Sashe 98
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kaya ne a jikinsa ba in wando da riga mai layi layi mai dogon hannu tana da kalan Ash da ruwan asa a zanen ta sannan ya yi zanzaro kansa kuma ya sanya P. Cap baka a jikin P. Cap in an saka Captain da manyan ba i. Kafarsa cikin wani bakin Booth in takalmi mai rufi ba ma wannan ba sai wani ba in gilashin da ya rufe wayar idanuwansa a ciki ba ta ta a ganinsa da glass ba sai yau shi ya sa ta ga ya yi mata wani irin kyau da warjini Ganin Auwalu ya sa ta koma gefe tana jiran su gama ai ta san shi a baya matashi ne amman yanzu Allah sai ta ga kamar ya yi mata tsufa, ba su jima suna mgana ba suka yi sallama shi Auwalun daman gida zai shiga ko kafin Mimi ta fara gaishe shi, ya kalleta cikin fara'a yana fa in" Amarya ina kwana? Allah yasa dai ba ki yi fushi ba? Da sauri Mimi tac e" Ina kwana, a a wallahi ya mutan gidan? Ya amsa da lafiya lau suna gaishe su, suna ma nan zuwa su gaisheta ta ce tana jiran su ya bi ta da adawo lafiya. Aji kuma daman tuni ya koma cikin mota ya kame, bayan shigewar Auwalu ta bu e murfin mota ta shiga da sallama.. "Assalamu Alaikum." "Wa'alaikis Salam." Ta cikin bakin gilashin sa ya ke are mata kallo ba ta sani ba, bayan amsa sallamar da ya yi har suka kama hanya kanzil bai ce mata ba itama ba ta ce masa ba, Sai ta maida kanta ta jikin Kofa tana kallon waje, motar ta yi sanyi kalau amman tsit sai karan nurza Sitiyarin in da ya ke yi, Ita dai ba ta nuna masa hanya ba amman da alamu kamar ya san ma'aikatan na su. Wayarsa ce ta fara vibration da karfi tunda ta na saman motan ne daga gabansa, sai ya zura hannunsa guda aya ya auko wayar ta gefen ido ta ga sunan mai kira sai da sunan ya kusa saka ta dariya. "Mu'azzam Gaddafi anjuma" Sai ta yi saurin danne bakin ta, shi kuma sai ya auki wayar ya saka a speaker ya ijiye ta nan saman cinyarsa dai dai lokacin da Mu'azzam ke fa in" Barka da safiya Yaya Mansoor.' Ya amsa mai da lafiya lau Mu'azzam ya Junior? Mu'azzam ya ce" Lafiya lau, Yaya Mansoor gobe Birthday ina." Yamutsa fuska Mansoor ya yi kafin ya ce" Nasani, kai yaro ne da kake murnar gobe Birthday in ka? Shekaran ka talatin da aya , kana da mata kana a, so ka daina abun yara don Allah Mu'azzam." Sai ya bar Mu'azzam da fa in" Amman ni a wajen ka yaro ne arami, Saboda haka ka turomin Birthday gift ina." Mansoor ta ga ya yi mirmishi har hakoransa su ka bayyana kafin ya ce" Shike nan i will, mu yi mgana anjuma ina driving ne." Sai Mu'azzan ya amsa da Allah ya tsare sannan ya katse kiran. Mimi na gefe ta na jin su, shi kuma sai ya hau ka a kai, bai ga shekaran da ta za ta zagayo ya manta ranar arin shekarun kanin na shi ba, shi ya kan manta na shi amman ba ya iya manta duk wani abu mai muhimmamcin da ya shafi Rayuwar Mu'azzam. A.c in motar ya ure sanyi ya fara yawa Mimi ta fara takure jikinta alamun sanyi, Slsai ya kalleta kafin ya ce" Da sanyi ne? Sai ta gya a kai, kawai sai ya jinjina kai kafin ya ce'" Hukuncin matar auren da ta saka turare za ta fita kenan, wannan hukunci na duniya na kenan." Kallonsa ta yi shi kuma sai ya auke kai ya kara ma motarsa gudu yana fa in'" ki yi fatam kafib mu sauka ya sirace, in ba haka ba sai kin yi zaman mota ko na awa goma ne sai ya sirace tsab za ki iya fita" Kallon da Mimi ta yi masa sai da ya kusa sa ka shi dariya amma sai ya kanne lokaci aya yana fa in" Wato yau na ha u da bala'i ko? Nasan haka kike ta fa a a cikin ranki, gwara ma ki sani wallahi ba ni da Sau i a dukkan wani abu da ya shafe ki MIMI." Yana gama fa ar haka kuma sai ya koma ya ha e rai kamar ba shi ba, ita mamakin sa take yi ashe ya iya zence haka? Ba ta sani ba baya so ya saki layi ne amman yanayin da ya ke jin kansa a tare da ita kamar ya auke ta su yi ta shawagi a gari su dauwama a haka har gaban abada, ba ya so kowa ya ra u da ita sai shi ka ai amman ba shi da yadda zai yi, in har ya nuna a zalamarsa sirin zuciyarsa da ya binne shekara da shekaru zai iya fallasa. Ita sai lamarin sa ya ba ta dariya sai da ta an murmusa, abun mamaki sai gani ta yi sun yi kwanar shiga juction in gidan tibin su ba ta gama