← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 208

Sashe 141

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tunaninta yanzu ba da ba ne, Mimi na da aure ita ba ta san ta na yawan kiranta saboda wannan mara mutumcin mijin nata. Ranar tana wajen aiki Na Misau na zencen Mimin sai ta aga waya ta kirata amman Sai ba ta same ta a waya ba sai ta yi tunanin in ta tashi daga wajen aiki za ta biya ta dubata, la'asar ta baro ma'aikantarsu ta hau adaidaita zuwa Gidan Wanzamai a kofar gida ta ha u da Baba Danjuma a lokacin su ka gaisa, shi kuma bai yi mata wani bayani ba sai da ta shiga gidan, abin da ya bata tsoro shi ne ganin wata a akin Mimi, Saboda lokacin da ta shigo Inna na akinta, Walida kuma ta tafi makarantar Islamiya. Shi ya sa ta shiga akin Mimin kai tsaye sai kawai ta ga komai ya sauya har da mai akin ma gaba aya. Cikin mamaki ta ke kallon Maaesha kafin ta kara komawa baya a tunaninta ko ta yi makuwan shashen ne. Sai dai ta ara ganin tabbas nan ne. Cikin mamaki ta ce"Ko na yi makuwa ne? Ba nan ne akin Mimi matar Mansoor ba? Maeesha na zaune ta na cin Aya ta yi waata yar dariya kafin ta ce" A da ba, amman yanzu ya zama akin Maeesha matar Saddiqu." Rukky ta yi shuru tana kallon Maeesha cikin tarin mamaki, amman ba ta sake mgana ba gabanta na fa uwa ta fita daga akin rike da wayarta tana ara kiran layin Mimi sai kuma ta shiga dalilin da ya sa ko arayin dakin Inna Meri bata kallah ba. Allah ya taimake tana fita sai ta ga mai adaidaitan da ya kawo ta bai tafi ba ya tsaya mgana ta waya sai kawai ta fa a ciki dai dai lokacin da Mimi ta aga kiran Rukky. "Baby Ru ayya.." Mimi ta fa a cikin sanyin murya, Ita kuma Rukky Kamar zuciyar ta za ta fito waje ta ce"Fatima kina ina ne? Na zo gidan mijin ki a akin ki na ga wata, ko kin ta shi ne ban sani ba? Mimi ta yi dariya daga bangarenta kafin ta ce"Eh! Ina gidan Hajiya ki zo ki same ni." Cikin fa uwan Gaba Rukky ta ce"Mimi me ya faru ne? gaba na fa uwa." "ke dai ki zo, ba komai sai alheri." Daga haka ta katse wayar, Rukky gaba aya sai da jikinta ya yi sanyi, mai adaidatan na mganar Hajiya komawa za mu yi? Tace Eh amman yanzu anguwan Hashidu Estate za su je, nan da nan ya juya kan adaidata suka nufi gidan su Hajiya. A Gaggauce R ukky ta shigo, gidan Hajiya na falo Baaba Uwani na kitse mata kanta da ya cika da farin ga shi. Tsabar ma ru ewa da gaisuwan da tambayan Mimi duk a lokaci aya ta yi su, Hajiya ta ce tana ciki ta shiga ta same ta ai ko har da gudunta ta wuce Hajiya da Baaba Uwani suka bi ta da Kallo Hajiya ta girgiza kanta kafin ta ce"Ina ga ta ji labarin Binta na gida" Baaba Uwani ta ce"Hajiya yanzu ba za'a gyara lamarin nan ba? Hajiya ta ce" To Hamza ne kan batun ya ce na cire bakina, sai in har Mijin Binta ya tako da kansa sannan za'a yi maganar gyara." Baaba Uwani ta yi shuru kafin ta ce" kuma bai zo ba ko? Ni fa kamar sau aya ma na ta a ganinsa tun bayan auran nan." Hajiya ta jinjina kai kafin ta ce"Zuwan na shi bai wuce ayan ai zuwa biyun." Baaba Uwani na son cigaba da Magana amman Hajiya ta kauda mganar ta fara mata zencen mutanen can garin su na Akko sai su saki hiran Binta suka kama ta mutanen gida. Mimi na kwance ta na latsa wayarta Rukky ta fa akin cikin damuwa. Kamar ta fa a kanta haka ta fa a saman gado tana fa in" Kar dai ki fa a min kun rabu ne? Mimi ta mi e da sauri ta na fa in" Rukky me ye haka? Kin bani tsoro wlh." Ba ta damu ba sai ma gyara zama da ta yi ta na fa in" Don Allah ki gayamin abin da ke faruwa ko zan samu natsuwa." Mimi ta yi shuru kafin ta ce" Eh mun rabu amman ba mu rabu ba." "Ban gane ba? Rukky ta tambaya cikin zullumi. Sai Mimi ta gyara zama tana fa in"Rukky labarin na da tsawo amman takaice shi ne na dawo gida ne. "Saboda mene? Ta tambaya tana mai tsare Mimi da ido, ita kuma ta kauda kanta saboda Idanuwanta sun fara tallah kwalla, babban ba in cikinta yadda ta fahimci ba ta da wata faraja a wajen Aji kwananta takwas da dawowa Gida amman ko kiran ta bai yi ba, ba Sa o ba zuwa kenan ya nuna ma kowa cewa bai Damu ba da zamanta da tafiyarta duk aya ne a wajensa. Kawai sai ta saka ma Rukky kuka, ita kuma baki bu e take kallonta