Sashe 7
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shine gaba aya Ahalin Sulaiman Dabo suna iban kamanni da juna. Hajiya ta na ganin Rukkaya ta washe baki ta na fa in "A'a mai sunan yan gayu ne yau a gidan? Rukkaya kanta na kasa ta amsa lokaci aya kuma ta durkushe kasa ta na gaida Hajiya. Sai ta amsa mata itama ta na zama kan aya daga cikin kujerun falon tana ce ma Rukkaya ta tashi ta koma saman kujera ta zauna. Ba ta yi musu ba ta ta shi ta zauna lokacin kuma Baaba Uwani ta kawo mata ruwa da lemu a wani aramin faranti da aramin Kofin silba. Bayan gaisuwa da tambayan gida da aiki Hajiya ta kalli Rukkaya kafin ta ce"Ita Bintan tunda ta shige bata fito ba? Hala kun biya wani wajen ne kafin ku kariso nan ko? Kan Rukkaya na kasa tace"E. mun biya gidan wata Yaddiko." Nan da nan fuskar Hajiya ta sauya lokaci aya tana fa in "Me ya sa Yaddiko ba ta jin magana ne? Ta yi kuma orafin Binta ba ta zuwa gudanta, kuma in ta je bakinta baya iya shuru sai ta ja abin da kafin Binta ta koma gidanta sai an yi ta fama kai jama'a." Hajiya ta fa a ta na mai lokarin bayyana takaicinta kafin ta ce"Allah ya sauwake to." Rukayya ta tashi taje gaban Hajiya ta mika mata zogalen da Mimi ta barta da auka lokaci aya da jakar Mimi da key in motarta tana fa "Hajiya ga sakon zogale Yaddiko ta ce a kawo miki. Wannan kuma jakar Mimi ce da key din motar ta" Hajiya tace Rukayyan ta ijiye a kan Kujera, sai ta ijiye mata sannan ta tashi ta koma wajen zamanta ba ta jin kishi amma kada Hajiya tayi mganan bata sha komai ba ya sa ta zuba ruwa ta sha ka Falon ya yi shuru kowannensu da tunanin da ke cin ransa. Rukayya ce ta kauda shuru bayan ta kalli Hajiya ta ce"Hajiya Mimi kamar kuka take yi acikin akinta fa? Hajiya ta sauke numfashi kafin ta ce"Shi zata yini yi yau tunda aka famo mata wannan tsohon ciwon, yau kuma kamar gidan makoki haka zai kwana." Rukky ta gyara zama kafin ta ce"Hajiya shin wane ne naji yaddiko na mata maganar shi? Domin bayan an yi mganar ne Mimi ta shiga cikin tashin hankali tun muna hanya ta fara Koke koke." Hajiya ta yi shuru na wani lokaci kafin ta ce"Wani shu en labari ne Rukayya, shekarun sun da e amma In Binta ta tuna kamar yau abun ya faru haka take ji." Sai kuma ta yi shuru Rukayya kuma ta kosa taji ko waye wannan da tunashi ka ai kan iya haifar da tashin hankali a rayuwar Mimi Cikin aguwa Rukayya ta ce"Hajiya to wane ne wannan mutumin da tuna shi ka ai barazana ne ga kwanciyar hankalin Mimi? Hajiya ta yi wani iri kafin ta kalli Rukayya ta ce"Wani ne, wani saurayin Binta ne da suka yi soyayya da jimawa." Rukky ta ware ido kafin ta ce"To yanzu ya na ina? sun rabu ne ko ya rasu ne? Hajiya ta girgiza kai kafin ta ce"An ya? Bai rasu ba ya na nan da ransa. Irin soyayyar nan ce tun na tashen balaga Rukayya ya so Binta itama Binta ta so shi kamar ta mutu, amma faruwan wasu abubuwan ya sa suka rabu tun shekaru sama da takwas ina jin." Rukayya ta yi jugum kafin ta ce"Me ya hana su aure tun a wanchan pokacin Hajiya? Kuma anan garin ne ko acan Abuja? Hajiya ta ce"Mahaifinta ya hana al'amarin, A nan garin ne anan kuma suka ha lokacin tana zuwa min hutu," Rukayya cikin arin mamaki ta ce"Kuma tun bayan rabuwarsu yana nan a nan garin nan? Hajiya ta yi shuru kafin ta ce"Gaskiya ba na jin ya bar garin nan, tun da tun bayan faruwan lamarin zumunci mu ya yanke tsakanina da mahaifiyarsa ba ni da labarinsu, ba ta zuwa in da nake nima kunya da nauyi sun kasa barina har yau na nemeta. Allah Sarki Inna Meri wata mace kwara aaya da na zauna da ita mai kirki da mutumci mai kawaici da ya ana mai hakuri da sanin darajan an adam ta zauna dani kamar ni na haifeta daga baya abubuwan da suka faru ba ma su da i ba ne shi ya sa sai alaqan da ta ha amu tun a wanchan lokaci ta jima da lalacewa daga kuma Lokaci ban kara jin labarinsu ba amma ina da tabbacin suna nan a garin nan Rukayya ta yi tagumi tana jin Hajiya kafin ta ce"To Hajiya me ya sa Abban Mimi ya hana su aure tun da Mimi tana son shi? Hajiya ta ce"Ai shima ya sota, ya so ta sosai so mai tsanani wallahi. sai dai kinsan komai sai Allah ya yi, alokacin duka an yi abun ne cikin rashin lura da gaba, shi ya sa ake son in mutum ya ciza to ya busa saboda gaba kar ya zo yana nadamar abin da ya aikata, labarin ba shi da da in fa