← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 185 OF 208

Sashe 185

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fa i, Cikin mamaki Inna Meri ta mi e lokaci aya tana fa in" Binta? ke ce da yamman nan? Kalamanta sun tsaya sanda ta ga Mimi ta dafe kanta. Jakar hannunta ta sulale tare da ledan mganinta wani irin juwa ce ta kwashe ta za ta kai asa cikin zafin nama Inna Meri ta tare ta lokaci aya tana fa in" Subhanallah Binta ba ki da lafiya ne? Ba mgana sai kawai Mimi ta saka mata kuka, Inna ta ru e ga shi ita ka ai ce a gidan Walida ba ta dawo daga wajen koyon inki ba. Sai ta rike Mimi ta taimaka mata zuwa cikin falo ta zaunar da ita a kan Kujera, amman sai ta koma ta kwanta Inna Meri ta yi mata zuru tana kallonta lokaci aya da nazarinta ba ta raba ayan biyu Fitinannen yaron nan ne ya yi wata tsiyar, Sake fita ta yi ta je ta kwaso jakan da ledan mganin ta duba daman ai daga ganin Binta ba ta da lafiya duk ta wani ashe, Inna ba maganin ta gani ta fahimta ba ita fa uwace tun lokacin da ta dawo Mimin ta zo mata sannu da zuwa ta ga yadda ta yi wani fari ta ga alamun Bintar na da shigar ciki, kuma a tunaninta daman dukkansu da ga ita har Baban Inna ba su san dashi ba. Falon ta koma ta iske Mimi na rawan sanyi sai ta shiga akin walida ta ijiye mata jakar da kedan ta auko mata blanket bargo ta rufa mata sai faman jera mata sannu take yi, ta koma ta kashe fanka falon sannan tunda mangriba ta kusa. Sai ta saki labulayen falon ta kuma rufe ofar falon da Window saboda akin dai ya yi umi, kitchen ta shiga ta kunna gas tunda ta iya sai ta ora ma Mimi ruwan zafi ta samu ta yi wanka ta gasa jikinta sai taci wani abu ta sha mgani ruwan na tafasa ta fito falon sai ta isken Mimin na barci sai ta kyaleta. Har a ka kira mangariba tana barci Inna Meri kuma ba ta tashe ta ba. Ta shiga ciki ta auro alwala ta zo nan falo ta shimfi a sallaya tana cikin sallar ne Walida ta shigo gidan Inna ma jin ta tana fa in"Laa Anty Mimi' Sai kuma ta le a ta kafin ta ago tana kallon Inna, goshinta ta ta a ta ji da zafi ka an sannan ta ga tana zufa. "Inna Anty Mimi ba ta da lafiya ne? Innar na sallah ya sa ta san ba za ta samu amsarta ba. Sai ta kwashi hijabinta da jakarta zuwa cikin akinta ta na shiga ta ji ana ta kiran waya a jakar Mimi ta gani yasan ta san wayarta ce ta bu e kenan ta auko wayar ta ga an saka Baby kafin ma ta yi wani abu wayar ta auke da alamu ila ba chaji ne, ba ta yi tunanin saka mata chajin ba sai dai ta maida mata wayarta cikin jaka, ledan maganin ta auka ta duba abun ya ba ta mamaki Yaya Mansoor ya yi tafiya ne? In ba haka ba me Anty mimi ke yi a gidan nan a dai dai wannan lokacin? Ba ta da mai ba ta amsa ba ya sa ita ma ta sauke kayan hannunta ta fa a tiolet ta yi alwala ta zo ta yi sallah tana cikin tahiyar karshe ta ji Inna na walamata kira shi ya sa tana sallamewa ta fice zuwa falo tana ce ma Inna ta na sallah ne lokacin da take kiranta. Inna Meri ta kalli Mimi da ta farka ta janyen bargo daga jikinta saboda zazzabin ya sauka zafi ma take ji, cikin tausayawa Inna ta ce" Sannu Binta ya jikin? Mimi kamar mai ciwon baki ta amsa ma Inna da sau i, Walida ma ta karisa kusa da ita ta zauna lokaci aya ta na fa in"Anty Mimi Allah ya baki Lafiya.". Ta amsa da Amin idanuwanta sun tasa abun ka ga farar fata duk fuskarta ta bayyana halin da take ciki. Walida Inna Meri ta kallah kafin ta ce"ki je kicthen na saka mata ruwan zafi ki sake ki kai mata bayi ta samu ta yi wanka ko jikin nata zai saki." Daman abin da Mimi take bukata kenan wanka, da sauri ko Walida ta mike ga aikin da Inna ta sakata. Sai falon ya yi shuru Inna sai ta maida hankalinta kan laziminta amman tana ganin Bintar na share walla, tausayinta ya kamata wai har yaushe ne Baban Inna zai bar rayuwar ar mutane ta zauna cikin salama ne? Ta san wlh tsiyar shi ce amman bari Bintar ta natsa ta ji abin d kuma ya sake aikatawa wannan karon. Bayan Walida ta kai mata ruwan zafi saboda jikinta ba karfi, ta mike Walida ta riketa hannun da a ka yi mata karin ruwa har ya kumbura da walida ta ta a wajen sai da Mimi ta yi wash, cikin sauri walida ta