'karin kunna motar.

A hankali yaja suka bar haraban wajen, sai da suka yi tafiya mai 'dan nisa kafin ya sake tsaida motar.

Kallon tambaya Noor tabishi dashi sai yayi 'dan guntun murmushi tare da fa'din " muje gidan mu?" Yayi tambayar yana mai kallon cikin idanun ta.

Noor kam wani tashin hankali ne ya ziyarce ta da jin furucin nasa, idanu ta waro a kansa itama sai ta jefa masa tambayar" gidan mu kuma Yah Deen? saboda me?"
Muryar ta na rawa tayi maganar saboda tsinkewar da zuciyar ta tayi.

Deen kuwa bai damu ba sai ma ya kwantar da kansa akan sitiyarin motar a hankali yace " me yasa kuma zaki ce Nuree?.....i need u kema kinsani ai".
Kansa a kan sitiyari ya fa'di hakan batare da ya kalle ba cuz shi ka'dai yasan abinda yake ji a lokacin.

Sai tace
"Amma Yah Deen ai naga gobe zamu koma, kuma fa kaga gidan yayi 'kura sosai dan an da'de ba'ayi amfani dashi ba.... ta ina zamu fara gyara shi...please kayi ha'kuri idan mun koma gida mana kaji?"
Ta 'karashe maganar da sigar lallashi ha'di da shagwa6a.

Deen kuwa 'dagowa yayi a take tare da juyowa ya fuskance ta da kyau sannan yace" ni bazan iya ba Nuree ke bakya jin tausayina ne? sati nawa rabona dake dan Allah da kike wani kawo min silly excuse....nima 'din ai gobe zan koma ko haka kike so in tafi da damuwa ta?"

Kai ta jijjiga masa a hankali alamar " ah ah"

Sai yace " muje to ai gyaran 'daki 'daya bazai bamu wahala ba".
Yana maganar tare da 'ko'karin sake tada motar.

Noor kam wani zazzafan hawaye taji ya sau'ko mata akan kuncin ta, wani 'daci take ji a zuciyan ta sam ta tsani wannan gidan ko ganin sa bata son yi a rayuwar ta me yasa shi bazai fahimce ta ba?, ko laifi tayi da take tsananin son shi da kishin sa.

Rintse ido tayi tana tunanin hawaye na bin fuskar ta suna sau'ka da gudun gaske.

Deen ma fasa tada motar yayi ya 'kura mata idanu yana kallon ta, sam bai yi mamakin halin data shigan ba amma yanzun sai yake ganin kamar harda rashin damuwa da lamarin sane ya sanya ta hakan.
Tsawon mintina uku suna a haka ganin kukan nata ba mai 'karewa bane ya sanya shi 'kiran sunan ta.

Bu'de idanun tayi ta sau'ke su a kan fuskar sa, saurin kawar da nashi idanun yayi gefe, domin ganin cikin 'kwayar idanun Noor cike da hawaye na matu'kar gigita masa lissafi, baya so ya 'kara wani abu akan abinda yake ji a yanzun.

A hankali ya bu'di baki kamar bazai yi maganar ba da 'kyar ya furta " bu'katata ce ta sanya ki kuka ko Nuree?"

Bata bashi amsa ba sai kawai tayi 'kasa da idanun ta tayi shiru.

" Tambayar ki nake ki bani amsa".

Hawayen ta tafara sharewa da hannun ta 'daya tare da dai-dai muryar ta amma still da yanayin kuka cikin maganar sai ya kasance shagwa6a ziryan ne ya fanshi muryar tata " ba haka bane fa Yah Deen... ni dai dan Allah kar muje wancan gidan ban son shi".

Juyowa yayi ya kalle ta sau 'daya tak sai ya kuma ya 'dauke idanun sa. Batare da ya 'kara furta komai ba ya tada motar yaja bai tsaya ko'ina ba sai a 'kofar gidan Ummah.

Parking kawai yayi yana jira ta fita ya wuce kansa na kallon gefen hanya.

Noor kam ji tayi hankalin ta ya tashi sosai da ganin yanayin nasa, sai dai hakan ba zai ta6a sawa ta amince ta bishi wancan gidan ba duk kuwa da tasan kalar yanayin sa ha'kurin sa ka'dan ne ta wannan 6angaren.

Kallon gefen fuskar sa take yi duk da babu wani haske sosai amma farin watan da ke haskawa shine ya bata daman ganin sa da 'dan kyau.

Sun kai mintina kusan shida a hakan batare da wani yayi magana ba, shi Deen jira kawai yake ta fita shima ya wuce yayin da ita kuma Noor take ta sa'ka da warwara cikin zuciyar ta har ta yanke shawaran da taga ya fi mata sai dai tana ganin bazata iya wucewa gida ta barshi a cikin wannan halin ba ita kanta hankalin ta bazai kwanta ba.

Ganin tana 6ata masa lokaci ne ya sanya shi waigowa a nutse yace mata " ki wuce gida dare nayi ina so inje in huta nima.....".

Kafin ya rufe bakin sa sai tayi saurin kwantar da kanta bisa kafa'dan sa tare da dabaibaye shi da hannayen ta duka biyu.

Shi kam shiru yayi bai kula ta ba jira yake yaji manufar hakan.

Hawaye ne ya sake gangaro mata sai tayi saurin rintse idanu.....shima danshin dayaji ne gefen wuyan sa ya sanya shi fahimtar kukan da take sake yi.
Sai ya kai hannun sa kan nata hannun yana 'ko'karin raba ta da jikinsa amma ta no'ke.

A hankali tace " Yah Deen please kayi ha'kuri kar kayi fushi dani.....ni ban isa in gujewa bu'katar ka ba kai kanka kasani koda kuwa a ina ne ina maraba da kai amma dan Allah kar muje wancan gidan kaji?"
Cikin natsuwa tayi maganar shi kansa sai da yaji natsuwa ta shige shi, musamman da ya fahimci maganar tata inda ta dosa, sai dai shi kuma ba zai iya kusantar ta a mota ba in ma hakan take nufi kenan.

'Dago hannunsa yayi tare da kai wa kan fuskar ta ya shafa a hankali sai ya cire hannun sa, nata hannun ya sake 'dagowa ya kai gefen fuskar sa yasha da hannun nata suna kallon juna yace " karki damu i'm ok...ki je gida sai safe".

Bata fita ba sai take binsa da idanu kamar me san karantar wani abu a fuskar sa, ganin hakan yasa Deen ya saki hannun nata sai ya kai hannu ya bu'de mata 6angaren da take tare da sake nuna mata bu'da'dden 'kofar.

Karyar da wuya tayi gefe tana kallon idanun sa sai ya jijjiga mata kai left and right.

Slowly taja jiki ta fita daga motan tare da rufo masa 'kofan sai ta tsaya tana jiran wucewar sa.
Yasan halin ta sarai yanzu sai ta'ki shiga gidan ta tsaya bin bayan motar da kallo idan yayi gaba, shima 'din kuma baya jin zai iya tafiya ya bar ta a wurin tsaye ba tare da yaga ta shiga gida ba cuz dare nada sharri kala-kala, dan haka sai yace da ita
" 15seconds ban yadda ki 'kara anan ba maza ki shiga gida".

Motan ya tayar dai-dai itama ta juya ta kama hanyar shiga gida, bai ja ba sai daya tabbatar ta shige kafin ya tafi.

*Ayi ha'kurin jina da akayi shiru na tsawon lokaci plz...........JASMINE NA GAISUWA SOSAI* 🤠

*Salmerh ce* 😍
[11/17/2019, 9:35 PM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
Chapter 9 · 0% Book details