← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 208

Sashe 38

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

karin guga Kallo aya zaka yi ma Aji za ka shaida da gaske ne shi in Aji ne da kansa ba sa o ba, kuma Ajin na shi ya kama kasa ba, hankalinsa na kan wayarsa ne arama mai tocila ya na faman latsawa, yi yake yi kamar hankalinsa na kan abin da yake yi ne amman kuma ba akan wayar yake ba, yana can gefe in da yake hango yar matashiyar yarinyar nan da Inna Meri ta ce jikar gidan ce. Ta kofar falon da zai sadaka da falon gidan yake ganinta tana lekowa ta na kallonsa sai ta koma in ta ga kamar zai ago, ba yau ta fara haka ba tun daa ya fara shiga haraban gidan ya jira fitowar Inna Meri tana yawan le osa amman ba ta ta a fitowa ba. Shima sai ya yi kamar bai ganta ba, alhalin duk lokacin da za ta yi wannan leken shima sai ya tattara hankalinsa a kanta. Yau in ma nunawa ya yi kamar hankalinsa na kan latsa wayarsa sai da ya ji megadi na fa "Bintar Hajiya ki fito mana, kina leke tun azu." Ba ta da yadda za ta yi tunda an ganta kuma har an kira sunanta, sai ta fito tana nokewa tana sanye da doguwar riga na abaya ta yafa mayafin rigar a saman kanta sai faman mirmishi take yi lokaci aya kumatunta na lo awa. Ta wutsiyar ido yake kallonta a ransa ya ce yarinyar nan akwai arhar fara'a da dariya, Ko ba'a yi mata mgana ba ita ka ai ma sai ka ga tana mirmishi. Yana jin ta tsaye a kansa tunda ta ariso shi kuma daman Megadi ya shige aramin akinsa ya barsu, shi kuma sai ya yi kamar bai san da wanzuwar mutum ma a wajen ba. Kamar daga sama ya ji maganarta cikin za in muryanta da ya shaida ta tun a karon farko. "Ya sunan ka? agowa ya yi yana kallonta kamar yadda shima ta ke kallonsa hannayenta na bayanta tana juya jikinta yamma da kudu, lokaci aya kuma ta na jifansa da mirmishinta da har gobe suke da tasiri a rayuwarsa. "Ni? to ke ya sunan ki? Cikin kara inta ta ce"Ni sunana Mimin Mimin Abi" "Ni kuma Sunana Mansoor Aji.." "Aji..? Ta fa a da sigan tambaya har ta na saka a yatsa a gefen bakinta, irin sunan ya ba ta mamaki sai da ta saka shi ya yi murmishi ta na da surutu da kara in magana kafin ma ya kara magana ta yi zaraf ta kara cewa. "Wajen wa ka zo? wajen Hajiya? Sai da ya girgiza mata kai kafin yace" A'a ni wajen Innata na zo." Cikin mamaki ta kallesa har da waro ido kafin ta ri e ha a ta ce" Inna Meri mai girkin Hajiya.? Sai ya gya a mata kai, kamar wata babba sai ta kama baki tana dariya kafin ta ce"Laa wai daman itace maman ka? Kallonta kawai ya ke yi ba tare da ya yi mgana ba a ransa ya na fa in yarinyar nan akwai bakin surutu. i ba'a tambayeka ba kenan shi fa bai tsareta da tambayoyi ba, amman har ta fara fesa masa ita Abuja take suna da Mommy kuma Abi in su soja ne. Sannan ta gama Jss3 yanzu za ta shiga Ss1 ne, labarai kala kala haka ta na tsaye take gaya masa shi dai ya yi kasa e kawai ya na jin ta kuma yana kallon bakinta. "Kai ina ne gidan ku? Kansa ya nuna kafin ya ce"Ni? Sai ta gya a masa kai, cikin gajiya da maganar ta ya ce"Gidanmu ya na can da nisa" Ya fa a lokaci aya yana mikewa sai kawai ta ce"To ina ne ina so na sani ne" Cikin osawa ya ce"Ke can da nisa ne ba ki san hanyar ba." Sai ta rage fara'a sai da ya kalleta sai ya ji bai ji da i ba sai ya samu kansa da fa in" Ba ki san gidan ba yana da nisa daganan" Sai ta yi zaraf ta ce"Za ka kai ni wata rana na ga gidan ku? Saboda ta kyalesa ya saka ya gya a mata Kai kafin ya ce"How old are u Mimi? Cikin za in muryanta ta ce"I am 16 years old." Jinjina kai ya yi aransa ya na fa in ba Shakka domin ya ga aikin yarinta. Shima kawai sai ta sauya harshe tana tambayansa "How old are u? Mamakinta ya kama shi har nuna kansa ya yi ta gya a kanta sai lamarinta ya bashi dariya har sai da ya murmusa kafin ya ce"I am 20 years old." Sai ta washe baki kafin ta ce"Ka girme ni ashe." mamakinta yake yi jin turanci mai kyau a bakinta, bai auka haka Mimi take ba sai da ta dame shi da tambayoyi, har sai da ya gaji ya kalleta yana fa in " Kin cika tambaya Mimi, kamata ya yi in kika girma ki karanta aikin jarida." Bai cika sakewa da wanda bai sani ba sai gashi ya biyema yarinya tana tambayarsa yana amsa mata. A