mamaki ba sai da ta gansu a kofar get in har ya yi hon akwai security a wajen sai sun ba ka takardan shiga sannan za ka shiga. Sai ya age gilashin motar aya daga cikin Security in ya leko yana fa "Barka da zuwa yalla ai." Sai kawai ya ci karo da Mimi sai ya washe baki yana fa in" A'ah Hajiyar Allah, barka da zuwa." Mimi ta kalli Aji, shi kuma bai kalleta ba sai ma hannu da ya mika ya kar i takardan hannun Security kafin ma ya yi ko arin tashi a jikin motar sai gani ya yi gilashin na agawa lokaci aya motar ta fara tafiya Megadi ya zura da gudu ya bu e musu get Aji ya fizgi motar da gudu har Kan Mimi na sunkuyawa, ita bakinta ya yi shuru ma domin lamarin ya fi arfin ta. Yana gama parking a parking space, Mimi ta yi kokarin fita sai ta ji ya rufe motar Sai ta juya tana kallon shi lokaci aya tana fa in" Turaren bai gama siracewa ba ne? Kai tsaye ya an sunkuyo kanta har sai da ta auke numfashi, sai da ya ja numfashi sannan ya koma ya zauna lokaci aya yana fa in" Eh to da saura ka an, ki jira nan da mintina goma" Kawai sai ta sauke Nunfashi ta koma ta zauna ta na ri e Jakar hannunta, bayan ta duba agogon dake tsitsiyan hannunta na hagu lokaci nata tafiya "Dokata ta farko a cigaba da aikin ki a wannan wajen da aurena a kan ki shine ban amince ki ri a mgana da kowani ba auye ba, ina da kishi sannan in raina ya aci ina da zuciyar da ba ta tunani sai bayan ta aikata abunda ta so, ya kamata ki kiyaye wannan." In mgana ta zama dole daga gaisuwa kada ta cigaba, ba na so ba kuma zan lamunta ba, kada ki yi tunanin ba na ganinki za ki iya yin abunda kike so na rantse da Ubangijina fatima in kika sa a umarnina zan sani kuma sanina ba zai haifar miki da makoma mai kyau ba, so gwara ki kiyaye." Ba ta ago ba, idanuwanta na kallon adon jakar hannunta ne, ya san acikin ranta tana sake sa e a kanshi ya sa ya ce" Na san kina cewa a cikin ranki wannan wani irin aure ne mai cike da sharu da da takura ha e da dokoki? Uhm aure ne kamar kowani aure amman ba kamar auren Aji ba, ni aurena ki kaddara kamar igiya sau ukun nan sai da ta ninka sau ari a kanki kin ga kenan auren ki da yadda za ki tafiyar da auran zai sha bambam da sauran ma'aurata." Mimi ba ta san lokacin da ta jinjina kai ba, domin ita ta daina ma mamaki, a yanzu tunanin ta aya me ya zo yi a in da take aiki? Ba ta samu amsar tambayanta ba ta ji ya bu e motar ya fita, itama sai ta bu e ta bangarenta ta fita, Kai tsaye ya kalleta kafin yac e" Ina ne office in shugaban ku? "Manaja? Mimi ta tambaya cikin mamaki kai tsaye ya ce" koma waye in dai shugabanku ne a wajen aiki.". ari tace acikin ranta sai ta ce a fili kawai ya biyo ta zuwa bangaren su na shashen labarai na gidan talabijin in karamchi. Tana gaba yana bin ta a baya kamar yana irga takunta. Tun da suka shiga wajen kowa sai kira Mimi AMARYA amman ba ta mgana sai dai ya e ta aga hannu shi kuma gogan kamar wani Bodygourd yana baya hannayensa zube cikin Aljihunsa yana taku kamar ya na cikin filin wasa. Daman ai da wanda a baya bai san wanda Mimi ta aura ba, da wanda ya sani yanzu kowa ya sani, domin a yanayin sa kawai kowa ya shaida mijinta ne sannan wasu da dama sun gan shi wajen aurin aure. Sannan arin abun mamaki ganinta da hijabi har gwiwan kafa sai ya ara ba su mamaki tana shiga babban falon da daga shi sai Office in News Manaja in su da Na misau ta fara cin karo . Ri e baki ya yi kafin yac e" Wata sabon gani? amarya ce nake gani ko gizo idona yake yi min." Domin har ga Alla bai lura da Aji ba sai da ya ga mimi ta yi mirmishi amman ba ta yi mgana ba sannan ya aga kai ya ga Ingarman namiji a gabanshi sai ya uge da bashi hannu suna gaisaawa, da sauri kuma ya juya ya na lalubar lambar Yusuf wanda ke sharhin kabaran wassani ya zo ga Mansoor Aji ya zo gidan talabijin in su. Tun kafin ta yi tambaya ta hango Manaja a office in sa tunda wajen gaba aya kofofn gilasa ne, sai kawai ta ce ma Aji bari ta shiga ta sanar masa duk yan intern in da ke wajen suna ta gaisheta da Sauran ma'ikatan su hannu kawai tak daga ma mutane ba su san jalin da ta ke ciki ba ne shiyasa. Manaja na ciki suna mgana da Salim