kafin ta ce"Mimi me ya faru ne? Ki bar kukan nan ki yi min bayani domin Allah." ewa Mimi ta yi zuwa gaban window in da ke akin lokaci aya tana fa in" Ru ayya ban ta a tunanin hukuncin da na yanke ma rayuwata na auran Aji kuskure ba ne sai yanzu, na yi gaggawa me ya sa bayan na ciza ban tsaya na hura ba? Rukky Aji ba ya sona iya wancan Soyayya na yarinta ta gushe a zuciyarsa ya aure ne kamar zai rama abin da Abi ya yi masa a shekarun baya, Rukky Aji baya sona tunda na aure shi bai ta a kama hannuna da gangan ba sai dai bisa Kuskure." Ta yi shuru ta na sauke numfashi Saboda kuka ne ke cin zuciyarta. Rukky ta yi kasa e tana sauraran Mimi cikin mamaki ta ce" What? Hoto kike a wajen sa? Mimi ta Juyo tana fuskantar Rukky kafin ta koma ta zauma kusa da ita, ita ka ai ce aminiyarta sai ta ji tana son gayamata abin da ya faru tun farko har zuwa karshe.. Sai ta samu kanta da fara ba ma Rukky labarin auran da Aji har zuwa abin da ya Faru ta dawo gida amman ta sakaya yadda ya ke cin zarafin iyayenta ta dai nuna mata ba shi da zuciya mai kyau tunda bai san afuwa da yafiya ba sannan ya na amfani da abin da ya faru yana mu'amalanta da shi. Cikin Kuka Mimi ta ce"Rukky da kansa ya ce na tafi din ya nuna bai damu ba, yau kwana na takwas a gidan nan bai kirani ba sannan bai zo ba, annensa ma da suke zuwa da abokansa wah sun yi ne domin suna son aure da shi ba saboda shi ba. Na rasa wani irin miji nake aure? Wlh Ajj ya sauya a baya ba haka yake ba Rukky, ina son mijina amman ya zama dole na yi nesa da shi ko zai fahimci Muhimmancina a rayuwarsa." Ta arishe fa a tana gunjin kuka, Tausayinta ya kama Rukky sai ta kama ta Rumgume tana bubbuga bayanta alamun lallashi, har sai da ta yi shuru sannan ta dago kanta suna fuskantar Juna Rukky ta fara fa in" Na ji da in yadda kika nuna masa ke ma macece, sannan na ji da i da Daddy ya goya miki baya sannan na ji da in yadda baki saurari annensa da abokansa ba, Ire iren mijin ki Fatima yan burauba ne hanyar Sau i ba ta bille musu sai an biyo musu ta bayan gida, Na fahinci wlh arya yake yi yana sonki in baya sonki ba wata Hajiya ko Mommy da yake gani da mitumcin da saboda su zai aure ki. Sai dai tsabar bakar zuciya da Tunanin banza ya sa yake ta gasa miki aya a hannu kuma ya yi anfanin da cewa kina son shi duk kashin da zai ya a miki ba za ki iya aga kai ba, To Wlh ya yi karya har shi ya isa? Mimin ce zai yi ma wannan cin zarafin? Kinga share hawayen ki na rantse da wanda raina ke hannunsa sai Aji ya zama a tafin hannun ki, sai Aji ya nuna ma duniya kece mace mafi daraja a wajensa, Wlh tallahi sai kin rama kwatakwacin abin da ya yi miki kila ma fiye da wanda ya yi miki. Sai ya wahala sai ya raina kansa sai ya yi laushi sai ya yi la'asar ba tun farko ya ki sharen masallaci ba, to ai yanzu ina baki tabbacin zai yi na kasuwa sai mun saka shi ya aatan da kanshi in da yake tunanin ya fi karfi sai Aji ya zo ya duka yana miki magiyan da ro on ki dawo cikin rayuwarsa ke kuma a lokacin kike da damar rama duk abin da ya yi miki har ma fiye da hakan." Har Rukky ta gama maganarta kallon ba ki da hankali Mimi take yi mata. Kafin ta girgiza kanta lokaci aya tana fa in" Ba ki da hankali Rukky Ajin ne duk zai zauna na yi masa haka? Ke wai duk ba ki saurari labarin da na ba ki ba ne? Nan matar aninsa Hibba ba abin da ba ta ce na yi ba amman daga karshe me na samu? Bayan cin mutumci da wula anci.? Rukky ta bigi Kafa an Mimi lokaci aya tana na fa in" ke dilla gafara can, kina wani abu kamar ba mace ba, wa ya gaya miki ba abin da kika samu? Kin samu mana ke ce ba ki fahinta ba amman tabbas Aji na sonki so kuma mai tsananin da shima ba zai iya rayuwa ba sai dake. To tunda ya yi kuskuran bari mu ka sani ya shiga uku, Ajin banza ajin wofi, ai sai dai ya cigaba da amsa wannan sunan a waje amman a gabanki sai dai shi ya zama Ajin waje ke ki zama ajin cikin gida, na yi rantsuwa ko Kaffara ba zan yi ba yana can cikin tunaninki ya tsaya ne yana tunanin za ki neme sa ku daidaita, yana tunanin kina son shi saboda haka ba za ki iya dogon fushi da shi ba to ya yi kuskure, tabbas sai kin rama tabbas
Chapter 141 · 0% Book details