← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 208

Sashe 138

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

aki domin Matar Saddiqu za ta dawo nan ne cikin gaggawa. Walida ta same Inna zqune kawai ta yi tagumi, Hibba ta je gidansu Jiya ba ta dawo ba sai ta kwana a can, Junior kuma ya i zaman nan sai gidan Bintu saboda su Husaini. "Inna ko dai an zo aukan kayan sawan Anty Mimi ne? Walida ta fa a tana zama kusa da Inna Meri, ita kuma sai ta girgiza kanta kafin ta ce"Ban sani ba, makullin akin kawai ta tambaya." Ita kanta Walida duk jikinta ya yi sanyi, Uban gayyar kuma tun ranar da suka zo da Nasir ba wanda ya ara ganin shi Baba anjuma har ya yi tunanin su je gidan Sanata Hamza shi da abokinsa Mallam Hashimu su ba da hakuri Inna ta hana ta ce shi wai mai auren bai damu ba sai su ne za su damu kansu? Ai abin da ya nuna ya nuna ma duniya shima hakan ya za a. Cewa ma ta yi in dai ya je ita ba da yawunta ba, Shi ya sa sai ya dakata shi kuma gogan in an neme sa sai ya ce kar kowa ya saka baki yana tutiniyan duk in da Ma Mimin ta je a cewarsa za ta dawo ne ma. Har su Yaya Amina sun so su zuwa har gidan Hajiya su Samu Mimi su ba ta ha uri Inna Meri na ji ta ce kar wacce ta taka ta je, ba hurumin su ba ne. Su dai suna zaune sai gani suka yi wata mata ta shigo Hajiya Turai, Mama ita ta le akin Inna ta ce a gaya ma matan gidan Maza za su shigo su fita da kaya shike nan ta faru ta kare. Daman Zuwan Mama kayan Sawan Mimi ta gama ha a mata duka a cikin akwatinta da duka kayan kwalliyarta da takalmanta, Inna ko iya fita ba ta yi sai Walida ne ta je ta gayama magajiya Maza za su shigo aukan kaya. Tana jin haka ta san Dalili a ranta ta ce abin dai ya tabbata kenan Daman itama duk ita da gayama ya anta har Maaeesha dake gidan Zuwaira ta je ta kai mata labari sai ta ji da i ko banza za ta zama tauraruwa a wannan gidan. Kuma ta ji da i da za ta koma akin Mimi Saboda ya fi jin kayan gyara sannan ya fi kyau komai na fantin akin da abubuwa Uniqui ne masu tsada da yarari. Walida hankalinta ya ta shi ganin da gaske fa tunda ana ta fita kaya. Sai ta Lalla a ta saci wayar Inna Meri ta Kira Bintu ta sanar da ita abunda ke faruwa sai ta ce ga ta nan zuwa ta kuma ara kiran Hibba ita sai ta ce ta na kan hanya tunda sun yi waya da Mu'aazzanm tun asuba ya ce ya ta so. Da Bintu da Hibba a kofar gida suka ha u suka shigo gidan lokacin har gqdon Mimi an kwance an fita da shi Kujeru ne su ka i fita a na tunanin a haura da su ta garu kamar yadda dama suka shigo gidan tun farko. akin Inna suka fa a cikin wani yanayi Bintu ke fa in" Inna ke kika ce su zo su kwashe kaya? Inna Meri ta yi shuru ba ta yi mgana ba sai Walida ne ta maida musu abin da ya faru, Bintu ta auko wayarta daga aljihun rigarta ta lalubo lambar Yayan na su ta kira shi amman wayarsa tana kashe ne so take yi ta sanar da shi abin da ke faruwa ila in ya ji ya zo ya dakatar da su. Hibba fa i take yi" Inna domin Allah ki dakatar da su mana.". Inna Meri ta mi e tana fa in" Saboda wani Dalili Hibbatu? Ba ni da wannan hujjar." saboda ma kar su dameta fita ta yi ta zuba ruwa a buta ta zagaya ta kama ruwa tana fitowa ta auro alwala ta zo ta shige ciki ta shimfi a sallaya ta kabbarta salla. Ganin ba mafita ya sa Bintu ta ja hannun Hibba suka fita lokaci aya tana fa in" Mu je mu yi musu mgana. Wlh makiyan gidan nan dariya suke yi mana." Sun shiga akin sun iske Mama da Turai suna maida wasu kayan Kitchen in a cikin kwalayensu bayan sun gaishe su sai kuma suka kasa mgana har sai da Mama ta ce"Lafiya ko? Bintu ta marairace kafin ta ce"Don Allah Mama ku yi hakuri da kwashe kayan nan, shi fa Yaya Mansoor bai ce ya saki Anty Mimi ba." Mama ta yi yar dariya tana kallon anwarta Kafin ta ce" N ma yar aikace, umarnin Babanta ne ya ce Lalle lalle yau mu zo mu kwaso mata kayanta." Turai ta ce"To tunda har ya ce ba ya sonta zaman me za ta yi da shi? Mama ta ce" Babu kam, abin da yake so ne ta yi masa tunda ta ce za ta tafin ya ce gwara ta tafin." Da sauri Hibba ta ce"Sharrin she an ne, sannan