← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 208

Sashe 120

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fa matar Agolan nan na gida fa aiki take yi sannan har mota tana da shi, sai ni ce zan zauna na koma baya" Uwar kuma na jin haka tace ta sha kurumin ta motar banza za a siya mata mota da haka ta samu ar ta saki jikinta. Daga arshe ma sai ta ji itama aikin Gidan Talabijin in take so, itama ta sanu a duniya a santa kamar Mimi, shi ya sa sai ta yanke shawaran fara shige ma Mimin su kulla awance ita ko ganin cewa Mimin ba sa'anta ba ce ita fa iyakar ta 24 a shekaru ko Bintu ta girmeta, amman wai awance za ta Kulla da Mimin da ba'a sa'arta ba, ita dai Mimi sama sama ne ba ta wani saki jikinta ba, tun ballantana da ba zaman gidan take yi ba sannan kuma ta fara fahintar halin Maeesha. Domin komai ta gani a akin ta sai ta ce itama an siya mata irin shi ko tana da Irin shi, sai ta yi ta tunanin aryan arziki da nuna itama ba'a fita ba Ita kuma ba ta san wace ce Mimi ba, ba ta da wannan halin ko ka an domin yar na gada ne ba hayan arzikin ta yi ba. A lokacin kuma daman Mimi da ku in albashinta ta siya ma Bintu da Walida Abayas masu kyau na alfarma sannan ta siya ma Inna Meri atamfa mai kyau da takalmi su Yaya Amina kuma ansu ta siya ma kaya da takalma har Magajiya ma sai da ta siya ma turmin atamfa, da aka kai mata a reni ta amsa abun ya tsaya mata a rai ta so ace yau ita ce za ta ri a wannan kyautar alfarman ba Meri ba, sai dai ba ta sani ba shi Ubanigiji yana tafiyar da duniya da nutanen cikinta ne a yadda ya tsara. Aji sai da Inna Meri ta ba shi labarin abun arzi in da Mimi ta yi musu ta ce ya ta ya su godiya har kayan ta nuna masa. Ya ga ni ya ce Allah yasa albarka sannan da ya koma aki maimakon ya yi godiyar da Innar tace ya yi sai ya bige da neman fa Mimi ta sha wankan ta ta ci kwalliya kamar za ta je gasar kyau ta zo ta tsaya gaban Aji ta na masa Juyi, daman haka take yi ba ta kyaleshi sai ya furta ta yi kyau in abinci ne ya ci ta ri a mitan bai ce abincin ya yi da i ko ba ya so dole ya fara bu e baki yana mgana in ba haka ba Mimi ba ta barin shi ya huta. "Na yi kyau? Ta fa a tana baza masa kasan doguwar rigarta da ta rike da hannayenta lokaci aya tana kashe masa ido aya, kallomta ya yi lokaci aya ya ce" Kin yi kyau mana kamar a ladan" Ya fa a yana mata dariyan mugunta ata rai ta yi kafin ta ce" Ladan kuma? arin ta fara masa bugun kafa ne ya sa ya yi saurin cewa" I mean so Beatufull.". Sai ta washe baki tana fa in" Thank you My Aji." Abinci ta je ta kawo masa. Waina suka yi da rana ita da su Walida har Bintu a gidan ta yini, har su ka samu sa'in sa tsakanin ta da Maeesha tunda itama tare da ita aka fara aikin wainar. Bintu ce yar neman rigima daga jin Maeesha tana kiran sunan Mimi gatsal ba ma Mimi ba, fatima kai tsaye take kiran ta ko kunya ba ta ji ba. Shi ne Bintu ta kalleta a reni tana fa in" Gaskiya Maeesha ba ki kyauta ba, Ai in da kara Anty Mimi ba sa'arki ba ce tun da ai Yaya Saddiqun aninsa kuma shi ne yayanmu a gidan nan tana bukatar girmamawanki, in ba za ki iya kiranta Anty ba sai ki kirata da Mimi amman rashin Kunya ce ki ri a kiranta da Fatima kai tsayje wallahu na tabbata ko mijinta da Mimin yake kiranta gaskiya ki daina." Shike nan Maeesha ta sha a cikin gatse ta ce" To ina ruwan ki? Ai awata ce? Sai Binta ta kalleta sama da kasa kafin ta ce" Su awa manya." Daga nan Maeesha sai ta tashi ta bar Shashen tana cewa ita ba ta son rashin kunya, daman ta na lura da take taken Bintu so take yi ta ja ta da fa a, sai da Inna Meri ta fito ta yi magana ta ba ma Maeesha hakuri ita kuma Bintu ta yi mata fa a sai tura baki ta yi tana fa in" Wlh Inna ku daina sake mata munafunci ne ke kawo ta, ni fa wlh ba ta min ba ta cika over Sabi iyayi da nuna ta fi kowa." Inna Meri ta ce" To daman ba sai ta yi miki ba, nan dai ba gidan mijin ki ba ne, ita kuma gidan ta ne ba za ki zo ki takura mata ba." Bintu tace ai wallahi itama gidansu