a mai sunan yan gayu ki bar maganar kawai, gwara ki tashi ki karisa gida yau sai sa'a Binta zata fito daga cikin akinta" Ba haka Rukayya ta so ba, ta so ne taji mafarin labarin, ba za ta iya gaddama da Hajiya ba ya sa ta mike ta yi mata sallama ta fita. Sai da ta taka da kafarta har can babban titi sannan ta samu adaidaita zuwa gida. Kuma ita duk tunanin ya tafi akan me ya hana wannan auran? Sannan taji Hajiya na fa in alaqar dake tsakaninsu ta lalace tun daga wancan lokacin, a kuma yadda ta fahimta Hajiyar kanta bata ji da in abin da ya faru a wanchan lokacin ba sannan kuma duk yadda akayi Mimi na son wannan mutumin kuma shi ne dalilinta na har yau ba ta yarda ta ba ma wani namiji dama ba, duk ko da tarin masoyanta. Za ta so ta ji oabarin wannan Soyayyar domin kuwa tana da tabbacin akwai abun al'ajabi acikinsa. Za ta yi ta bin Mimi a sannu sannu har sai ta san komai, arin abun mamaki yadda Mimi tace bai yi aure ba shima a gidan Yaddiko. Kenan tana labarinsa? ta kuma kila san a in da yake rayuwa? Ammh me ya sa bata neme shi ba, tunda dai saboda soyayyarsa ta ki ba ma kowa dama ya kamata ta nemeshi saboda ta ba ma zuciyarta abin da take so. Har ta isa gida jukinta a sanyaye yake, sai taji Mimi ta ba ta tausayi soyayya ai kamar guba ce, ita kanta da suka rabu da saurayinta faisal ta sha wahala kafin ta farfa o balle na Mimi da aka ce sama da shekaru takwas da suka gabata ***** *7:30Pm* Tun da ta shiga akinta bata fito ba, duk ko da magiyan da Baaba Uwani da Hajiyar da kanta suka zo suna yi mata akan ta fito ta samu wani abu ta saka ma cikinta. Sai ta yi kamar ba ta ji su ba har suka gaji suka kyaleta. Mimi ta yi kuka kukan da sai ta auki lokaci ba ta yi irin shi ba, ammh duk lokacin da tunaninshi ya bijiro cikin duniyarta haka yake maida ta. Har zuwa yaushe ne zuciyarta za ta daina tunanin sa da begen sa? Sai yaushe ne za ta iya cire sa a cikin zuciyar ta? yaushe ne za ta sauya rayuwarta ta daina zaman jiran warrabuka?. Jiran da ta san har gaban abada na cire tsammani ne? Ita tasan ba zai dawo gareta ba ya tafi kenan kamar yadda ya fa a da gaske yake sun yi rabuwan Abadan Abadan ne tsakaninta da shi. Shekaru goma kenan ammh soyayyarsa acikin zuciyarta tana jin ta kamar sabuwa. Babu abinda bata yi ba saboda ta manta da shi amma ta kasa, babu kalan addu'an da ba ta yi a gaban ka'aba saboda Allah ya cire mata soyayyarsa a cikin zuciyarta ba amma lamarin kamar yana kara nisa ne, ba ta jin ko igon soyayyarsa ta ragu daga zuciyarta sai ma take ji kamar duk arin minti aaya na bugawar numfashinta kara son shi take yi. Ta fara son shi tun bata son menene so ba, ba zata a manta garkon ganinta da shi ba, tana da shekara goma sha shidda a lokacin hatta date in ya kasa ace mata a cikin tunaninta. 20 December 2008. A cikin hutun third tearm da makaranta kan ba su mai tsawo Hajiya ta kira Abi a waya ta ce maza maza ya saka akawo mata Bintu tayi hutu a wajenta, alokacin Abi bai so ba saboda baya so Mimi na yin nesa da shi amma Hajiya ce tanna kaunar Mimi bai isa ya ce mata a'a ba. Ba za ta ta a mantawa cewa tafiyar Jirgi Abi ya so tayi zuwa Gombe ita kuma ta ce tafi son na mota saboda ta rika ganin gari, direban su Mallam Sale Allah ya jikansa ya rasu a hatsarin da suka samu da Abi shi ya tuko ta tun daga Abuja har gombe. Ba kuma ta yi barcin hanya ba ta yi ta kalle kalle duk abin da ta gani sai tayi tambaya shi kuma Mallam Sale na bata amsa a wannan tafiyar ta haddace sunayen garuruwa da dama kuma tafiyar na aya daga cikin tafiye tafiyen da ba za ta ta a mantawa da su ba. Da yammah suka shigo garin ta san tana manne jikin window mota tana kalle kalle har age mata glass din mallam Sale ya yi da suka shigo cikin gari. A kofar gidan Hajiya daga nesa ka an ta fara ganinshi. Sanye cikin riga da wando baki da fari, rigar mai dogon hannu tana da layi layin baki a jikinta ya sanya duka hannayensa cikin aljihun wandonsa. Kansa na asa yana danna karamar wayar dake hannunsa. Lokacin da Mallam Sale ya yi hon shi kuma sai hankalinsa ya kawo wajen dai dai lokacin da ya ago yana kallon motar ita kuma tana kallonshi a a dai dai lokacin suka ha a ido. A lokacin ba za ta ta a mantawa ba, ta yi masa mirmishi har kumatunta suka lo sannan ta aga masa hannu. Shi bai aga mata ba,