← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 191 OF 208

Sashe 191

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dawo da ita gidan su wajen mamanta tun bayan sallamota daga asibiti ba ma za'a yi taron suna ba saboda yanayin rayuwar da ake ciki, bayan sun baro gidan suna hanya ya yi mata surutun ba ta ga yadda jaririyar ta mata kyau ba kamar ce ta ta ce, sannan ya koma mata magiyan me ta ke so ya biya ya siya mata. Sai a lokacin ta kalle shi kafin ta ce" Abu aya nake so shi ne ka yaleni." Daga haka ta kauda kanta muryanta kamar za ta yi kuka dole ya kyaleta amman tsakani ga Allah ya gaji da wannan horon bayan fagen. Fiye da sati biyu suna cikin wannan rayuwar, ya gaji ya fara bin ta da ban hakurin ta yafe masa ,ita kuma ta ce ta yafe kawai dai ta kasa sakin jiki ne tunda har shi bai yarda da ita ba, in ta tuna haka har kuka ta ke yi saboda bakin ciki. Tana mamakin yanayin cikinta baya sakata amai sai dai tashin zuciya wani lokacin, ita dai sai dai kasala da jiri sai zazzabin dare ba ta kuma zaban abinci amman dai ta na cin goro, saboda sau in tashin zuciya ta na iya kula da kanta da gidan aikin ma za ta koma ranar Monday tun da ta samu sau Ranar da Allah ya nufi su shirya. Ranar asabar ne Walida da Mariya a gidan suka yini suka girka shinkafa da miyar kifi. Kifin ma tun Tsaraban Inna ne na Argungu, ba ta ma sani ba suka saka shi a miyar sai kuma ta yi mata da i taci sosai a daran ma ta ara ci ta dora da maltina ta kwanta ai misalin sha biyun dare cikinta ya hana ta barci sai tashin zuciya, haka ta rarrafa ta shiga Tiolet ta rika kwara amai kamar za ta amayar da hanjin cikinta. Da jan jiki ta dawo gefen gado ta auki waya ta kira Aji, daman bai yi barci ba yana duba wani tsare tsaren wassanin su na gaba me ya ga kiranta, kuma sai da gabansa ya fa i ya san ba lafiya. Sanda ya zo har ta fara galabaita tana son yin aman amman ba komai a cikinta, ganin yanayinta ya sa kawai ya saka mata hijabi ya taimakamata suka fita falo,da gudu ya auko key in mota jallabiyansa a juye ya saka ya rike Mimi zuwa wajen mota megadi ya taso ga gudu ya na jera mata sannu, kawai sai Mansoor yace a bu e masa get. Wani asibitin ku i ya kaita mafi kusa, suna zuwa a ka kar e ta saboda emergency ne Mimi ta sha wahala duka sai da ta amayar da abin da ke cikinta sannan a ka mata allurai bayan an saka mata drip anan asibitin suka kwama ita an ba ta gado shi kuma ya na zaune da ita,.Sai bayan ya je sallar asuba ne ya dawo ya kira Inna ya fa a mata hankali tashe ta ce gata nan zuwa, likitan da ya kar e su ya kira shi ya yi masa bayani Mimi ta daina cin kifi domin cikin ta ba ya son shi, ta na daina cin wani abun da cikinta ba ya so. Allah ya sa abun ya zo da sau i Inna Meri ta zo ta yini da ita a ranar sai Hajiya da Mansoor in ya je ya gaya mata, kwananta viyu a ka sallameta ta koma gida duka yan'uwanta sun kirata a waya kuma kowa ya san ta na da ciki Khadi har da mata tsiyan cewa Oho su Mimi da ciki an kusa zama uwa. Mommy ba ta zo ba amman suna mgana ta waya, Mama da Anty har Daddy ya zo gida dubata shi ya ce a bar mata Baaba Uwani ta zauna da ita Hajiya ta ce itama me ta ke yi a gidan? Mansoor kuma ya ce har Hajiyan don Allah su zauna tunda Walida ba ta da lokaci yanzu. Yadikko ma ta zo ita da iyalanta su Anty Amina da su Bintu ma duk sun zo. Su jummai da su Zuwaira har Maeesha da matar Auwalu. Magajiya da su gaje sun zo duba ta, kuma taji da i kwarai yadda suka nuna mata kulawa shima kanshi gogan rawan jiki kawai yake yi, Nasir da su Makama duk sun zo dubata Rukayyan kusan kullum tana gidan. Zaman Hajiya da Baaba Uwani ya daidai ta Mimi da Aji, tunda dole ta bar musu akin ta koma akin Aji tana kwana kuma suna gidan ai ba za ta masa horon da ta saba a gabansu sai ta ke nuna komai lafiya sai sun shiga akin ta yi masa gum Ranar dai ya gaji cikin dare ya mi e ya kunna hasken akin ya ta da Mimi, ta tashi tana sosa idanuwanta cikin sanyin ta ta ce"Me ya faru? Gurfana ya yi daga saman gadon a gabanta ya ba ta kanshi lokaci aya yana da in"Gani ki yi min duk abin da kike ganin za ki wuce, na gaji Fatima kina horani wlh