← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 208

Sashe 96

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

can kuma ta kara fa in" Ba ka isa ka hana ta zuwa aikinta ba na fa a maka. Saboda haka in ka shiga ka sanar da ita ta shirya gobe ta koma wajen aikin ta" Da Slsauri ya kalli Inna kafin ya ce" Inna ni fa ba doka ta ba ce, dokar ubangiji ce ya za a yi ace macen aure tanna zuwa duniya tana bayyana adon ta, In wani ya ganta ta burgeshi har ni ba zan tsira ba Inna" Inna ta masa dakuwa kafin ta ce" Ai sai ka fa a min aure tunda ni tun shekaru aruru ba aure nake yi ba zaman kaina na ke yi ko? Sai ya yi asa da kansa kafin ya ce" Ba haka nake nufi ba Inna, kawai.." "Kawai me? Cigaba da mganar ka ishasshe." Sai kawai ya ka a kai kafin ya ce" Shike nan kawai, ki yi hakuri Inna." Ya fa a ya na huro iskar bakin shi, ita kuma ganin ya sauko ya sa ta gyara zama ta fara masa nasihan yafiya da kuma Illar ri o, Shi dai ya na jinta ne ta gama maganarta ya ce ya ji zai gyara ita kuma Inna Meri fa i take yi" Ka maida komai ba komai ba miye aciki? daman can Allah yasa abincin ka na wajen wallon nan, abunda Ubangiji ya tsara ma bawa fa bai isa ya kauce masa ba, domin Allah ka yi hakuri ka hutar da zuciyar ka Baban Inna, ka rike qmanar yarinyar nan kar ka ka watsamin asa a ido don Allah" Da toh kawai ya amsa mata ta rufe mganar ta da cewa" kayi hakuri ka barta ta cigaba da aikinta, in kana da wani tsari ne da irin shigar da za ta rika yi sai ka yi mata mgana amman domin Allah na ro e ka ka barta ta yi aikinta." Ba shi da mafita dole ya amsa da ma Inna da to. Har ta sallame shi jikin sa a sanyaye yake, suna tsaka da hira da Walida suka ji sallaman shi, Walida ta mike tana gaishe ya amsa sau aya ya kauda kai, sai ta fice ta na ce musu sai da safe. A kujeran da ya saba zama ya zauna ita kuma Mimi ta mi e tana yi masa sannu da zuwa ya amsa da Idanuwansa da suka sauya Launi. Ta juya za ta koma ciki sai da y jji miyau ya wuce ta bakin shi bai sani ba mukut, Plazo in dazu da ta saka ne a jikinta kuma yana bayyana sura kugunta ya bayyana a cikin wando, duk yadda ya so ya kauda kansa ya kasa sai da ta shige ciki ta maido kofa sannan ya sauke ajiyar zuciya. Yanzu tsakani ga Allah a haka ne zai barta ta na zuwa wajen aiki? Wata zuciyar ta ce masa" Ka manta ko ada ta na aikin ta? Sai a lokacin ya ji wani irin bakinciki ya ara rufe shi, allah ka ai yaasn yadda ya rayu a iya lokacin da ya fara ganin Mimi tana aiki a gidan talabiji, wa zai iya bu e ma zuciyarsa domin ya ga irin wahalan da ya sha akan Mimi? Ko ya zauna yana mgana da bayani ba wanda zai yarda amman Allah ke da kwanan duniya Allah ka ai ya san irin balla'in ya ke shiga kan aikinta a gidan talabijin in nan. Kishin da yake da shi a kanta Ubangiji ne kawai ya yi masa iyaka, shi kan shi wani lokacin ya na tsoran bakar zuciyarsa akan ta bai san me zai iya aikata nan gaba a kanta ba. Tsabar acin rai ma yana jin yunwa amman haka ya kwana da yunwar nan, ya tuna da zai baro akin Inna har tambayan shi ta yi me ya ke komawa gida yi da sassafe bayan ya kwana anan? Sai ya rasa abun cewa kawai sai ya ce shiryawa yake komawa tunda ba shi da kaya anan. Kai tsaye Inna ta ce" To kai ma da wahala kale, ka kwaso kayan naka mana, tunda daman hoto kake so gidan naka ya zauna ai sai Aljanu su samu mazaunin zama." Har ya je sallar asuba ya dawo fuskar nan ta shi kamar hadari, da ya shiga gaida Inna sai da ta kara tuna masa lalle Binta ta shirya ta tafi wajen aikinta a da une yace Toh Inna. Sanda ya koma akin tana kitchen domin ya ji uruntu kuma yaji kamshin kwai kamar ta na soyawa, sai ya yi kwanciyar saman kujera yana tunanin irin matakan tsaron da dokokin da zai saka ma Mimi akan aikin nan, tunda taci nasara Inna ta shiga tsakani to shi ba wawa ba ne dole ne ya san abin da ake ciki. Rufe ido ya yi kamar mai barci, yana jin ta tana zirga zirga tsakanin falo da Kitchen, ina zai bu e ido ya ga abunda zai fallasa sirrin zuciyarsa, ita kuma ta auka barci yake yi, kuma tunda ta ga zuwan shi jiya tasan Inna ta yi masa mgana kawai sai ta fara