← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 208

Sashe 74

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

suna fa a mata maganganun da suka yi ta yi, Inna Meri ta jinjina kai kafin ta ce" Da gaskiyar su fa, kar ku ga laifin su ga wanda ya ja min can na kuma gode masa tunda na haifesa." Ran Inna Meri ya gama aci amman ta kasa magana, kuma abun haushin ba wanda ya isa ya yi masa magana ballantana ya ji abunda ya raya a ransa zai yi shi yake aikatawa to ai shike nan amman ya sani hausawa na cewa idan an ciza to a hura Saboda kada watarana ayi nadaman rashin hurawan. Ma su ganin aki suna komawa suka sauke ma Hajiya rashin jin da in ganin muhallin da Mimi za ta zauna Khadi ta nuna mata Video in da ta auka Hajiya ta kar a ta gani kafin ta ce"To ai ni ban ga wani aibu ba aki ya yi kyau sosai Ma sha Allah" Ai sai su ka kasa mgana Hajiya kuma ta yi hakane saboda kashe mganar duk da itama wajen ya yi mata ka an ai ko akin Mimi na gidan nan ya fi akunan girma amman kuma tunda Mimi ta ji ta gani ita ba za ta ja da abunda ta ke so ba, Khadi ta ri a masifa ai ba ta ma auka haka auran Mimin zai zo ba, har ace wai bayan Sadaki shike nan ko lefe ba zai yi ba tsabar ya raina mutane Mommy ma Khadi ta tura mata, ita dai kam ta nuna raahin jin da inta ta kira Hajiya tana korafi Hajiya ta ce ta yi shuru in ta yi magana za ta ba ma su khadi daman kara tsanar auran. Amman ita kanta ta san Mimi ta fi karfin zama a wannan akin itama Mimi khadi ta nuna mata aki ta kallah ta ce ba ta ga aibunsa ba. Cikin Masifa Khadi ta ce" kike tunanin zama anan wajen Mimi? To wallahi ko Abi na da rai ba zai yarda ya kai ki wannan wajen da sunan aure ba" Mimi tace"Zai kaini mana tunda shi ya ce a yi mini abunda nake so" Khadi ta ce"To wannan kayan da ake shirin siya miki asara ne wlh" Mimi ta kada baki ta ce mata" kada ku wahalar da kanku ku siya kalilan in da za su shiga wajen ba shike nan ba." inciki ya cika zuciyar Khadi cikin takaicin Mimi ta ce"Ke yanzu a haka kike son shi? Kama ta ya yi a cikin kayan lefen ki akwai mota ma aciki kin isa kuma kin kai Mimi." Mimi ta kalleta amman ba ta yi magana ba, sun damu da kayan lefe ita fa ta ma siya kayanta ta online sannan Mommy ma ta ce kada ta damu ta yi ma ta wasu acan itama ai ta na ta shan surutu daga danginta sai dai ta toshe kunnuwanta Dr kuwa su Madiha na ta zuga shi ya yi ma Mommy bore ya ce babu ruwan shi abunda Mimi take so a yi mata a wuce wajen sai a zauna lafiya. Khadi har tantama ta fara yi domin kai tsaye ta kalli Mimi kafin ta ce"Anya ma to wannan ba karen yan wallo ba ne? Domin ni banga alamun an balla anan wajen ba, miye cikakken sunansa ai in ya sanu Goggle za ta bayyana min shi." Kamar ba za ta ga ya mata sai kuma ta kalleta kafin tac e" ki duba Gombe United Captain Mansoor Ibrahim Aji za ki ga bayanan sa" Daga haka ta tashi ta bar mata akin,ai kuwa Khadi ta sha mamaki, domin tana saka sunan Aji Goggle ta watso mata hotunansa da matsayinsa a wallo har da an takaittacen tarihinsa. _Mansoor Ibrahim Aji wanda aka fi sani da Ajin jihata Captain ne na ungiyar wallon kafa ta Jihar Gombe wato Gombe United sama da shekaru biyar, Mansoor Aji zakwa urine ne a fagen buga wasa a fili, gombawa suna alfahari da shi ya sanu a duniyar wallon kafa ta jihar gombe da zagayen ta._ Mamaki ya kama Khadi domin ga hotunan Aji nan birjit iya kallonta wasu shi ka ai tare da kambun nasaran da ya sha samu, sauram kuma shi da members in su, wasu shi da Couch na su wasu kuma a sauran Jihohin da su ke zuwa buga wasa a duka Hotunan da Khadi ta gani ba ta ga wani hoto aya da Aji ya yi ko da Mirmishi ba ne akwai wani hotonsa yana tsaye ne a ka yi hoton sanye da kayan United insu. Fuskar nan tana Kyali da ba i saboda cikin rana aka yi Hoton sai a lokacin ta iya ganesa domin abunda ya faru shekarun baya ai tana gidan a lokacin sai dai tun bayan hakane ta manta da komai ta cigaba da harkan gabanta duk da tana bin yan wallo amman na turai irin su man city hala da Sauran su amman ba ta damu da sanin na nageria ba sai dai fitattun irin su Ahmad Musa. Nan da nan ta ara goggle in ku in da Captain in wani Kungiya a wallo zai iya samu