fa an ma'aurata ne, in da an an dakata za su iya sulhunta kansu." Mama ta sake yin yar dariya kafin ta ce" To wannan kuma ban sani ba, amman ni dai yanzu Umarnin Babanta na ke aiwatarwa." Duk iya okarinsu amman su Mama ba su saurare shi ba. Daga karshe ma suna mgana sai suka yi musu kunnen uwar shegu. Dole su ka fita jiki duk a sanyaye sannan sun koma suna ta kiran Mimi ba su sameta ba, abin da suka lura shi ne kamar ta rufe su ne ba za su ara samun ta a waya ba. Suna ji suna gani aka kwashe kayan Mimi gaba aya tas kayan abinci ka ai suka bar musu a kitchen da za su tafi suka ba su makullin akin ba su ko ga Inna Meri ba ta na cikin dakinta. Makota ko sun cika ofar gida ana maida mgana, wanda ma bai sani ba duk ya san abin da ke faruwa Magajiya na tsakar gidan tana dariyan zuci burinta ya cika. Mariya ba ta cika zama a nan ba ita ce gidan Zuwaira ko gidan Auwalu, Saboda anan ba za ta sake ta ri a yin ta e ta e yadda ta ga dama ba sannan magajiya na takura mata kuma ba sa shiri da matar Saddiqu. Sai ga akin da Mimi ta yi rayuwa fayau ba komai a ciki haka su Hibba suka koma akin inna suka yi jugum jugun abin haushi ma ba'a ade ba sai ga Saddiqu ya shigo Shashen shi da wani abokinsa ba sallama ba komai suka shige akin suna dubawa ba in ciki ya sa sai Bintu da ta yi kwallah ta ce ma Hibba bari ta je ta dawo ta fice daga gidan gaba aya tana jin magajiya na shewa ita da Gaje daman ai murna za su yi. Daga nan Binta mashin ta hau zuwa gidan Yaya Amina domin ta sanar da ita halin da ake ciki ya kamata su san matakin da za su auka kafin su zama abun dariya a cikin gida da ma ota. ****** Duka kayan Mimi gidan Daddy a ka sauke su,. Sai dai kayan sawanta ne Mama ta aika mata da su gabadaya gidan Hajiya. Washegari Asabar Mommy ta biyo jirgi ta zo Gombe, can gidan Daddy ta je ta same shi suka tattauna bai fito ya nuna mata manufar shi ba amman ya ce sai ya nuna ma yaron nan Mimi yar gata ce, in yana sonta zai kawo kansa ya kuma ce kar ma wanda ya takuramata da Maganar komawa tukunna a yaleta sai ta kara samun natsuwa da hutu. Dole Momny ta bar mganar shi ya sa ma kwananta aya ta juya, sun yi sa ani ba ta da e da tafiya Dr. sulaiman ya zo garin shima, Duka dai bayanan da Daddy ya yi ma Mommy shi ya yi mishi ya ce kuma su taimaka masa wajen dawoma da Mimi darajanta a idon mijinta su cire bakin su su bar shi da shi da Mimin gaba aya. Shima in bai kwana ba a ranar ya bi jirgi ya koma kano amman ya je gidan Hajiya ya gaisheta sannan ya ga Mimi sun yi mgana shi dai ya ce ta kwantar da hankalinta komai zai wuce kamar bai faru ba. Khadi kuma aiki ya hana ta zuwa amman Kwazzaba yasa sai da Mimi ta amsa wayarta. Har tambayan Mimi take yi wai daman ance ba en maza sun iya rashin mutumci tana so dai Mimi ta bu e mata cikinta ita kuma sai ta i, ce mata kawai ta yi i ta ta ce ta na so daga farko yanzu kuma ta ce ta ha ura ba dole sai an matsa mata anji dalilinta ba, itama tana da wayon ta san kowa na rufe siirin shi ita ba za ta bar na ta a bu e ba, ko da ta za i rabuwa da Aji har yau har gobe zuciyarta ba ta daina son shi ba. Kawai dai ta za ar ma kanta barin rayuwarsa ne saboda imar iyayenta, Sannan kuma yana da hallaya masa kyau in da ba za ta iya zama da shi ba, to wanda bai da kyakyawan zuciya ai zama da shi hadari ne. Mutumin da ba ya ganin ka da kai da Iyayenka a wata tsiya ai ba amfanin zama da shi. Madiha kam da suka yi waya ce mata ta yi" Zan yi supporting in ki karo na farko Sisto, In bai sake ki ta arzi i ba to za mu maka shi a Kotu alkali ya kar an miki yancin ki, kin fi sa komai shi ne zai yi asaran rasaaki, ke kuma sai dai ki samubwanda ya ninka sa. daman abin da Abi ya guda kenan tun farko amman at last dai Hajiya da Mommy sun kasa ganewa ke ma wawanci ya rufe miki Ido, amman kar ki damu ba ki makara ba abin da kuma kika yi kin yi dai dai i support your Decession." Mimi dai ba ta ce mata komai ba. Daman ai madiha kowa yasan irin kalamanta kenan, ta kuma san za ta fi kowa jin da in abin da ya faru,
Chapter 138 · 0% Book details