haka har Baba Megadi ya fito ya gansu har sai da ya yi dariya kafin ya ce"Ka ha u da gidan jarida da kanta, Bintar Hajiya akwai tamboyoyi ita komai so take sai ta sani." A ran Mansoor ya ce y gga alama amman bai yi mgana ba. A bakinta ya ke jin izifinta goma sha Bbyar cikin mamaki ya kalleta kafin ya ce"ki na zuwa islamiya ne? Sai ta washe baki kafin ta ce"Uncle inmu ke zuwa gida ya na koya mana, sannan Mommy tana yi mana karatu da safe kafin mu tafi school." Jinjina kai ya yi, shi ya auka yadda take yar gata nan karatun addinin ba zai dameta ba, har fa sunan makarantar bokon da ta yi sai da ta gaya masa da sunan Yayyenta gidansu ya ji dai sunan khadija(Khadi) a bakinta har ya gaji, da labarin Abi ya siya mata kaza ya siya mata kaza kallonta kawai yake yi yana so ya ji ko a cikin asan ran shi ta dame shi amman cikin ikon Allah bai ji ya gundira da jin maganar ta ba. Har fa turkeshi ta yi wai shi ya sunan makarantar su? Ya fa a mata bai yi ma ta ba har sai ya gayamata ya iya karatun Qur'ani? Sai da tambayar ta saka shi dariya dai dai Lokacin da Inna Meri ta fito cikin shirin tafiya ganin Binta tare da Baban Inna ya sa ta ce" Binta Kina nan ashe? Hajiya na can tana cigiyarki." Tana ganinta da sauri ta nufeta ta riketa tana fa in"Inna Meri wai wannan anki ne? Ta fa a ta na nuna shi sai da tambayan ya saka Inna Meri dariya. Rike mata hannu ta yi kafin ta ce"Eh mana kuma bashi ka ai ba ne ina da wasu an a gida.". Da sauri ta ce"To ina za ki je yanzu? Ta ce gida zani Binta, kai tsaye ta ce"To nima zan bi ki ina so na je na ga gidanku ne" Ta fa a tana kallon Aji da ya yi gim da rai kamar ba yanzu ya gama dariya ba. Inna Meri ranar ta ga ta kanta, dakyar ta lallashi Mimi ta hakura amman sai da ta ce gobe za ta tafi da ita in dan ta zo, sannan ta yarda Inna Meri ta rakata har bakin kofar falom Hajiya sannan ta juya shi ko Mansoor har ya yi gaba a ranshi yana cewa yarinya nan akwai sai surutu da rigiman tsiya. A hanya ya ce ma Inna yarinyar akwai surutu Inna Meri ta yi mirmishi kafin ta ce " In da surutun ta yake burgeni ta bakin Hajiya akwai mgana mai amfani a bakin Binta duk abin da ka ji ta yi tambaya akansa mai amfani ne. Sai shima ya yarda da maganar Inna Meri ta na tambaya ne a kan gaskiyan duk abin da ba ta sani ba, kuma take son sani har suka isa gida Inna Meri sai labarin jikar Hajiya ta ke bashi. Abun da ya bashi mamaki Inna na gaya masa Hajiya na son a bar mata jikarta amman tana tsoron ta yi magana uban yarinyar ba zai bata ba. Cikin mamaki ya ce" Saboda mene Inna? Ba ita ta haife shi ba? Inna Meri tace"Kai ma dai kayi maagana, shine babba ma amman kuma kamar ba shi da sau i ko ka an na ta a ganinsa sau aya fusakarsa ba fara'a sannan ya yi ta magana a sama sama ina gidan ya zo Ina cikin madafi ina jin Hajiya na yi masa fa an kan dai wani abu amman harshensa a saman nata kuma naji ma da kunnena yana mata rantsuwan bazai yi abin da ta saka shi ba." Cikin Al'ajabi Mansoor ya girgiza kai bai sami zarafin mgana ba tun kafin ya gansa kawai yaji ya tsane shi me ya sa yana babba kamar sa bai san darajan mahaifiyarsa ba? Inna Meri sai gaya masa take yi Hajiyar da kanta ta ke mata orafin a cikin ya'yanta yafi ba ta matsala. Shi dai yana jinta amman bai yi magana ba sai dai acikin ransa sai da ya ce kuma ga shi Allah ya basa mai kyau da kaifin basira. Tun Mimi na matashiyar yarinya kyanta ya ke a bayyane. Bai taba tunanin in ta kara ganinsa za ta kama sunan shi ba sai da washegari ma ya koma gidan yana tsaye a haraban gidan ya ji ta wala masa kira. "Aji.." Abun ya aure mishi kai, ta kiran sunan shi cikin muryanta mai za i fiye da yadda sauran abokansa ke kiransa. Shima sai ya samu kansa da amsa mata har kuma itama ya kira sunanta. "Na'am Mimin Abi ko? Ta na yar dariya ta ariso gabansa kafin ta ce"A'a MIMIN AJI dai? Ido ya sakar mata ta na dariya Kumatunta na lo awa take fa in "Sunanka ya yi min da i ka bar min Please.". Ta fa a cikin yar shagwa har tana buga afafunta a kasa, a lokacin sai yaji kamar wani abu ya daki zuciyarsa da ya saka sai da ya saka hannunaa ya dafe jikin get in gidan da yake tsaye har bai san bakinsa ya
Chapter 38 · 0% Book details