Sashe 1
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)
By
*Salmerh MD*
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
Daga marubuciyar littafin CAPTAIN ABBAS.
*Masoyana bani da bakin gode muku domin irin 'kaunar da kuke nuna min tana matu'kar sanyani farin ciki..... fatana kawai shine kuma Allah ya faranta muku fiye da yanda kuke min.........Gashi dai yau na sake dawo muku da wani labari shima mai suna NOORUL fatan zaku bani ha'din kai ku kuma raka ni da da'da'dan sharhohin ku kamar yadda kuka saba....😍
🤞🏻 ~*AKAFTA*~ 👇🏼
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
🅿 *1*
Babban waje ne ba na wasa ba, zaka iya ambatan sa da suna wani tsararren mansion ko wani abu daban, sai dai ina sam ba haka bane......wannan tsarin na daban ne kamar yadda yake na musamman, bazaka ta6a fahimtar menene shi ba a tsanake daga yanayin wurin saboda sam ba'a yi shi yanda kallo 'daya zaka fahimce shi ba in ba kayi duba da Babban farin sign board 'din dake kafe gefe da gate 'din building 'din ba ko kuma in dama asali kasan mene shi ba, nima a sign board 'din na fahimci ashe asibiti ne nan 'din.........
A hankali wata ba'kar mota ha'd'diya mai sanyin yanayi take shigowa harabar wurin tamkar ba son jan motar ake yi ba, duk da ba'kin tinted glass 'din da ya lullu6e jikin motar amma hakan bai hana securities 'dagawa mamallakin motar hannu ba alamar gaisuwa, duk kuwa da cewa ba ganin sa suke yi ba amma saboda girmamawa yasa sukayi masa hakan, da yake ma sun san halin sa bayan hakan baya bu'katar komai dan ko kayi wanda yafi hakan ma ba bu'dan baki zai yi ya amsa maka ba wata'kila ma ko kallon inda kake ma bayi zai yi ba sa6anin hakan kuwa zaka iya samun kyautar murmushi daga gareshi...... cikin sa'a kuwa yau 'din sai gashi yayi 'kasa da ba'kin glass 'din motar ya 'dago musu hannu shima murmushi sukayi na jin da'di suna ayyana canjin yanayin sa na yau 'din.
Sosai yake birge da yawa daga cikin su dayake a zahiri sun san halin sa mutumin kirki ne na bugawa a jarida koka'dan bashi da matsala a idanun su bayaga rashin son hayaniyar sa.....wannan kuma su a wajen su ba wata babbar matsala ba ce tunda sam baya shiga ha'k'kin su ta fuskar ayyukan su abinda ke gaban sa kawai yake yi.
Wannan kenan.
Kamar yadda ya shigo a hankali hakan ya 'karasa har parking space inda musamman aka tanada dan ajiye motoci, gefe ka'dan da sauran motocin yayi parking nasa.
Bai bu'de marfin motar ba koda yayi parking 'din sai da ya 'dauki a 'kalla kusan mintina takwas sannan ya bu'de motar a hakan ma sai da ya 'kara 3mins akai kafin ya zaro 'kafar sa 'daya sannan ya ya fito gaba 'daya ri'ke da brief case 'din a hannun sa na hagu yayin da 'dayan hannun ke ri'ke da key 'din motar tasa gami da wayar sa, a nutse ya juyo ya fara tafiya bayan ya danna wa motar security ya nufi hanyar da zata sada shi da cikin ma'aikatar.
'Kofar da kanta ta bu'du kasancewar ta auto ce ita ke operating kanta ba sai ka wahal da kanka ba.
Stairs ya nufa da 'dan hanzari tare da duban agogon dake 'daure a tsintsiyar hannun sa wanda kana gani ko ba'a sanar da kai ba kasan cewa na musamman ne.
Shiru ya samu saman bayan hawowar tasa inda direct ya nufi office 'din sa yasa hannu ya bu'de tare da bismillah cikin zuciyar sa ya nufi faffa'dan table 'din dake cikin office 'din ya zagaya yaja kujerar data kasance mazaunin sa kenan in har ya shigo office 'din.
Jakar dake hannun sa ya ajiye sannan ya zauna tare da 'dago wayar sa da yaji ta fara 'kara alamar 'kiran sa akayi.
"Hi"
Yace tare da jingina da jikin kujerar ya lumshe idanun sa fuskar sa ba yabo ba fallasa ya sake fa'din " Yes na iso mana...."
" ah ah ba yanzu ba"
yana gama fa'din hakan yayi ending call 'din tare da gyara zaman sa akan kujerar yana juyi.
Bai jima da gama wayar ba aka fara gabatar masa da files 'din marasa lafiya da yake lokaci ya 'dan ja kusan 'karfe tara yanzun shiyasa batare da wani 6ata lokaci ba yafara duba patients.
'Karfe shabiyu ya dakatar da duba marasa lafiyan saboda gajiyar da yayi sai a sannan kuma yasake 'daukan wayar sa yayi dialling wata number tare da ha'da wayar da kunnan sa.
"Assalamu alaikum Yah Deen!"
Kamar jira akeyi ya 'kira daga 'dayan 6angaren aka 'dauka tare da doka sallama cikin natsuwa inda tayi maganar fuskar ta cike da annuri.
Amsa ta yayi da fa'din " Na'am.... Nureen Deen i missed u alots"
Shima yayi maganar yana sake lafewa kan kujerar dayake zaune akai harda lumshe idanu.
Murmushi tayi ita kam sannan tace " Ni dai yaushe zaka dawo please ka fa da'de wannan karan kusan fah satin ka biyu".