na tuba ba zan ara ba." Ya fa a kamar zai yi kuka idanuwansa sun kala yana bukatar matarsa amman sama da wata aya Mimi na masa kisan munmu Kallonsa ta yi kafin ta kauda kai tana kokarin komawa ta kwanta da sauri ya rikota ya jawota jikinsa ya kamkameta ya na Fa in"Kin ce kin yafe min amman ki duba abin da kike yi min? Ba ki yi min mgana ba na ganin dariyan ki. Ni fa bayan ganin ki a tare da ni ina bukatar ganin ki cikin farincikin ba na jin da in ganin ki haka don Allahi ki yi hakuri mu koma kamar baya." Mimi kwallah suka cika mata ido cikin rawan murya ta ce"Me zan maka? Na kasa manta maganganunka ne Aji, da bakin ka kace tabbaci gare ka a kaina ba zargi ba ne. Ni wai na ke cin amanarka? Ni wai haba don Allah ban yi lalacewa tun ban da aure ba sai da na yi aure zan lalace? Me ya sa ba ka za kamin uziri ba? Ni ba ka yarda da ni ba? Kai ne fa ka ta a sanina a mace amma har kake so ka saka zargi a zaman aure Saboda ina sonka ina kiyayema duka dokokinka komai ka ce in yi shi nake yi saboda mu zauna lafiya amman duk ban tsira ba, ka ce wai kana da tabbacin ina cin amanarka.. Aji ni ce fa Mimin ka ni? Abunda ya fi min ba in ciki shi ne yadda ba ka yarda da ni ba, sannan kana mijina wanda ya fi kowa sanina ka kasa iya shaidata to waye zai yi shaida ta?. Tana mgana ta na kuka saboda abun in ta tuna sukan ranta yake yi, Aji gaba aya jikinsa ya yi sanyi haka ya kara kamkame Mimi shima kamar zai yi kuka yana fa in" Wlh sharrin she an ne da kuma sonki, ina sonki Fatima shi ya sa nake kishin ki." Cikin kuka ta ce"In kana kishi na sai ka bari ka kasa yarda da ni? Haba don Allah shekara nawa muna tare? Ka rika sarrafa zucyarka sannan ka rage kishin ka, ka tuna sanda ka auke ranga ranga zuwa asibiti ka manta likitan namiji ne ya dubani a lokacin ba ka damu ba saboda lafiyata kake nema, To haka za ka rika hakuri da rayuwa dole zan fita wasu za su ganni kai ma za ka fita za ka ga wasu abunda kawai za ka saka a ranka shine ka yarda da ni, ko bayan ba idanuwanka ni mai tsare maka amana ne amman wlh abunda ka yi min yasa min bakinciki a zuciyata sannan kuma yasa na rage ganin ka yadda nake ganin kaa cikin Idanuwana." Haka ta fa a tana kuka, Aji ya ru yana fa in"Don Allah kada ki daina sona Fatima, in kika gujeni wa zai so ni? Zan gyara halina zan ri a sarrafa zuciyata da kishina amman kada abunda ya faru ya sa ki ji kin tsaneni." Mimi ba mgana sai kuka shi kuma ya na ta ban hakuri kamar zai mata kuka. Tabbas ya yi nadama kuma ba zai yarda ya ara aikata abin da ya aikata ba. Itama tana son mijinta duk da wasu hallayan na shi ba su da kyau.Sai dai ai daman an adam tara yake bai cika goma ba, a komai ba za ka ce ka samu abu ari bisa ari ba. Ko 50% ka samu sai ka yi hakuri da shi, tunda har ya Ffhimci bai kyauta ba ta na da tabbacin gaba ba zai kara yarda ya aikata abin da ya aikata a baya ba. Sai ta rumgumeshi cikin shesshekan kuka ta ce" Shi mgana zarar bunu ce, kuma wata mganar ta fi kaifin takobo kaifi, in ka caka ma mutum zata huda cikinsa har ta fita ta waje, ka daina barin ranka na aci kana fa in mganganu mara kyau a kan abin da ka ke so, wata rana za ka cutar da ni cutar da bazan iya yafe maka ba." "In sha Allahu ba zan kara ba." Da haka ta yafe masa ta kuma yi alkwarin manta abin da ya faru amman ta ce ba yanzu ba sai a hankali za ta iya manta abin da ya faru. Shike nan ma'auranta suka shirya, amman duk da haka Mimi ba ta sakin jiki da Aji, in ta tuna kalamansa a kanta sai gwiwanta ta yi sanyi shi dai ko da yaushe ban hakuri ne. Satin Hajiya biyu suka koma gida tunda Jikin na Mimi ya yi kwari, ta na yin amai amman ba sosai ba. Kasala ne dai da jiwa shima ba sosai ba. Sai zazzabin dare shima ya yi sauki sai dai ta yi fari fayau ta kuma rame. Sama da wata aya sannan Mimi ta koma aiki. Gogan ya yi sanyi yanzu yana gani za ta saka mayafi ta fita sai dai ya kauda kai tunda ya yi al warin yarda da matarsa kafin kishin sa a gaba, itama kuma tana yi domin ta ga ko da gasken ya daina abunda yake yi. Da gangan take saka abaya ta sha rolling ta wuce, baya mgana amman dai ya kan ce" Abaya
Chapter 191 · 0% Book details