← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 208

Sashe 160

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ci wainar da Inna ta aiko masa sannan ya sha tea ya ha a da soyayyen buredi da wai. Yana gama ci ya natsa kawai sai ya koma ya kwanta ya yi ta barci tun yau ba su da Traning sai gobe yana ta jin hayaniyarsu sun fita can haraba amman bai iya ta shi ba, wayarsa ma kashe ta ya yi sai gabda azahar ya ta shi ya yi wanka lokacin har sun yi sallah tunda suna da masallaci a cikin Camp in sai ya yi na shi a cikin aki sannan ya kunna wayarsa. Ya duba sakonni masu muhimmaci, har da sakon Mu'azzam daman ya fa a masa zai je wajen Mimi a jiyan, sai a lokacin ya tuna da takardanta da sauri ya mi e ya isa ga ma sagalan kayansa ya zura hannu a aljihun wandon da ya sa jiya ya auko takardan ya zo ya zauna a saman aramin gadon dake akin ya warware ya fara karantawa.. *SHARU AN KOMAWA TA GIDAN AJI.* 1. BA ZAN KOMA BA SAI NA SAKE YIN WANI TARON BIKIN. 2. SAI KA HA AMIN LEFE, DOMIN BAN AUKE MAKA BA. 3.SANNAN ZA KA RI A ZUWA TA I, DUK BAYAN BAYAN KWANA UKU, DA KUMA YAWAN TURAMIN SA ONNIN SOYAYYA.. 4. NA ARSHE SHI NE SAI KA GYARA MU'AMALANKA DA KOWA CIKI HAR DA SASANTAWA DA ABOKAN KA, DA MAI DA DANGINKA DANGINA DA MAIDA DANGINA DANGINKA." "Amincewar ka ga sharu dana sune tikitin komawata gidan ka." asa sai ta rubuta sunanta Fatima Kabir Dabo, shima daga gefe sai ta rubuta sunan shi Manaoor Ibrahim aji, sannan daga kasa ga wajen saka hannu da kawanan wata. Ya maimaita takardan ya fi sau goma amman ya rasa wani yarinta ne ke damun Mimi? Wai sai ta sake sabon taro ? Shi na lefen ma bai dame shi ba, sannan wai ya ri a zuwa ta i sai kace mara aikin yi? Ga tura sa onin soyayya wannan ai ga na masa azaba kawai za ta yi ina ga ya ga lokacin wannan shirmen tab, ko ta a takardan bai yi ba ya ninke ta ya ijiye. Sauran wainarsa na safe ya ci ya sha ruwa sannan ya fita da kwando waje, Su Zinder ya gani ya ba su ya ce su cinye su wanke kwanon, suka kar a suna mai fa in" Thank you Captain." Shi kuma sai ya koma aki yana duba takardun da Coach ya ba shi jiya sai wajen uku da Rabi ya ta shi ya yi wanka ya sauya kaya lokacin har sun wanko kwanukan sun dawo da shi, azumi ke gabatowa akwai tunanin ba su hutu zuwa bayan sallah. A masallacin cikin Camp in ya yi sallar la'asar sannan ya kwashi kwandon da aka kawo masa abinci sai gidan Inna, nan kuma ya iske ba ta nan Bintu ce kawai da Walida a gidan wei ta je can anguwam Arawa matar Saddiqu ta haihu. Bai yi mamaki ba ya san halin Inna daman ba za ta zauna ba, bai tsaya ba ya ijiye kwadon abincin ya ce bari ya je ya dawo ya na fita suka fara gulmansa domin Hibba ta kyankyansa musu Su Yaya Mansoor ana ta zuwa biko. Har zuwan Mimi gidanta na kano sai da ta gaya musu. Yana fita daga gidan Inna sai gidan Hajiya yana Hanya ya Kira Mimi ya ce ga shi nan zuwa, kafin ya kariso ta ci kwalliyarta cikin dogowar rigar atamfa ta kuma kashe auri tana tashin kamshi yau kam ko mayafin ba ta saka ba. Sannan ta kawo masa abinci Jallop din shinkafa da nama ya ce ita ta dafa tace a'a sai ya ce sai ranar da ta yi masa girki sai ya ci kai tsaye ta ce"To in ka fara zuwa ta i zam ri a yi maka girki " Bai yi mgana ba yana kallonta kenan da gaske take yi, shima ya sha kwalliyarsa yau har da hula tunda manya kaya ya saka ta kalleshi tana dage masa gira lokaci aya tana fa in"Ehye, an sha kyau za'a zo ta i wajen ar budurwa." Ta fa a tana masa wani irin mirmishi, Kallonta yake yi ko kiftawa ba ya yi, da gaske take yi kenan? Sai kawai ya saka hannu a aljihu ya fito da takardan harda ma bironsa ya zo, a kasan Cafet ya sauko sannan ya kalli Mimi lokaci aya yana fa in" Matso ki gani." Ba nusu ta matso har kansu na ha uwa waje aya. Lambar farko ta ga ya tsaya sannan ya kalleta kafin ya ce"Ke yanzu ban da rigima ina ke ina ara yin wani biki? Kiran bidi'a ko ata lokaci? Ko sake aura mana aure za'ayi ba bikin da za mu yi ballantana haka kawai daga kin yi yaji kuma sai ki ce sai an yi biki. Gaskiya a'a ban yarda da wannan ba." Kawai sai ya saka biro ya soke ta kallesa cikin mamaki ba ta samu zarafin mgana ba ya je ga