Sashe 200
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da matarsa da Ummi ai ko shima ya yi mamakin girman Ummi yana dariya ya ce yar lukuta. Ranar a gida Mimi ta kwana ana sabunta amarci sai can rana ya kawota gidan wanzamai inda ake sha'anin bikin,Inna ta bashi tsarabanta ya kar a da godiya a ranar ma da yamma jallabiyan ya saka haka kuma ya ga Mu'azzam ma ya saka naahi, sai suka kalli juna suna mirmishi suma suna ta shiryen shiryen wajen daurin aure a masallacim kusa da su ne amman sun saka an share kofar gida an gyara shi saboda mutane. Har saddiqu da shi ake komai ya ga ba sarki sai Allah ya saduda. Yaya Mansoor sama Yaya Mu'azzam domin ya fahinci in ya yi tawaye ba riba hakama Magajiya ta fa a masa. Gida cike da baki ana ta hada hada Matan sun yi ankon Atamfa na biki,sannan ko walima ba'a yi ba sai ranar lahadi a gidan Amarya. Mariya a gidan Bintu za su yi zaman su tunda kusa ne sai ya kasance su Mimi duk suna can har da su Nafisa da Bibi matar Ahmad dai sun koma kaduna. Har da Yan'uwansu Hibba duka da su ake sha'anin annen mahaifansu Yaya Amina kuwa, daman duk wani sha'ani da su keyin shi kuma duk saboda Inna Meri ne a ka zo a ka yi ma Magajiya karan. Ana jibi bikin nan suka kawo lefe akwati shidda kuma da kayansu ma sha Allah daidai karfin talaka mai nema. Ranar asabar aka tashi da shagalin biki sha daya na safe aka aura auren Mariya da angon ta Aminu, Baba anlami me waliyin Amarya anan wajen ya ce ya wakilta Aji ya yi ma Mariya wallici shi ya ba da auranta ga waliyan Aliyu sannan bayan aurin auran ana rawan jikin gaisawa da shi wanda bai ma san shi ba an gaya masa sunan shi. Ango da tawagansa sun sha fararen kaya suma su Mu'azzan kowa da kalan kayanshi amman sun saka babban riga har da Saddiqu da ya saka ta bikin shi, Baba ma sabuwa Mu'azzam ya inka masa da Sabon takalmi a cikin gida kuwa ana ta hada hada an dafa ahinkafa da alala sannan an yi waina Amarya da aawayenta sun yi firaidi rice din shinkafa da Alala sai nama da Mimi ta bada ku i aka siya kilo uku saboda baki Walida yan jami'an an sha kwallya tunda sun yi makeup, nan aka bar wasu awayen su Mimi suka tafi da Amarya can gidan ana ta hotuna duk rashin son hoton Aji su Yaya Amina suka rike shi sai da ya shiga amman ya na rike da Ummi a kafa ansa ayan hannun kuma ya na rike da Junior da damam an gidanshi ne. Ammi dai tana wajen uwarta Mu'azzam dai daman ba shi da wani nane ma yara. Gaba aya ahalin gidan Wanzamai a ka ha u a ka yi family picture su Gaje da Harira da yayansu maza da mata da su Baba anlami Inna meri da Magajiya da Baba Danjuma da su Aji da yayansu da matansu gaba aya a ka dauki joton kowa ya gansu sai ya ji sun ba shi sha'awa babu abunda yafi ha in kai da Bayan La'asar Mansoor da Auwalu suka dauki amarya zuwa akinta daga umarmin Baba anjuma, tare da Inna su ka je da wata anwar Magajiya sauran daga baya su ka zo bayan ango ya kawo motoci, Mariya na ta kuka domin yayyenta sun mata fa a ta zauna lafiya kowaani aure da ta gani yanzu na da shi kalubalen gwara ma ta zauna lafiya, Walida ne da sauran awaye suka kwana a gidan sauran kuma suka koma gidajemsu suka kwana su Hibba dai a gidan Inna daman suke kwana Mimi kuma Aji ba barinta daman zai yi ba. Sai washegari suka koma kai kayan da ake ba ma dangin ango bayan sun auki Mariya zuwa gidan iyayen mijin, su Mimi da su Yaya Amina sai Inna da su Gaje,an gama komai cikin girma da arziki sun mika amanarta ga dangin mijinta suka baro ta acan tana kuka. Wasu suka sauka gidan Magajiya wasu kuma gidan Inna irin su Mimi da sai dare Mansoor ya zo suka koma gida. Wasahegari litini Mimi ta tafi aiki shi kuma sai ya leka Camp in su na Gombe United su ka gaggaisa da su Kb suna ta cewa sun yi kewarsa ya ga pele sosai daman yake da kokari shima auransa ya kusa sun zauna da Caach suna ta hira kan sabon horon da yake samu anan Abuja sai can rana ya baro wajen ya isa ma'aikatansu Mimi ya aukota suka dawo gida. Ranar talata ya bi jirgi ya koma Abuja Mu'azzam kuma washegari shima suka koma kano, amman ba su tafi sai da suka sallami Safiya da ku in mota za ta koma An yi cincin da dublan na Amarya an yi kuma na rabo