albashin da ta gani ya kara ba ta tsoro bayan allowonce da suke samu in suka fita wani gari wasa. Sai ta fara shan jikiinta akan ba in Saurayin Mimi anya ba shi da wani nufi akan hakan? Ta duba tarihin sa kaf yana da Degree ya yi karatu a Gombe State University sannan ku i dai yana da su wulakanci ne kuma komai ya yi da gangan ne. Tunaninta sai ya karkata Allah yasa ba aukan Fansa zai yi a kansu ba. Nan da nan duk ta yi sreenshoot in abubuwwn da ta gani game da shi ta hau Chart ta turama Madiha tana kuma online sai ta ce ta duba. A kasa ta Rubuta mata" Gayen da Mimi za ta aura ne, duba ki gani." Sai da Madiha ta gama ganin komai sannan ta doka ma khadi video call ta auka suna kallon Juna. Madiha ta ce" Na duba komai, in dai haka ne to me hakan ke nufi? Me ya sa ya yi hakan? Khadi ta ce"To Allah yasa ba abunda Abi ya yi masa ya ke so ya rama akan Mimi ba na fara tsorata da mutumin nan daga ganinsa ba shi da kirki." Madiha ta ce"Gaskiya idanuwansa ma na tsageru ne daga gani." Khadi ta ce"Ko a baya da kowa ke tsoron ha a ido da Abi shi bai yi ba, akwai taurin zuciya da tsaurin ido." Sun ci gaba da tattaunawa Khadi na kara mata bayanin ta yi fa Goggle in har albashin su gayen na da arzikinsa sai dai ya shirya mugunta ne, Madiha ta ce"Kyaleta ai ita ta ji ta gani Allah ya ba da sa'a." Kamar yadda Khadi ta binciko waye Aji haka Alhaji Hamza ya saka aka yi masa binciken tun daga tushe saboda Mama ta zo itama da na ta korafin bai dace a kai Mimi wannan muhallin ba, ta kuma nuna masa wajen ya gani, Mimi da ta so a babban gida itace a bedroom guda aya kamar wata yar aiki, Sai ya yi amfani da mganar Mama da ta ce ko yaron ba shi da Sana'a ne yasa a ka masa binciken sama da kasa akan Mansoor Ibarahim Aji. Har ta da anin mahaifinsa Alhaji Yakubu da ke zaune Bauchi ya samu labarin shi, da kuma aukakan Aji a jihar Gombe, shi ya samu labarin ya na da gida da mota sannan ya na kan samun Ku i a harkan wallon kafa sannan Jarumi ne zarafinsa na haskawa a kungiyar da suka auke sa na gombe united shima an kawo masa hotunansa ya gani yaron bai sauya masa ba sai dai ya kara girma da cika ido, shi ma ya yi ta mamakin menene mission insa na auran Mimi a haka ahalin yana da arzikin da zai iya yin auran ban mamaki? Shi kan shi sai ya fara Tltnanin Allah yasa ba ramuwa yaron yake so ya yi ba. Mimi kuma ba ta damu ba harkan gabanta kawai ta ke yi, ta kuma ce a yi mata komai saffa saffa shi ya sa aka siya mata saitin kujeru kananu mai uku sai tibi da tibi Stand sai cafet kawai a falo da Disppanser bedroom kuma aramin gado aka yi sai wardrope kananun kofa uku sai shuraf wajen ma'adanan takalma shima sai cafet kawai, kayan Kitchen kuma sai aka siya masu muhimmanci irin su Friza aka siya mata arami saboda kitchen sai gas mai hu arami saboda kada wajen ya matse komai Mimi ita ta za a abun ta ba ta son tarkace ta ce ta bakin Khadi ta ce kada ma a kashe kudi a siya abu domin ba wajen zaman su a gidan nan. Ta koma Kaduna sai ana biki saura kwana biyu ta ce za ta dawo. Gyaran Amare kuma Hajiya ta saka Yaddiko a kan gaba sannan Inna Zainabu ta zo daga kano nan ta sauka gidan Hajiya tun ana saura kwana goma biki ita ke kula da bangaren gyaran jikin amarya ta zo ma da Mimi da kayan gyara daga Bojuwa na surayya Dee, kayan ta masu inganci ne da abi'a suna kuma da ewa a jikin mace ba su daina aiki ba, ita ta ha o ma Mimi kayan gyara har da na sanyi bayan su dahuwar amare na kaza +234 803 277 3332 Daga sokoto kuma wata awarta Suwaiba za ta zo ta yi ma Mimi Halawan Amare. Rukky kuma itace babbar awa amman ba wani shiri a hannunsu sun dai fitar da Ashoben biki, abunda ya ba ma Rukky haushi kamar Mimi ace za ta yi aure amman ko walima ba za a yi ba kamar wata bazawara, Sannan arin mamakinta duk wani shiri Mimi da an uwanta ne ba Aji aciki akwati guda Mimi ta ha a ma kanta bayan wanda Mommy ta ha a mata za ta taho da shi, Dr. Kuma duk shi ya yi mata kayan aki tun da ya hana Daddy yin komai ya ce shi zai yi shi kuma Daddy sai ya ce zai yi mata kayan gara. Allah sarki Jaheed 100k ya tura ma Mimi ya ce ba yawa Allah ya sanya alheri sai taji tausayinsa. Ko a
Chapter 74 · 0% Book details