Idanun nasa a rufen yace " kina kewata ne?"
Kwafa yayi tare da juya idanu tana murmushi tace
"Ba dole ba, ai kaima abinda kasani ne ko sai na sake tuna maka?"
Sai yace
"Da zanfi son hakan ai idan naji shi a zayyane daga furu in ki".
" Allah yah Deen baka jin magana...kai kullum sai na ta maimaita maka abu 'daya ne?".
Ta 'karashe maganar tamkar zatayi kuka.
Hankalin sa a kwance yace " toh ai ni nafi son hakan ya za'ayi"
Ganin kamar shi bai ma wani damu ba yasa tace " ni dai please ka dawo in yaso sai ka koma kaji.....?"
"Sai nayi tunani tukun na"
ya bata amsa atakaice.
Tana shirin sake yin magana sai ya dakatar da ita da fa'din
" ya isa plz......! kar ki damu soon zan dawo kinji nima am so eager to meet u Nureee...."
Murmushi mai sauti tayi before saying a word sai ya rigata yin magana da fa'din " where is my diamond?"
Dama tasani tunda yace ya isa please 'din nan tasan 'yar sa zai tambaya bakomai ba.
'Dayan hannun ta ta 'dago ta 'daura shi akan cikin ta sannan ta amsa shi da fa'din " ai tana school yah Deen bata dawo ba".
Ta 'karasa maganar tana 'dan ha'de gira.
Shima goshi ya 'dan dafe daga 'daya 6angaren tamkar suna wuri 'daya da ita tare da furta " upps sorry Nureee kinga ma na mance ne amma please ki 'kirani idan ta dawo kinji?"
Da " uhm" ta amsa shi daga nan tayi shiru shine dai ya furta " i love u Nuree i have something to do now.....bye owk"
Shiru tayi masa bata tanka ba daga haka kuwa ya yanke 'kiran.
'Karfe 12:50pm
Ta sake duba agogon dake cikin wayar ta karo na barkatai domin kuwa abin yafara bata haushi duk da ba wai yau ne hakan yafara faruwa ba amma zuwa yanzun abin na 'dan fara 6ata ranta ganin yanda lokaci ya tafi amma har yanzu Jas bata dawo ba kuma tasan dawuri driver yake tafiya school 'din nasu yayi zaman jiranta har a tashi, amma ta rasa mai yasa sai sun da'de kafin suke dawowa gida, kusan kullum sai sun 6ata lokaci wanda ta fahimci hakan a 'yan kwanakin nan dayake bata shiga school sosai ita 'din, Nursery school dai kowa yasan ba'a haura 12:00pm batare da an tashe su ba amma tana ganin kamar na Sani yana yawa lokacin......bata gama tunanin nata ba Driver yayi sallama hannun sa 'dauke da wata 'yar kyakkyawar yarinya da bazata haura shekara biyar ba yayi mata 'daukan jarirai da lunching box 'din ta a hannun sa be dire ta ko ina ba sai gefen mahaifiyar ta dake zaune kan kujera, bata wani nuna alamun rashin jin da'din ta game da hakan ba cuz tasan kusan kullum a hakan yake kawo ta ya zaunar da ita, cikin natsuwa yayi wa matar dake zaunen barka da gida tare ta amsa shi sannan ya bar 'dakin yana bayyanar da murmushin sa afili.
Binsa tayi da idanu haka kawai sai take 'dan jin haushin sa a ranta, daf da zai bar 'dakin sannan ta furta " Sani yau kuma mai ya rike ku har haka?"
Sosa kai Sani yayi sannan ya juyo ya kalle ta suna ha'da ido da jas sai yayi murmushi ita kuwa 'dan yatsan ta 'daya ta 'daga ta kalli mahaifiyar tata tare da fa'din " Mummy kinsan me yasa muka da'de ne.......?"
Sani na jin haka yayi saurin dakatar da maganar nata da fa'din " Ranki ya da'de wallahi mun 'dan yiwa wani abokina lift ne shiyasa".
Jas kam shiru kawai tayi tana rarraba idanu tsakanin Sani da mahaifiyar ta jin 'karyar da ta tafka duk da 'karamcin shekarun ta amma sarai tasan 'karya ya shirga.
Matar ne ta sake cewa " amma ai Sani ka dawo da ita gida tukunna kayi yawon naka ai ko? Jasmine 'karama ce kasani kuma ko mahaifin ta yaji cewa kana yawo da ita cikin gari ba zaiji da'di ba".
Sani cewa yayi
"Insha Allahu Hajiya baza'a sake ba"
Kauda kai tayi tace
" Allah yasa "
A 'kasan ma'koshi tayi maganar tare da maida duban ta kan 'yar ta, shima Sani ba tare da ya sake furta komai ba ya fita ya bar 'dakin.
Matar bata wani damu da shi ba har ya fitan wanda bayan fitar tashin ne tace da 'yar yarinyar " Jas tun 'dazu Daddy yake ta tambayar ki fa....." bata 'karasa abin tayi niyyan fa'dan ba ta kai hannu kan fuskar Jas 'din da kulawa ganin sauyi tattare da ita atake ta sauya akalar maganar da fa'din " Jas me ya sami bakin ki yayi ja haka ?"
A ru'de tayi maganar
Jas kuwa sai ta 'daga hannun ta itama i zuwa bakin sannan ta ce
" bakina?"
Jas 'din ta tambaya
Da sauri ta amsa ta da fa'din
"Ehh mana... ko kin bige ne a school?"
Kai ta juya mata alamar "ah ah"
Uwar sai tasake fa'din
" Toh menene? Har fa 'dan kumburi naga yayi"