Sashe 22
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
za su ha u a gida in ya dawo. Mu'azzam sai da ya yi barci ya koshi sannan ya tashi ya yi wanka ya sauya kaya ya auki motarsa ya bar gidan bayan ya kulle gidan tunda ya ga key din gidan anan cikin bedroom din. A wajen Inna Meri ya je ya karya da waina da Miya Inna Meri da kokari da Safen nan ta toya ta miyar kuma Walida ta yi shi kafin ta ta fi makaranta Mansoor bai zo gidan ba sai da rana sai kuma a lokacin shima ya karya da waina da miya, daga nan Mu'azzam ya je tudun wada ya ga kwanan Hibba daga nan ya taho ma da Mansoor Junior. Tunda kuma ya auke shi suka fita a mashin sai yamma ya dawo da shi akwai wani team ne da suka gayyace shi kallon wasan su, Bacerlona sunan Team in anguwan Jekadafari ne, can ya je kallon buga wasan su tsakaninsu da Mesi team na anguwan Tudun wada. A hanya ya ga ana saida kayan wasan yara ya siyan masa jaka guda ya kawo sa wajen Inna Meri, yana ma gidan Mu'azzam ya kira shi ya ce suna tare da Nasir ya ce yana gida su zo su same shi. Sai ga Nasir har akin Inna Meri, daman ai sun saba zuwa lokaci bayan Lokaci ko ba su Mu'azzan suna zuwa gaida Inna Meri. Nasir ya mika ma Mansoor hannu suka tafa lokaci aya yana fa in "Aji aji manyan gari." Mansoor ya ce"Nasir kana nan a gari abin ka" Nasir ya ce"Karyan tsiya kake yi baka neman mutane, ya wasa? Aji ka kusa haurawa waje fa duk garin nan hiran irin taka ledan ka ake yi, ranar muna gaddama da wani a wajen aikinmu na ce ai Aji tun a Nasara Team kowa yasan guru ne a taka leda na gaya masa lamba goma kake bugawa ya ko san duk wanda ke buga lamba goma ya kware a sanin wallo." Mirmishi ya yi bai yi mgana ba, sai Mu'azzam da Nasir suka koma hiran wallo Jefi jefi Mansoor na tsoma musu baki. Daman Mu'azzam mafarkinsa ne kwallo, Shi ma Nasir haka in suka ha e hiran su kenan wallo. Sun fi awa a akin Inna Meri sannan suka fito kofar gida sun jima suna hira kafin su yi sallama akan sai sun ha u da sallah. Nasir ya tafi ya na yi ma Mansoor tsiyan da azumin nan sai yasa yara sun ki aa masa gwuro. Mu'azzam na ta dariya shi kan shi Mansoor din sai da ya yi mirmishi. Daga Mansoor har Mu'azzam nan suka yi mangariba da isha'i bayan Mu'azzam ya maida Junior wajen maman shi tare kuma da Baba anjuma suka ci tuwon masaran Inna da miyar kubewa. Bayan sun gama kuma suka zauma suna ta hira, yau Inna ce ke da turaka shi ya sa suka samu zama da Baba Danjuma sosai. Sai wajen goma suka baro gidan suka koma gidan Mansoor suka kwana washegari Mu'azzam da iyalansa suka koma kano. Duka duka sun tafi da kwana goma aka fara azumin Ramadana. Kamar yadda suka saba ha aa hannu shi da Mu'azzam duk azumi su siya komai buhu a raba nan cikin gida da kuma makota. Sannan kowannen su ya aika da ku i danginsa, Shi Mansoor ya tura sakon kudi a can kwami shi kuma Mu'azzam nan Anguwan bolari inda aka haifi mahaifiyarsa. Inna Meri ba ta yi sakacin da suka manta dangin su ba, sannan kaf an'uwansu mata sun samu siga da gero na kayan azumi. Bintu kuma 50k Mu'azzam ya tura mata Mansoor kuma ya siya mata firiza da ta ce ta na so zata fara saida Zobo da ruwan sanyi da azumi. Sannan ya ba ta jarin kayan zobon ranar Bintu ta tiki rawa abokiyar zamanta ta sha habaici da Bashir ya yi magana ta ce ya kyaleta itama in taji haushi yayyenta su siya mata. ****** Hajiya da Mimi a na saura kwana hu u a fara azumi suka aga umra, Hajiya ce daman duk Azumi can ta ke yin azumin ta wannan karon kuma ta matsa tare da Mimi za ta tafi sai Daddy ya niya musu suka tafi tare aka bar ma Baaba Uwani amanar gida. Hajiya ta je ara yi ma anta Kabiru addu'a tare da Binta ita kuma Mimi ta je yin ma Abin addu'an Allah ya bashi lafiya duk da ta ta a zuwa Umra sau biyu. Hajji kuma sau aya ta ta a zuwa lokacin da ta gama bautar kasarta ne kafin ta koma kano ta yi master inta. Tunda suka je ibada kawai suke yi, kuma daman ba ta da matsala da wajen aikinta tunda Umra ce, ba ma ita ka ai ta je ba har news manaja din su yaje shi da iyalansa sun ha u da shi acan, sannan har Madiha sun gani ta je ita da mijinta da anta amman su ba acan suka yi sallah ba. Tun suna Umra Rukky ke damun Mimi a chart da mganar