Sashe 67
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kira tana fitowa ta mika ma ta wayar lokaci aya tana fa in"Ke kiramin yayanku" Walida ta kar i wayar kafin ta ce"Yaya Mu'azzam? Inna Meri a fusace ta ce"Mara mutumcin za ki kiramin, shi wannan ai an albarka ne mai jin mganar iyayensa." Tunda Walida ta ji haka tasan Yaya Mansoor ya tafka wata tsiya yau ta ha osu da Inna sai Allah. Lambarsa ta nemo ta kira ma Inna shi sai da ta kusa katsewa ya aga kiran muryansa a cunkushe kamar ko yaushe. Ko amsa gaisuwansa Inna ba ta yi ba cikin aga murya tac e"Ina fatan kana garin ko? cikin sauri yace"E, Inna." A kufulce ta ce" To ka zo gida anjuma ina son ganin ka" Ko ta jira ya amsa ta mika ma Walida wayar ita ce taji sanda ya amsa da Toh inna ina nan zuwa bayan sallar Mangariba sai dai aka bar walida da katse wayar cikin mamakin me ya ha a Inna da Baban nata kuma yau? koda ya ke kullum cikin fa a suke kamar wasu jika da kaka. Tana jin Inna tafiya ka an sai tsaki daga gani ranta ya na ace ne, Baba Danjuma kuma baya nan sun je wani kauye aurin aure. Inna Meri ta rasa ma abunda ke mata adi ta zauna ta yi tagumi ta auna tunaninta waje aya ko dai ta kira su Yalwa ne ta gaya musu domin ita a ganinta Baban Inna ya fi karfinta ta kasa gane masa su sako hannu a lamarinsa kila su ya ga girmansu. Har kiran walida ta yi, ta saka ta kira mata Babansa Yakubu sai a ka yi rashin sa'a ba ta same shi ba. Sai kawai ta fasa sai ta koma tace ta kira mata Amina domin ta rasa wa za ta fa a maganar taji da i acikin ranta. Amina na gidanta ta samu kiran Inna bayan sun gaisa da tambayan yara Inna ta fara fa in "Amina Baban Inna zai janyo mana wani bala'in." Dagacan bangaren Amina ta ce"Me kuma ya faru Inna?. Nan Inna ta zauna ta karanta mata komai har zuwan su Hajiya da abin da ya faru anan Walida ta ji bakinta ya i rufuwa Yaya Mansoor zai auri Anty Mimi kuma za ta zauna tare da su ita tunaninta bai kawo mata dalilin fushin Inna ba. Mamaki da al'ajabi ya kama Amina cikin mamaki ta ce"Ikon Allah su da kansu suka zo neman ya aureta kuma ya amince? Inna ta ce"To kina wata magana wai ba ga shi ina gaya miki abunda ke faruwa ba, ni ban damu da komai ba sai wai a gidan nan za ta zauna ko a ina ya ga aki Oho" Yaya Amina ta yi dariya kafin ta ce" Inna ga aki nan kusa da akin ki ba, kila shi ya ke nufi." Sai da Aminan ta yi mgana Sannan ta tuna akwai ciki da falo a karshen lungunta Lokacin da aka yi mata gyara ne aka fitar da shi bakomai a ciki sai karitai irin su tarkacenta wani lokacin har girki ma ta na yi aciki. Inna Meri ta auna matsayin Mimi wai itace Baban Inna zai kaskantar ya ce za ta zauna a wannan akin cikin jin haushi ta ce" Au to da nan ya kwanta ? To sai ya zo ya sakata in in gidan ubansa ne." Yaya Amina ta ga ran Inna ya aci ta fara lallashinta da cewa"Inna mu bi komai a sannu, ni na yi mamakin yadda ya yi saurin amincewa sai yau na kara yarda da mganar Mu'azzam da Binta da su ka ce har gobe ya na sonta, Inna ba ki da buri sai na ganin ya yi auran to tunda yanzu an samu ya furta da bakinsa zai yi don Allah ki yi hakuri ki bishu a sannu har mu ga abunda Allah zai yi" Inna Meri sai ta yi shuru ba ta ce komai ba cikin marairacewa Amina ta ce"kin ji Innata don Allah ki yi ha uri" Sai Inna ta sauke numfashi kafin ta ce"Shike nan Amina Allah shi sauwake masa to." Ita dai Yaya Amina nata ta lallashin Inna ne ganin yadda take a harzu e Sai da su ka gama waya ta zauna itama ta na mamaki ba ta raba ayan biyu Baban Inna na da dalilinsa ko da ace yana son Mimi har yanzu akwai kuma babban dalilinsa na Saurin amincewa cikin gaggawa haka. Inna Meri ko duk da Amina ta lallasheta amman a kufule ta yini har abun ya so ya shafi walida da yamman ba ta shirya taje islamiya ba ta same ta kwance kan gado ta na waya da wayarta ta na ganinta sai ta kashe ba ta san Inna ta ji ta ba. Daman tana jin haushinta ta rasa wani shegen yaro ne ya fara auke ma walida hankali, ta kuma san Baban Inna ya hana su zence tunda ya taba kama mariya na zence da wani dan can kasan anguwa yaron gidansu ba tarbiya ya ce duk ya kara ganinta ko ita ko walida sai ya