← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 208

Sashe 35

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Uwa uba kuma mijinta na sonta kuma ya na tattalinta sannan ita kanta Meri mace ce mai alheri da maida kowa nata shi ya sa ta kasance a bar son kowa suka riketa kamar ar su, duk da shima ba shi da iyaye amman yana da kanne da yan'uwa. Duka duka auransu bai kai shekaru biyu ba ta haihu ta samu a namiji sai aka sanya ma sa sunan mahaifin Meri wato Mansoor, shi ne silan da Meri take kiran Mansoor da suna Baban Inna, a farkon rayuwarta ba ta ta a tunanin wata rana mutuwa za ta yi sanadin rabata da wannan rayuwar da take ciki ba, ta zama yar garin mallam Sidi sai dai in ta je gida ziyara da ganin an'uwa kowa sha'awarta yake yi ganin ta kowani Fanni ta samu jin da in rayuwar da kowacce mace take fatan ta samu. Sai dai kash ita mutuwa ba ruwanta da jin da da zaran lokacin ka ya yi sai ka tafi. Mansoor na da shekara biyar a duniya Mallam Ibrahim ya rasu sakamakon kayar kifi da ta makale masa ya yi ta amai dare zuwa safe an yi an gama, Meri ta yi kuka kamar ranta zai fita ba abin da ke kara saka ta kuka sai in ta aga ido ta kalli Mansoor mai kuruciya da kananun shekaru da bai san komai na rayuwa ba har ya zama maraya, yan'uwanta sun zo har akayi bakwai sannan Inno soro ta zauna tare da ita har akayi arba'in ta so ta tafi da Meri can gabanta ta ida sa takabanta sai an'uwan Ibrahim suka hana suna kuka suna rokon Inno soro ka lda ta raba su da Meri da Mansoor su ka ai suke gani su tuna da an uwansu Ibrahimu. Sai inno soro ta tausaya musu kuma ganin ba abin da Merin ta nema ta rasa sai ta bar ta a nan ta koma argugun, Allahu akbar Allah mai tsara komai yadda ya so a hanyarta ta komawa gida har ta sauka a garin argugun ta samu a kori kuran dake aukan mutane zuwa cikin kauyakun su to anan ajalinta ya sauka suka samu hatsari nan take Allah ya yi ma Inno soro rasuwa Meri ta yi kamar ta haukace ga rasuwar miji ga ta uwa abun sai ya yi mata yawa dole ta shirya ita da Mansoor da Yalwar kanwar Ibrahim suka tafi can har aka yi bakwai da farko Meri ta so ta yi zamanta a garinsu ne sai 6an'wan ibrahim suka ce ko bayan kasa ya shafe idanuwan Ibrahim ba za su bari Iyalansa su rasa mafaka ba, da roko da ban baki kawun Meri mai suna Surajo ya amince ya ba su Meri da anta Mansoor suka dawo garin Mallam Sidi da zama a kuma cikin dakin mijinta suka riketa ita da anta. Bayan ta fita takaba saboda halin rayuwa duk da suna kokari a kanta ba za ta ce ta zauna a haka ba. Sai ta fara sana'ar cikin gida saboda dogara da kai ba domin yan'uwan Ibrahim ba su barta ta neme wani abu ta rasa ba amman ai ba zaka zama a kwance komai sai an dauka an baka ba a kallah dai kai ma a ga kana wani abun domin taimakawa. Ta zauna da su na tsawon shekara aya har Mansoor ya fara makaranta fimari anan cikin garin Mallam Sidi. Tun tana garin Mallam Sidi a ke kiranta da Inna Meri, saboda ita Innar kowa ne yara da manya kowa nata ne kyauta da Alherinta ya sa ta ke zaune da kowa lafiya Mansoor kuma ya na ganin gata saboda su na ji da shi suna kallonsa kamar makwafin an uwansu Ibrahimu ne, tun Mansoor ya na araminsa Inna Meri ta fahimci cewa ya na da bakar zuciya da kafiya ga naci ko fa a ya ha asu da yara sai ya yi kwanaki bai bar mganar ba, tun mahaifinsa na da rai in ta yi mgana sai ya ce zai bari yarinta ne. Ko ita ce ta dakesa sai ya kame a waje aya yana huci da kumburi kamar wani mai Aljanu in za ta kara masa sai an'uwan uban su hana su a tunaninsu yarinta ne ya na girma zai daina sannan ga shi da fitina komai shi a wajensa na fitina ne, saukinta aya suna tare da masu kaunar su shi ya sa abun sai bai cika damunta sosai ba sai da kaddara ta sake jefa ta a wata rayuwar sannan ta san illar halayen Baban Inna a wani muhallin. Gaddaafi anjuma wanzan. Ya kasance wanzamin dake yin wazanci a tsakanin kauyen su na karamar hukumar kwami saboda sunan da gidan su ya yi, ya sa duk tsukin nan suna zuwa cire beli ko kaciya ko wani abu da ya shafi kuna suna ba da maganin gargajiya sai a samu dacewa. To anjuma ya kasance wanzamin gidan su Ibrahim Sufi sannan har shayi ma shi ke yi ma yaran gidan in aka haife su, Mansoor ma shi ya yi masa shayi lokacin da ya cika shekaru uku, sannan