ne tun da gidan ubanta ne, ita dai Mimi ba ta yi magana ba, amman ita Allah na tuba awance da Maeasha kamar wacce ta koma baya ita kanta yarinyar ba ta yi mata ba, hallayarta duk marasa kyau ne ko a maganganunta. Aji bai yi ma Mimin maganar kaya ba sai da safe. Kawai ce mata ya yi" Inna ta nuna min kayan da kika siya musu, lalle ma wato ku i ne da ke wasa wasa yarinyar nan." Ya fa a har ya na ri e haba cikin yar mamaki, ita kuma sai ta ka a kai kafin ta ce" Ku i kuma? Ni ba ni da wani ku i domin ban kai ka ba." Kai tsaye ya ce" Ko da yake na manta kina aiki, sannan kuma Major ya mutu ya bar muku gado nasan kason ki yana da yawa kema." Wata harara ta je fe shi da shi, sai ya yi saurin aga hannuwansa sama lokaci aya yana fa in" Yi hakuri, kar yar Sojoji ta saka a zo a kamani dole zan yi ladabi." Yana gama fa a ya tura kofar yiolet ya shige ya barta nan. Har hawaye sai da ta share, shi ya sa da ya fito wanka ta yi masa fuska ya fahimci ta daman haka take yi masa wai ita mai Baba. Yana goge gashin kansa ya kalleta ta madubi tana zaune gefen gado tana latsa wayarta ya ce" Allah Sarki sorry mai Baba, mu kuma da ba mu da Baban Allah ya ba mu hakuri gaba aya." Duk domin ta tanka shi sai ma tashi ta yi ya bar masa akin, shi ta ke jira zai kaita wajen aiki motarta na gidan Hajiya jiya da ta je da wankinta wanda ke musu wanki zai zo ya auka daman tun bayan auran nan take kaiwa da ta yi dare ne ta kira shi ya zo ya auketa yana ta kunkuni har cewa ya yi" Allah sarki bawan Allah! Aji ya zama direban ar Major." Cikin gatse ta ce" Kwarai biyayya dole, a yi gaddama a kwana a zaune." Haka suka bar gidan Mimi na wani shan kamshi, a cikin mota ma saboda janta da fa a har kiran sunan ta ya yi da cewa" Mimin Aji wannan shan kunun fa? Sai kawai ta kalle shi ta auke kai shi kuma sai ya yi dariya kafin ya ce"Lalle ne ma." Har ya sauke ta wajen aiki tana shan kunu shi kuma sai kawai ya ce mata" Kar ki kuskura ki ce za ki kirani domin ba zuwa aukan ki zan yi ba, ni kike sha ma kamshi Mimi? ni ko?. Ya yi kyau" Haka suka yi rabuwar sai da ya bar haraban ma'aikan na su ta ri a mirmishi ita ka ai, a she dai in ta yi fushi ya sani ga shi duk ya damu kansa Saboda ta na shakan kamshinta, Allah ya taimake ta ya an rage mata takura tunda ta na zuwa gidan Hajiya gidan Daddy ma taje ya fi sau biyar gidan su Rukky ne ko ta masa mgana sai yace a'a, Kamar dai ba ya son Rukky ne daman ya ce munafuka ce. Da wuri ta koma gida, bayan ta biya gidab Jiya ta auko motar ta, tana dawowa gidan ta ga matar Nasir ta zo gidan Nafisa sunan ta, sai ranar Mimi ta ta a ganinta Walida ta ce tun safe ta zo da akace bata nan ne ta ce za ta jira ta, sai Mimi ta bu e mata daki su ka shiga, Nafisa yini ta yi mata sai yamma ta tafi sun sha hira Mimi har goya mata Bby ta yi mai suna humaira. Mimi akwai son yara daman, balle ga Nafisa mai hankali Kuma ko Mimin za ta girmeta da ka an ne, yini aya kamar sun shekara tare da za ta tafi ta ce ta na jiran Mimin, ita kuma ta yi mata al awarin za ta zo in sha Allahu. Da za ta tafi ta ha a mata su turaruka masu kyau sannan ta ba ma Bby humaira 5k, tun kafin Mansoor ya dawo ta kira shi ta ba shi labarin Matar Nasir ta kawo mata ziyara abin da ba ta sani ba sun ha u da Nasir in a Camp in su ya je ya same shi ya na yi masa tsiyan shi ya nemi shi tunda ya fahimci in a ka biye masa ba za a yi zumumci ba nan yake fa a masa Nafisa matarsa yau gidansu ta je, da ya dawo ne Mimi ta ce itama ya kaita don Allah tana so ta je har gidan Makama. Kai tsaye Aji ya ce" kawai da girma na sai a ganni ina zuwa gidan matan aure? Ki saka Walida ko Bintu wata cikinsu su ta raka ki, amman ni ki cireni a ciki." Mimi ba ta damu ta ce shike nan daman ba ta ce dole sai ya je ba, Ai ko ranar lahadi ta shirya suka tafi tare da Walida Maeesha ta na ganin za su fita ta ce itama za ta je sai su ka je tare da ita, Nafisa ta ji da i kwarai Nasir din ma na gida har cewa ya yi
Chapter 120 · 0% Book details