← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 208

Sashe 115

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kyau? Walida ta ce" Na rantse da Allah Kin yi kyau Anty Mimi Ma sha Allah." Walida ta ri a zuzuta sai ta ji kanta ya fashe ta ara kallon kanta a madubi tana fa in" To ya? sarkan da komai ya yi kyau? Walida ta ce" Sosai ma. Komai ai ya dace da kwalliyar." Sai Mimi ta bu e mata wardrope ta ce ta zaba mata mayafi da takalmin da za ta sanya nan Walida ta za a mata wani mayafi mai kalan adon zanen yalin fuwalan jikin kayan mai ruwan fari fari kuma kamar milk, sai kuma wani farin takalmi mai an tudu ka an Walida ta ce Mimi ta sanya, sannan a ka koma fesa turare har sai da Mimi ta ce a barta haka tana dariya saboda Walida ne ke ta mata arin turare. Walida ta kalli Mimi tana kallon Kanta a madubi kafin ta ce" Sun iso ne?. Mimi ta ce" Ban sani ba, bari na kira shi naji. Sai ta auki wayarta ta kira shi amman har kira biyu bai auka ba sai ta kalli Walida tana fa in" Bai auki kirana ba." Sai Walida ta ri e baki kafin ta ce" Kar dai sun iso tun azu yana gidan shi.? Mimi ta kalleta cikin alamun tambaya ta ce" Wani gidan kuma? Walida ta ce" Gidan sa mana, ai wani lokacin in dan ya yi tafiya ya dawo sai an kwana ma an yini muke ganin sa." Sai Mimi ta ji wani abu ya soki ranta kar dai ace da gaske ne, ya wuce gidan nasa ne kuma ta san zai aikata. Kawai sai ta cigaba da kiran lambarsa a kira na biyun da ta yi masa ne ya kashe kiran sai ya biyo bayanta. "Kun iso ne? Tana agawa abin da ta fara cewa kenan cikin wani irin sautin, ganin haka ya sa Walida ta fice domin ta ba su waje su yi mgana. "Eh yanzu mu ka shigo gari." Sai ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce" Shi ne kuma ina kiran ka ba ka auka ba.". Ta fa a kamar ta yi kuka murya kasa asa ya ce" Wayar tana silet ne ban ga kiran ki ba." Sai ya ji ta na sauke numfashi ya auka kuka take yi ya sa da sauri ya ce"Miye kuma? Nace miki banga kiran ki ba ne, kuma shi ne za ki fara min kuka tunda na auri yar gata ko shagwaba biya." Ya fa a kai tsaye amman a hankali. Sai Mimi ta yi masa muryan kamar tana kuka ta ce" To ba kai ne ba." "Ni kuma?. Me na yi? "To ina ta kiran ka baka auka ba." Kai tsaye ya ce" Kash. Na ce na amsa laifina am sorry shike nan ko? Sai ta gya a masa kai kamar y na ganinta kafin ta ji yana fa in" In na isa gida zan kira ki in sha Allahu." Da Sauri ta ce" Wani gidan kuma? Shima kai tsayen ya ce" Gida na mana, ta can zan fara sauka." Kawai sai Mimi ta fara masa jan hanci har ya na jin buga kafarta yarinyar nan so take yi ya zama abun kallo a cikin motar nan. Da Sauri ya ce" Menene kuma yanzu? Mimi na jan hanci ta ce" To na ji kace wai gidan ka zaka fara sauka kana da wani gidan da ya wuce in da ka ijiyeni ne? Ina nan na shirya maka tarba ina ta zaman jiran ka, kuma ka na min mganar wai ta can gidan za ka fara sauka" Ta fa a har ta na kara buga kafarta tana Uhm! uhm! Sai kawai ya ji kamar barci zai kwashe shi saboda yanayin da muryan Mimi ta sakar masa ya sa a kasalan ce ya ce" To ke in ban abun ki, kayana suna can gidan zan je na yi wanka na sauya kaya sai in zo daga baya." Mimi ta ma e kafa a kamar yana ganin ta ta ce" Ni dai A'a." Kai ya girgiza kafin ya ce" Kin cika rigima to yanzu ya kike so ayi? Ya fa a yana kara jan hulan P.Cap in da ke kansa saboda ba ya so a fahimci waya yake yi shi ya sa ya yi kasa da murya sauran Yaran suna baya kujerun gaba daman Coach na su ne da sauran shugabbanin sauran kungiyoyinsu na Gombe da suka tafi da su ne. "Ni dai ka sauka anan don Allah AJI NA." Lumshe ido ya yi kafin ya ce" Mimi ba ni da kaya anan, kuma a gajiye na ke ina bukatar wanka da sauya kaya da zaran na sauka." Da sauri tac e" Nan ma fa akwai Tiolet sannan akwai ruwan zafi." "kayan da zan sauya fa? Kin cika rigima ki bari na sauka ta can, ina yin wanka zan zo gidan in sha Allahu." "Ni dai wlh a'a ban yarda ba." Ta fa a har tana kara buga afa, kansa ya dafe kafin ya ce" To naji sarkin shagwa a, kina katuwa dake kina abun yara." Kai tsaye ta ce" Eh in ai mijina nake yi ma ba wani ba." Bai san ma lokacin da ya yi yar dariya ba kafin ya yi kyafci ya ce" Ki ma yi ma wanin kinsan sauran" Sai ta share mganar da cewa" A nan za ka sauka ko? Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" To na ji in na sauka anan ke za ki bani kayan da zan saka? Cikin murnarta ta ce" Eh wlh, sai ka za a ga su nan kala kala, riga da sikat na Atamfa ko na less ko goguwar rigan material ko abayas wanne kake so.? Bai san yana dariya mai sauti ba sai da ya ga ya juya sun ha a da Coach sannan ya ankare da shagalan da ya yi. Da sauri ya ce'" Mimin kin dai maida ni wani kakan ki ko? Ta na yar dariya ta ce" Ni dai kace min Toh don Allah." Ba shi da mafita dole ya amsa mata sai ta kashe waya tana murna. Ba shi da mafita dole ya ce a sauke shi a bakin hanya tunda sun shigo cikin gari,bai ma bari sun isa Camp ba sanin halin shi daman in aka yi tafiya ba duka ba ne yake bari mota ta isa da shi camp ba, ya fi sauka a saman hanya sai ya hau abun hawa ya arisa. Yana da kaya aramar jakarsa ta baya, sai ledojin da ya yi ysaraba, daman a kaduna suka kwana Sai ya ga ana ta tallar kayan marmari shi daman fa ba ya tsaraba in ya yi tafiya abun da bai ta a yi ba Mimi ta saka shi, itama har tsaraban da ta ce sai ga shi ya zage yana siya mata. Sai daga baya yaji haushin kanshi domin ya tsani aukan kaya in ya yo tafiya jakarsa ma damunsa take yi. Mashin ya hau zuwa anguwan arawa kokacin sha aya saura mintina ka an ya sauka a kofar gidan Wanzamai, kuma ya ci sa'a ba kowa ma a kofar gidan nan ya sallami mai mashin in, shi fa sai yake ganin abun kamar almara tunda ya yi gidansa bai ta a tafiya ya dawo ya sauka ta nan ba sai ya fara sauka a gida ya huta tukunna amman a cikin ranshi da zuciyarsa sun janye sa dole sai ya yi ma Mimi abin da ta ke so, tunda yar gata ce yar shagwa a sai ta fara kuka Inna ta ji labari ya shiga uku. Sanye yake da riga da wando duka baka e, rigar mai gajeren hannu ce sannan daga bayan rigan an rubuta Footboller da farin rubutu wando kuma baki ne mai an matsewa ta kasa sai bakin booth in takalmin dake kafarsa kansa hula ce P.Cap da ta rufe masa rabin fuskarsa. auke da jakarsa a baya da lodojin hannunsa ya shigo gidan dai dai lokacin da Maeesha ta yo ma mijin ta Saddiqu rakiya har tsakar gidan Shigar da ke jikinta ne ya sa kallo aya ya yi musu ya kauda kansa. Ko ma ya san da wanzuwarsu a wajen sallama ka ai ya yi ita da ta zame masa dole. Daf! Daf. Da aran takun takalminsa tare da yanayin tafiyarsa ya wuce Saddiqu daman ba su cika mgana ba, in sun ha u gaba da gaba ne yake gaisheshi amman in har daga nesa ne sai shima ya fauke kansa, har ya shige bangaren Inna Meri daga shi har matarsa suna bin shi da kallo, Sannan ya Juya yana kallonta, itama sai ta kalle shi kafin ta ce" Waye wannan kuma? Kai tsaye ya ce" Agolan gidanmu ne, uban yan girman kai ba." Maeesha ta ta e baki kafin ta ce" Ko wannan an kwallon kafan, mijin matar nan da ta shigo akina jiya? Saddiqu ya ce" Kwarai shi ne, ki ga yadda ya shigo gida kamar gidan uban sa." Maeeasha ba ta yi mgana ba ta dai ta e bakinta kawai. Sanye take da riga da wando kuma sun kama jikinta mayafin da ta yafo arami ne bai rufe komai ba. Daman haka t ke yi, ita a dole yar boko iyakarta ga NCE, amman ji ta ke yi kamar ta yi digiri, tana kuma ganin ita yar masu ku i ne ta kuma taso cikin gata. Ko kunyar Magajiya ba ta ji sai dai itace za ta ji kunyarta a gaban kowa take sanaben ta ita a dole wayayyiya ce. Sai da ta rumgumesa ta yi masa sumba sannan ta sallame shi ya fita ya na wani taku aya bayan aya kamar wani saraki, Sannan Ita kuma ta koma akinta ta zauna ta yi shuru. Tsakani ga Allah Inna Meri da anta sun bambamta da Yayan uwar mijinta acikin gidan komai na su ya fita dabam. An ce daya an Sanda ne yana can Kano da zama ayan da akace Agola ne sannanen an kwallon kafa ne, ga matar shi an ce yar masu ku i ne ma'aikaciyar gidan talabijin ne, ita fa? Yayan mijinta ma magini ne, annensa duka a wahale suke, har gwarama Anty Zuwaira, uwar ta su ma duk aya n ce, ita fa yar gata ce a tunanin za ta zo ta
Chapter 115 · 0% Book details