akwai abota tsakaninsa da Ibrahim tun ya na raye, ya na siyan Kifi a wajensa akwai dai mu'amala mai kyau domin hatta Inna Meri ta san shi, har bayan rasuwan Marigayi Ibrahim in ya shogi garin yana zuwa ya ganta har ya yi ma Mansoor kyauta baya dai zuwa hannun rabbana. Tun Meri ba ta fahimci akwai wani abu a zuciyar anjuma ba har su Yalwa suka fahimta sai ba ta auki abun da gaske ba, tunda ta san matansa biyu a lokacin ashe abunda ba ta sani ba aya daga cikin su Allah ya yi mata rasuwa ta rasu ta bar a uku mata biyu da aramin yaro namiji. Kuma ta san hakane bayan Danjuma ya gama zagaye zagayensa ya fito ya sanar da Inna Meri manufarsa na son auranta domin ta taimaka ta ri e masa yaransa duk da yanzu suna hannun dangin ita matar tashi ne, amman ya fi son shi ya rike ansa da kansa. Bai oye mata komai game da labarin matarsa ba wato uwargidansa Magajiya kenan. Fitinanniya ce mara kirki, ta yi rantsuwan ba za ta rike masa a ba nata sun isheta har ga Allah da farko Inna Meri ba soyayyar anjuma ya sa ta amince da auransa ba, sai illah tausayin yaran da aka mutu a ka bari tunda yace har da aramin yaro dan shekaru uku da wani abu da ba ya yarda da kowa, Sai ta juya ta ga itama marayan da aka mutu aka bar mata a na kowa ne ba ka san wanda zai rike maka na ka ba watarana bayan kasa ta shafe idanuwanka ba. Ba ta yanke hukunci ba sai da ta yi shawara da yalwa ita kuma sai ta yi mgana sauran annen Ibrahim wanda acikin su ashe akwai wanda ya so ya auereta sai bai furta ba ganin kamar Inna Meri ta nuna ra'ayinta a kan anjuma saboda rike marayu sai ba su hanata ba saboda in dai kyawun hali ne da hakuri da kawaici da sanin ya kamata Danjuma ya cancanta tunda sun san shi tun ya na matashinsa kuma gidansu babban gida ne mai kunshe da tarihi. Sai su ka ba ta damar ta yi za i cikin guda biyu ko kanin ibrahimu mai suna Muftahu ko anjuma ita kuma sai ta bar ma Allah za insa sai taji tafi natsuwa da auran babba wanda ya mallaki hankalinsa kansa tunda a lokacin Muftahu saurayi ne bai ta a aure ba, annen nasa maza uku ne Karimu ne babba sai yakubu yalwa sai muftahu shine aramin su daman Ibarahimu ne babban su. Karimu ne ya yi aure da matarsa acikin gida yalwa ma ta yi aure nan makota da su, sai yakubu da shi ba agarin yake kasuwanci ba yana garin bauchi ne kuma shi bai wani damu da zumunci ba sai ya jima bai zo garin ba. Ita kuma Inna Meri sai ta yi duba da gwara ta auri anjuma ko bakomai Allah zai ba ta ladan rike marayun da suka rasa uwa a ananun shekarunsu. Lokacin da ta gaya musu za inta ba wanda ya nuna bai ji da i ba sun yi mata fatan alheri yalwa ce ma ta yi ta kuka tana fa in za ta yi nesa da su Inna Meri tace suna tare ina nisa tsakanin garin mallam Sidi da Gombe za ta zo itama ai nan gidansu ne zata rika zuwa ta na ganinsu tana kuma kawo musu Mnsoor. Tunda akwai kyakyawan alaaqa da fahimta a tsakaninsu shi ya sa ba za su iya raba ta da Mansoor ba amma sai dai anjuma ya ba su tabbacin shima Mansoor ansa ne kuma yayi alkwarin yadda suka ba shi Amana to zai kula da amanar Mansoor har karshen Numfashin sa, sun kuma aminta da shi sai suka bashi Amanar Inna Meri tare da Mansoor ba da ewa aka yi auran Inna Meri ta bar garin Mallanm Sidi tana kuka yalwa da Marliya matar karimu suna kuka sula kuma rakata har Gombe a akinta na gidan Wanzamai. Tun a ranar sula san Meri ta shigo wata rayuwar da ba ta saba gani ba, ba wanda ya kar e su a gidan nan sai Harira Magajiya kuwa sai bala'i ta ke yi tana zage zage tun a ranar farko Inna Meri ta san sai ta ninka hakurinta kuma ba ta damu ba tunda Danjuma ya gaya mata komai bai rufe ta ba, Abun bakincikin su ganin Inna Meri ta zo da yaro shikenn Magajiya ta rika sakin habaicin anjuma da kwashe kwashe ya je ya kwaso wata kuma mai a ta zo musu da Agola acikin gida, kafin su Yalwa su tafi sai dai suka kara jadaddama Inna Meri hakuri da kauda kai ta ce in sha Allahu zata zauna da kowa lafiya suka rabu suna kukan sabo Mansoor kuma sai jin da yake yi a ganinsa kamar irin sun koma sabon gida ne sai da su yalwa za su tafi ya saka kukan sai ya bi su dakyar aka lallashe sa sai da Danjuma ya ja shi shago ya siya masa alawa sannan ya yi shuru amman ya yi ta kuka ya na numfaashin zuciya. Inna
Chapter 35 · 0% Book details