shirinta, ita kwastan ta sha sai ta soya kwai ta ci da buredin da jiya ta ba ma Walida kudi ta siya mata, ganin shi a falon nata har lokacin bai tafi ba kamar yadda ya saba sai ta dafa mai ruwan tea ta gasamai buredi ta ha amai saman wani kayattacen farantin yan gayu, ta zo da kanta ta ijiye saman center table in da ke tsakiyar falon sannan ta shiga ciki ta yi wanka ta shirya. Shi kuma haushi ya ke ji ya sa ko kallon farantin da ta ijiye bai yi ba sai faman juye juye yake yi, ya rasa mafita guda aya. Yana kwance sai ga ta fito kamshin turaren da take yi ne ya fara masa sallama baisan lokacin da ya bu e ido aya yana kallonta ba, yarinyar nan kamar ta yi hauka yake tunani,mSanye take da leshi fitted gown ne shi a ganin shi a idon shi rigar nan ta matseta sosai. Sannan ga wani shigen mayafi mai raga raga shi da babu duk aya kafarta cikkn takalmi mai tubu milk kalan mayafinta da jakarta. Wuyanta da hannayenta suna walwali an kunnen gold kamar wacce za ta je wani gasan kyau, shi dai yana kwance yana kallonta da ido aya sai ya ga kamar ta yi hanyar fita bai san lokacin da ya mi e ba sai ganin shi ya yi a zaune yana fa in" ke FATIMA ina za ki je a haka? Shi ne ka ai ta san ya na kiran ta da suna Fatima, Sai da ma ta juyo ya ga kamar har da jan baki ta saka a saman le enta nan da nan yaji duniyar ta yi masa wani irin duhu. Ita kuma mamakin sa take yi, daman ba barci yake yi ba.? "Na ce ina za ki je a haka? Kai tsaye ta ce" Ina kwana." Ya fara jin haushin sa na aruwa a fusace ya ce'" Ki amsamin tambaya ta, na ce ina za ki je a haka? Kai Tsaye ta ce" Yanzu dai zan je na gaishe da Inna ne na dawo." Kai ya jinjina kafin ya ce" Je ki gaishetan ki dawo ina jiran ki." Sai kalamansa suka ba ta mamaki amman ba ta nuna ba. Sai ta saka kai ta fita zuwa akin Inna ta shiga ta duka har kasa ta gaisheta Inna ta amsa cikin sakewa tana fa in" Anyi haraman tafiya ne? to Allah ya ba da sa'a" Mimi ta amsa da amin amin na gode Inna, ta mi e tana fa in" Ina Walida? Inna ta ce" Tana ciki tana barci, ina ma ta kiranta ta tashi ta sama miki abunda za ki ci ba ta ga dama ta tashin ba." Mimi ta ce" Na karya ma Inna kyaleta ta sha barcinta sai na dawo." Inna ta rakata da Allah ya tsare amman ita kanta a ranta ta na mamakin ko ina Baban Inna? Ta san da wahala ya bar Binta ta fita da wannen siririn mayafin. Sai dai ta yi shuru ba ta yi mgana ba. Har ta fice ta na kallonta sai da ta murmusa a fili domin kaf a zagaye zagayen Baban Inna Kishin Binta ke murkukusan bai gane ba, ya ki bar ma zuciyarsa salaman da za ta zauna da abunda take so ya na can ya na fama da rikon abunda ya wuce tuntuni. Ita tana ji acikin ranta auren su na har Abada ne ba mai karewa ba ne, kuma yau da gibe zai saka in suna tare ya manta da baya ya kuma rumgumi matarsa domin ta na da tabbacin duk duniya ita ka ai ya fara so kuma ita ce karshe. Mansoor na inda Mimi ta barshi nan ta zo ta iske shi, amman wannan karon zaman sarakai ya yi harda ora kafa aya kan aya , tana shigowa bai neme ta da mgana ba sai ita ce ta koma ciki ta auki wayarta ta saka a jaka sannan ta fito ta tsaya a bayan kujeran da ke facing in sa ta ce" Ni zan tafi, zan biya ta gidan Hajiya na auki Mota." Karfin halinta yake gani ita yanzu a zamanin gaba gaba suke da za ta fita a haka? Bakinsa ya matse kafin ya ce'" Ina Hijabin naki? Cikin mamaki ta ce" Hijabi kuma? Domin ita ba ma'abociya saka hijabi ba ce, sai dai in za ta yi sallah, duka duka Hijaban ta ma uku ne a duniya sai dai kowani kaya da kalan mayafin sa. Shiyasa ta yi mamaki da tambayar sa, shi kuma sai yacga in ya tsaya mata mgana za ta ata masa lokaci ya sa kawai ya mi e yana fa in" Ba auran cuci na yi dake ba, ballantana ki fita da wannan abun mai raga raga kamar yallen tata da sunan mayafi zuwa wajen aiki ba, ke wallahi sai ma kin sauya duka dressing in ki, bazan ta a lamunta ki fita daga gidan da wannan shigar mai kama da tsirara ba." Ya fa a kai tsaye yana nuna ta da yatsa, Mimi mamaki ya hana ta mgana sai kawai ta bi shigar ta da kallo domin ita ba ta ga aibun shigar ta ta
Chapter 96 · 0% Book details