bikin Bibi sai da Mimi ta yi mata alkwarin in da ta dawo ba zata ja baya ba da ita za'a yi komai a gama in sha Allahu. Acan kuma ta siya ma Bibi zanin gado mai kyau na guddumwa. Ranar salla ta yi Hoto ta ora shi a status in ta mutane suna ta cewa yaushe za ta dawo? Gidan karamchi Talabijin na kewarta. Daman tunda suka tafi ba ta cika amfani da waya ba sai jefi jefi ta dukufa addu'an Allah ya cire mata Soyayyar Mansoor acikin ranta ko zata samu sauki acikin ranta, ba ta san cewa Na Misau ya dauki hoton ta ya je shafinsu na Faceebook ya orata tare da cewa. " Fatima kabir sulaiman dabo(Mimin karamchi) na yi muku barka da sallah daganan Birnin Madinatul munnahwara." Ita ba ta man san ya saka ba sai da daddare da zata kwanta ta bu e data ta gani ta sha comment har wani na fa in" Hajiya Mimi Madina ta kar eki har kin kara jan kumatu." Sai da kalamansa ya sa ta yi dariya har ta yi masa reply da cewa" Zama waje aya ne, kafin na dawo manaja ya rika sani fitar dafiya." Shike nan sai aka fara cecekuce ana ta hira ta jima online ta na yi ma masoyanta reply ita kanta ai ta yi nishadi sai da Mommy ta kirata Vedio call sannan ta koma suna waya da ita tare da Abi da duk ya kara ramewa ya tsufa saboda ciwo. Hajiya har ta fara barci ta tashe ta suka yi mgana da Mommy da Abi. Su ma suna ta shirin dawowa gida nan da sati mai zuwa. **** Mu'azzam da matarsa da ansu duk anan suka yi salla sati aya suka yi suka koma kafin komawarsu sun ha u kan bikin Makama amman babu Mansoor ba ya nan sun tafi Bauchi buga wasa su kansu ba su damu da shi ba sanin ba zai shiga wannan hurumin ba, ta bakinsa ku ri a yin abu na masu Aji mana. Tun ana washegarin sallah ya tura ma makama 150k guddumuwa kuma ko da ya kira shi a waya ya yi masa godiya bai auka ba. A chart kuma ya yi masa mgana bai bu e sakonsa ba, ya yi ma mu'azzam korafi ya ce kada ya damu ba ya son ya yi masa godiyar ne shi ya sa bai auki kiransa ba. Sun tattauna yadda za su shirya dinner da sauran bukatun amarya Nasir suka bar ma komai a hannunsa tunda shi ke zaune a gari. Kuma shi ake ba ma jagoran zama da amarya domin ya ji tsarinta. Bikin zai kama 28 Ga watan April, tunda an ara sati aya. Nasir ya je gidan su Bibi sun ha u da Rukky tunda kamar ita ce ja gaba kan komai sun yi mgana, Nasir irin mutanen nan masu maagana kai tsaye ba su tauna ta Sai da ya yi ma makama mganar yayar matarsa ce za ta ci ma kanwarta awa ne? Makama yace to in ma hakane ina ruwansa. Nasir yace"Shi fa na gani babu ruwana ai da din kallo ne da shi." Bayan guddumuwar da suka ba ma Ango sun ba ma Amarya ku in gyaran jiki da na abinci inkunan kuma da aka sanya a acikin akwati Ahmad ya inko su duka ya aiko da su da yazo sallah daman ya ce Makaman ya bashi zai inka ma amarya kayan fitan biki. Kala goma ya inka mata kaya masu kyau da yarari ga su sun ha u da tela wararre sai kayan suka fita sosai. Ana saura kwana goma biki aka kawo kayan aure akwati bakwai da ghana Must go. Mimi da Rukky daga wajen aiki suka zo tare ta ga kayan sai dare ma ta koma gida. A yadda Rukky ke ba ma Mimi labarin abokan angon da Angon kanshi sun yi kokari sosai ba su yi waron hannu ba. Dinner daman su suka ce a bar komai a hannunsu za su shirya daga bangarensu. Saboda Rukky Mimi ta shiga bikin kuma Bibin ma ta ce"Don Allah Anty Mimi kune yan gayu ki tsara min bikina." Har sai da tayi dariya, da ta kawo mata zanin gadon da ta siya mata da ta je Umra har Babansu Rukky sai da ya yi mata godiya. Hajiya ma ta ba da 20k ta kaima Mamansu Rukkaya. Duk Lokacin da Angon da abokonsa za su so Mimi ba ta nan ko suna wajen aiki kuma da daddare sukan zo lokacin ta koma gida. Ana saura sati aya biki suna mota ita da Rukkya daga wajen aiki za su shiga kasuwa Rukky tana ta mita da tsaki. Mimi ta ce"Wai me aka yi miki ne? Kin ishe ni da mita" Rukky ta ce"Ni da abokin Usman ne da suke zuwa tare ba shi da mutumci shekaran jiya kallo na fa ya yi yana cewa wai Amaryan nan ba ta da awaye ne sai ke? Mimi ta fasjhe da dariya kafin ta ce" Gaskiya ya fa a kina Yaya kin zama awar anwarki." Rukky ta ce"To ina Bibi ta ga wasu kawaye Allah na tuba, ai na yi ta jaraba Usman ya bani hakuri da cewa haka yake