na biyu ya na fa in" Nawa kike bukata? Ya fa a sannan ya yi ticking lokaci aya ya zura hannu a gaban aljihun rigarsa ya auko Atm insa na bankin albashinsa, ya sauke a gabanta lokaci aya yana fa in" Daga naira aya har milyan ari za ki iya amfani da shi wajen ha a abin da kike so." Sai kawai ya gangara na uku ko ba ta damar magana bai yi ba. Ya nuna rubutun ta kafin ya ago yana kallonta lokaci aya yana fa in"Haba Mimi yanzu da girman ki kike wani zencen ta i? Haba ko yara kanana yanzu sun daina wannan ata lokacin mq? Me ye ta i in ba a zo a samu fahintar juna ba? Ni kuma d ke tun muna yara zukatan mu suka samu. daidaito ba amfanin da aueren mu, mu zo muna wani abun ata lokaci. Sannan mganar wai sa onin soyayya haba Fatima ni ina na ga wannan lokacin? Kin san fa yanayin aikina ni fa mutun ne kamar kowa ba zan miki karyan abin da ba zan iya ba, Mijin Novel ne ke tsara mace da kalaman Soyayya, ni kuma mijin zahiri ne, in Soyayya kike so tsantsan na gaskiya zan nuna miki ita a kan gadon mu na Sunna in sha Allahu" Ya fa a ya na kallonta asa asa, nakwa nakwa ta yi da fuska kamar za ta yi kuka sai ya saka biron hannunsa ya lakace mata hanci kafin yana fa in" Rigimammiya." Cigaba da duba takardan ya yi zuwa lambar karshe sai ta ga ya yi ticking lokaci daya yana fa in"Wannan ba matsala, Abokaina kada ki damu zan neme su mu sansanta duk da ni banga laifin da na yi musu ba, mganar dangina kuma daman ko Inna na ga alamun ta fi son ki a kaina. Sai mganar naki dangin ki suma in sha Allahu zan saki da su mu zama aya saboda ina son ki, kuma abin d mata take so shi miji ya ke so? Ko ba haka ba Mimin Aji?. Ya fa a ya na kallonta, kawai sai ya ga ta koma ta zauna a gabansa ta har e hannayenta saman kirjinta tana wani ata rai sai shima ya mi e ya zauna yana fa in"To kuma yanzu menene laifina! Na yi miki fa duka bayani" Kawai sai ta fara mgana cikin shagwa a"Ni dai wlh ko aya ba zan soke ba, kuma ai ba gayyata zan yi ba kawai dai kawayena da Yan'uwana mganar ta i kuma ni ko? Ba za ka rika zuwa kana ganina ba ko? Yadda ta yi mganar ne ya sa bai san lokacin da ya ce"Na ji shike nan sai kuma me? Har ta na jan hanci kafin ta ce" Ni dai in ba ka amince ba, sai na ce na fasa komawa." Har da kukanta fa, gefe kawai ya koma ya na kallonta kafin ya ce"Da girman ki, Mimi ki yi ta shagwa Sai ta ara narkewa tana matsan hawaye, Har ta na cewa shike nan tunda baya sonta ba zai mata abin da take so ba. Ya na jin haka ya arisa gareta ya ri o hannuwanta yana fa in" Sorry, shike nan na ji ki daina kuka" Da sauri ta ce"To ka amince? kai ya gya a kafin ya ce"To ya zan yi? Tunda na auri yar gata shagwa iya." Dariya ta yi masa sannan ta kwantar da kanta saman kirjinsa sannan ta jawo takardan ta saka hannu ta mi a masa ya kar a yana fa in"Kamar auran coci, ni fa ba guduwa zan yi ba." Tana dariya ta ce"Eh na ji dai." Haka nan ta saka shi ya saka hannu sannan ta auki takardan tana fa in" In na fara zuwa aiki zan ba da a yi mana photocopy, na ba ka naka nima na auki nawa." Sai ya yi fuska kafin ya ce"Ba na so, ki ri e a hannun ki kawai" Dariya ta fara ta na son kallon fuskarsa shi kuma ya ha e rai ya kauda kai.Sai bin shi ta ke yi, daga karshe ma ture kanta ya yi daga kafa ansa har ya na juya mata baya, ta shi ta yi ta koma gabansa ta na jan kumatunsa lokaci aya tana fa in"Ehem Ehem, kamo shi nan kamo shi nan." Har matse masa fuska ta yi sai da ya yi dariya kawai sai ji ta yi ya ri e mata hannuwana sannan ya rumgumeta yana sauke numfaahi, itama sai ta yi lakwas tana shakan amshin turarensa. "In na zo ta in me za ki ri a bani? Haka ya fa a cikin dishewar murya itama a hankali ta ce"Duk abin da kake so? agota ya yi yana kallonta kafin ya ce"Komai fa kika ce? Sai ta aga masa kai, sai kawai ta ji ya Sumbaci bakinta kafin ya ce"Har wannan? Sai ta fara waige waige tana zaro ido da sauri ta matsa daga jikinsa tana fa in"No." Mirmishi ya yi kafin ya ce"Ai ba ki isa ba kin yi alkwari yarinya." Tana tura baki ta ce"Ni ban yi ba, ba wannan a sharu dan mu." Kansa ya shafa kafin ya ce" Wa ya ga ya miki su Nasir na gaba da ni? Dariya ma ya
Chapter 160 · 0% Book details