an dibar ma su Mu'azzam sai Mansoor da Mimi ta ha a masa cikin kayan snkas din ta yi masa , har da dambun kaza da miya ta yi masa saboda ya gaya mata wancan tafiyan ba karamin wahala ya yi ba, shiyasa wannan karon ta shirya ma tafiyar nashi sannan sun yi mgana da Mommy ta ce za tari a ba ma direba abinci da lambar wayarsa sai ya ri a kai masa can Camp in su. Amman kuma ta san halin Aji ba lalle ya amince ba amman duk da haka sai ta ce za ta gaya masa, ta na ko yi masa mgana ya ce a'a ba ya son ya saka Mommy wahala da awaniya. *Janafty* *INZB3020* Duk da yace ba ya son saka Mommy awaniya amman duk weekend Asma'u kan yi abinci a saka direba ya kai masa har Camp in su fitowa kawai ya ke yi ya kar a. Daman abinci ya fi ba shi wahala saboda Camp in Abuja ba aya yake da Camp insu na Gombe karami ba wannan babban waje ne da ya tattara manyan yan wasan kwallo na asa gaba aya duk wanda ka gani a cikin wannan kungiyar fitattace ne sannan ya kwarewarsa ce ta kaisa. Shi ya sa ko yanayin traning in su ba aya ba ne, duk da akwai manyan an wasa da asa ta jima da sheda fuskarsa dama duniya gaba aya wasu yanzu suke cin zarafin su wasu kuma suna cin zarafin nasu har kuma wa'adin da za su yi ritaya ya cimma musu shi ya sa a ka auki ire iren su Aji masu okari domin maye gurbin su. A baya ba shi da burin zama a wani gari face jiharsa saboda Inna da kuma yanzu ya zama uba kuma mai mata, ko a yanzu da ya samu sauyin wajen aiki bai ji ko a ranshi wata rana zamansu gaba aya zai dawo Abuja ba, ya saka a ranshi duk matakin da zai taka a rayuwa jihar Gomb uwace a gare shi ba da Mama. Ya kan yi sama da wata a Abuja wani lokacin ma sai ya raba wani watan ya ke zuwa Gombe ya ga Mimi da Ummi da Inna tare da sauran an'uwansa sannan in ya dawo in ya da e ne kwana hu u zai koma Shi ya sa sai zaman ka aicin ya yi ma Mimi yawa sai ta ke ro on shi bayan ta tashi daga wajen aiki ko ta biya gidan Hajiya ko wajen Inna to shima in ba kullum ba ranar da bai ga dama ba sai ya ce ta koma gidanta ta zauna in ta ce ba kowa sai yace ga Ummi nan, kada ta damu ita uwace yanzu kuma yanzu suka fara gina rayuwarsu a kwai lukatan da za su yi nesa da juna ba domin suna so ba, sai domin neman halas da kuma inganta zamantakewarsu ta nan gaba, ta maaa uzuri sanin halin shi ya na da Kulafacin gida amman tunda ta ga Aji ya hakura da zaman Gombe ya koma Abuja ta san ya arbi canji da Ubangiji ya yi masa da hannaye bibbiyu. Wani lokacin sai su yini ba su yi mgana ba, ya fi kiranta da asuba ko can wajen sha biyun dare lukatan da ya ke samun sukuni kenan itama sanin ba shi da lokaci ba ta takura masa da kira sai in har tana da mgana da shi mai muhimmanci da ta shafeta ko ta shafi Ummi ko inna, sai ta kira shi in ya zo ya ga kiranta zai kirata daga baya. Hakan ce ta faru yau ma tunda tun kwanaki a wajen aiki sun yi mgana da Manaja kan wani sabon shiri da Ma'aikatansu za ta irkira shirin kuma na mata ne, mai suna matsalolin mu Ayau shirin da zai ri a gayyato mata dabam dabam domin jin irin matsaloli da challages in da suka fuskanta a rayuwa kuma ana so ita ta kasance presenter ta shirin gaba aya ba, ba ta amsa ba sanin halin mijinta ta ce sai sun yi mgana da shi, to ba ta samu sun yi mgana ba saboda karancin lokaci, yau in ma ba su yi mgana a daran ba ta kira shi wayarsa a kashe sai da Asuba ya kirata ya ce sun shiga Meeting ne shi ya sa ya kashe wayarsa sannan ba gama da wuri ba shiyasa bai kirata ba a tunaninshi ta yi barci kada ya tashe ta ita da Ummi. Bayan gaisuwan da tambayar yadda take ita da Ummi su ka an yi zantukan soyayyarsu na kewar da su ka yi da juna. Sannan Mimi ta shigar masa da maganar Manaja nan ta ke Aji ya fara fa a ta in da ya ke shiga ba ta nan ya ke fita ba,Mimi ta jawo Ummi da ke barci ta rumgumeta a sanyaye ta ce" Kayi hakuri Baban Ummi." Haka kawai ta ke fa a amman ya ma i sauraranta sai faman fa a yake yi yana fa in" Ba fa mganar hakuri ba ne Fatima renin wayan ne na ga ya yi yawa. Me ya sa sai ke? Ke ka ai ce ma'ikaciya mace a wannan wajen na ku? Haba sai ace ke dole fuskarki ce za ta ri a yawo a akwatin Talabijin in kowani gida? Haba ba ta yuyuwa kina matata