saki hannu kafin ta ce"Sannu arin ruwa a ka yi miki? Mimi ta gya a kanta kafin ta ce"Daga wajen aiki ne na fara ciwom sai Rukayya ta kaini asibiti can na yini aka sakamin ruwa da Allurai." Inna Meri da Walida suka ha a baki wajen fa in Allah ya ara lafiya. Cikin kayan Walida. Walidar ta za o mata wata doguwar riga, da yake daman rigar ta mata yawa ta kuma san za ta yi ma Mimin,Ai ko ta ji da in gasa jikinta sosai sannan ta auro alwala salla tun ta asuba rabon ta da yi, rigar ta saka ta yi mata sai dai tsawon ne ya yi mata ka an sai ta ce Walida ta bata zani ta ora saman rigar ta yi salla kuma Alhamudulillah a tsaye ta yi sallar tunda ta samu sau i tana i darwa Walida ta kawo mata Tea mai auri da buredi ta sha, sai ta fara dawowa daidai, bayan tea ta dafa mata Indomie da wai taci ta yi kat sannan ta sha ruwa, ba ta da alwala ya sa ta koma Tiolet ta yi alwala ta zo ta yi sallar Isha'i ta sha mganinta sannan Walida ta gyara mata gado ta hau ta kwanta, Inna Meri ta zo ta dubata ganin har ta kwanta ya sa ta kyaleta ta huta zuwa da safe. Walida ce ta kasa hakuri ta koma falo tana fa in" Inna wai anan Anty Mimi za ta kwana? Inna ta amsa mata da eh, cikin arim mamaki ta ce"To ko Yaya Mansoor ya yi tafiya ne? Inna ta kalleta kafin ta ce"Ban sani ba, ba na son tambaye tambaye mara amfani, ki je ki kwanta ki kula da ita tunda ba ta da lafiya." Ganin Inna ta ha e rai ya sa Walida ta kama bakinta ta yi shuru, ta yi ma Inna sai da safe ta koma akin ta shimfi a bargo a kasan cafet ta yi shirin kwanciya sannan ta kwanta ta auki wayarta tana danne danne. Ba su farka ba sai asuba Mimi ta ji da in barcin nan ta kuma ta shi kamar ba ita ba. Bayan sun idar da sallah Walida ta fita gyaran gida tunda da wuri take fita, Mimi ba ta san wayarta ta mutu ba sai da ta auko domin kiran Rukayya ta gaya mata ta cike mata takarda za ta auki hutu ba ta da lafiya sai ta samu wayar a kashe, da chazar Walida ta saka chaji sannan ta koma ta zauna a wajen har ta an farfa o ta kunna wayar ta na gama saituwa sannan sa o ya shigo wayar daga Aji tana gani ko dubawa ba ta yi ba, tana shirin kiran Rukky sai ga kiran jaheed ta san yana ta neman lambarta bai samu ba. Ta auka a sanyaye suka gaisa ya ce ya jikinta ta ce masa ta ji sau i. Kai tsaye ya ce"Ina fatan ba matsala? Kai tsaye itama ta ce"Da Sauki dai, za mu yi mgana daga baya." Da ga haka suka yi sallama bayan ya ce ta kira Rukky tana ta neman wayarta itama a kashe. Suna gama waya Rukkyn ta kira nan take gaya mata Bibi ta haihu aiki a ka yi mata ta samu mace suma asibiti, Mimi ta yi mata Allah ya raya sannan ta ce in ta shiga ma'aikata ta rubuta mata takarda sai ta ce mata eh za ta je. Daman Manaja ya san ba ta jin da i amman za ta je ta yi rubutun ta ba da, ko alama Mimi ba ta nuna ma Rukayya wani abu ba itama ba ta sani ba tunda Jahedd ya rike al wari bai fa a ma kowa ba . Tana gama abunda za ta yi da wayar ta sannan ta kashe wayar ta maida ta chaji, ta na shirin komawa ta kwanta Inna Meri ta shigo cikin akin sanye da hijabin da ta yi salla. Mimi na ganin ta da sauri ta duka ta na gaisheta Inna Meri ta zauna gefen gado lokaci aya tana fa in" Tashi ki zauna Binta ke da ba ki da lafiya? Sannu ya karfin jikin na ki? Ta amsa mata da sau i kanta na asa, Inna Meri ta yi mata fatan Allah ya kawo afuwa, shuru na wani lokaci sannan Inna Meri ta gyara zama lokaci aya tana kiran sunan Mimin. "Fatima.." Mimi ta ago tana kallon Inna Meri bayan itama ta daidaita zaman ta a nan gefen gadon na Walida ta amsa mata cikin antar da kai. "Kin auke ni a matsayin uwa Ko Fatima? Mimi ta gya a kanta sannan Inna Meri ta cigaba da fa in"Na kuma ga haka, tunda ki ka zo wajena ba tare da kin tafi ga Hajiya ko Mahaifiyarki ba na ji da i da kika mutumtani Binta, ki fa amin abin da ya faru kika zo gidan nan cikin wani yanayi kuma har kika kwana ban ga megidan ki ya zo bin bayan ki ba? Me ya faru? Ki fa a min kada ki oyemin komai domin Allah Fatima." Inna Meri ta arishe fa a tana kallonta Mimi kuma sai ta ji idanuwanta sun cika kwallah, ta kasa mgana jikinta har ya fara rawa Da
Chapter 185 · 0% Book details