karya kafafasun in mutun na son su ya zo ya ga manyan su, ba ta mata mgana ba sai da ta ga har hu u da rabi ba ta fito ba, sai ga Mariya ta biyo mata amman sai Walida ta gyara kwanciya ta ce ba za ta je ba. Inna na kofar akinta tana tanka en garin tuwo ta ga fitowar Mariya cikin mamaki ta ce"Ya naga za ki tafi? Ina abokiyar tafiyar taki? Mariya ta ce"Ta ce yau ba za ta je ba Inna" Inna Meri ta ce"Ubanta za ta zauna ta min acikin gidan? Tsaya ta zata je dolenta ma." Ta ijiye rariyan hanunta ta shiga aki Walida na kwance a kan gadon Inna Meri sai dai ta ji dundu a gadon bayanta a zabure ta mike ai sai taga Inna Meri a kanta tana hararanta. Da sauri ta mike zaune kafin ta yi mgana Inna Meri ta ce" Za ki ta shi ki shirya ku tafi ko sai na yi miki dukan tsiya? Ai walida na jin haka ta sauko daga kan gado jikinta na rawa sanin halin Inna In Baban Inna ya ata mata rai to wallahi akan duk wanda ta samu take hucewa sulum sulum ta zura dogon hijabin mai ruwan kasa kalan na Islamiyan ta auki jakarta ta fice har ta kai falo Inna Meri ta biyota tana Fa in"Ina wayata? Sai ga Walida ta zaro ta daga cikin jakarta Inna ta warce a hannunta tana fa in"Za ki sani ne, je ki dawo sai ki yi mu su bayani." Gaban walida na dukan uku uku ta saka takalmi su ka fice daga gidan ita da Mariya inna Meri ta bi ta da kyaci nan kofar aki ta ijiye wayar ta cigaba da aikinta aiko saurayin walida na ta kira tunda Inna ta dau a ya ji muryanta babba ya kashe bai kara kira ba cikin gatsine Inna Meri ta ce" an batar uba kawai." Tana ka a miya Baba Danjuma ya shigo a wahale daga gani sun wahala da Sauri Inna ta ijiye abunda ta ke yi taje ta auko masa tabarma ya zauna sannan ta auko masa ruwa mai sanyi sai da ya sha ya samu natsuwa sannan ya kishingi a yana fa in" Meri yau mun sha wahala'" Nan fa ya shiga ba ta labarin cewa can cikin wani kauye ne in da mota ba ta shiga da kafa ma suka karisa sannan wajen dawowa ma ba su samu mota ba, kai dai sun wahala kwarai. Inna Meri ta jinjina kai kafin ta ce" Wai Allah na sannu Mallam ko a sama maka ruwan wanka ka watsa ko kaji sanyi sanyi? Da sauri ya ce"Da kin kyauta kuwa Meri na gode Allah ya yi miki albarka." Da hanzari ko ta mike ta zari botiki nab kofar akinta ta nufi babban robanta na ruwa ta zuba masa ta kai masa makewayi sannnan ya tashi ya shiga wankan amman kafin ya shiga sai da yace ta je akinsa ta auko masa wasu kayan da zai sauya. To daman akinsa nasa na bangaren Magajiya ne ta ko sha mgana tunda ta ga ta bu akin ta shiga ta fito da kaya Magajiya ta saki shewa kafin ta ce"Aikin banza ko nace aikin bur in ji tusa wani dare ne jemage bai gani ba? Allah na tuba ai ni Magajiya na gama si e romon si en kwano na bar miki Meri" Duk ta na jinta sai ba ta tanka ta ba, sai da ta auko kayan ta zo za ta wuce sannan ta kara cewa"An girma amman ba za a bar Jaraba ba, Allah dai ya sauwake" Ita sai abun ma ya ba ta dariya to ita a tunaninta wani abu ne ya faru? A shekarun nan na magajiya in ba ta yi hankali ba, to kila ita da hankali har abada, kwanaki nan daman sai faman sakin mata habaici take yi tunda Saddiqu ya zo daga Lagso ya yi ta barin ku i Magajiya ta yi ta zagin Inna Meri da nuna itama yayanta na da shi yanzu shima abunda ya dawo da shi neman aure ne yarinyar da ya ke so ne iyayenta su kace sun tashi aurar da ita su Baba Sani jiki na rawa sun je amman waliyan yarinya sun ce a ba su lokaci za su neme su. Ko kafin ya fito daga wanka har ta ha a masa abincinsa waje aya kaya ya sauya sai ya rama sallar la'asar din da ta su uce masam Dambun zogale walida ta yi da rana shi ya zauna ya na ci ita kuma Inna na kwashe tuwo suna hira Jefi jefi cikin hiran ne Inna Meri ta kallesa kafin ta ce"Mallam anka ya isheni da fitina wallahi nagaji." Kai tsaye ya ce"Wanne cikin an nawa? Inna Meri ta ce" Kafi ni sanin shi fitinannen ciki mana." ar dariya ya yi kafin ya ce" Allah Sarki ai dukkansu an albarka ne, yanzu dai fa amin me baban naki ya yi ne? Inna Meri na aikinta tana gaya masa wayarsu da Hajiya, Baba Danjuma ya yi dariya kafin ya ce"Topha babban mgana.." Inna Meri tace"Uhm wallahi na rasa abun cewa ma