← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 177 OF 208

Sashe 177

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya yi turjiyan ne ya amince shikenan amma yanzu tsarinsa ya rushe, zuwan shi kwami da Bauchi ba zai samu ba sannan Mimi ma ba zai hana ta tafiya Abuja tunda ya riga ya yi mata al wari kuma ya san ta sanar da Mommy, sai dai yanzu su tafi tare shi ya je ya yi abin da ya kaisa ita kuma ta je gidansu ta zauna in ya gama abib da ya kai sa sai su dawo tare, ga kuma babbar salla ta arato sai dai su aga tafiyarsu Kwami zuwa bayan sallah. Gajiya ya yi da zama ya tashi ya kunna talabijin a tashar kwallon afa daman su yake kallo ko tasoshin wa'azi Mimi kuma daman kallo bai dame ta ba barta da barci sai kuma waya,wayar ma ba sosai ta dame ta ba. Bai san fitowarta ba sai ji kawai ya yi ta sa alo hannayenta daga bayansa zuwa wuyansa lokaci aya tana ora kanta a saman kansa cikin yar shagwa a ta ce"Shi ne ka tashi ni ba ka tashe ni ba ko? Ta fa a ta na sosa kirjinsa da ayan hannunta ayan hannun nata kuma ta fara sosa masa kunninsa guda aya, juyowa ya yi bayan ya ri e mata duka hannayenta sannan ya zagayo da ita har gabansa ya zaunar da ita kan cinyarsa suna masu kallon juna ya ce"Kina ta sharan barci duk kin bugemin jiki, kina ta munshari, ga shi kin saki baki galala da miyan barci." Ya fa a lokaci aya har ya na kauda kansa yana ar dariya. Rufe baki ta yi tana kallonshi cikin mamaki kafin ta ce"Ni ne ke minshari da miyan barci? Ta fa a har ta na zaro ido cikin tsoro domin har ga Allah ta auka da gaske ne. Rumgumeta ya yi yana fa in" E, mana, ban ta a fa a miki ba ne, amman kada ki damu ke na ke so ba zan damu da minsharinki da miyan barcin ki ba" Yadda ya arishe maganar da dariya ne ya sa ta gane abin da ya ke nufi, da sauri ta saka hannu ta mintsine shi a cikinsa har sau biyu kuma mintsinin da zafi da ya sa dole ya saketa ya yi gefe yana ra in"Mimi ba na son mugunta fa daga fa in gaskiya? Mikewa ta yi daga kan cinyarsa ta ri e kugu daga ita sai rgar barci fara mai shara shara iyakarta gwiwamta sannan surar jikinta duka yana bu e ne gashin kanta ma yana aure ne kanta ba hula ba ankwali. "Waye mai miyan barci da minshari? Haka ta fa a ta na zare masa ido har da aga hannu kamar za ta kai masa duka ya saka hqnnuwansa ya kare kansa yana fa in" Allah ya baki hakuri Inna Fatima." Ya fa a yana yar dariya sai kawai ta ja cution in kujera ta mara dukanshi da shi ya na karewa da hannunshi yana dariya bai hana ta ba sai da ta gaji ta bari shi kuma daga kwancen ya saka hqnnu ya jawo ta ta fa o jikinsa ya rumgumeta ita kuma tana neman wace kanta lokaci aya tana fa in" Ina miyan barci ko? Ya na yar dariya ya ce"Na tuba na janye mganata ina ga ni ne me miyan barcin da minshari ban sani ba" Hararansa ta yi kafin ta ce"Za ka ma sani ne." Ta fa a ta na kokarin tashi ya sake ri eta ya nanna eta a cikin jikimsa yana mata ra a a kunne ba ta san lokacin da ta yi dariya ba. Bai bari ba sai ya fara yi mata cakulkuli ta fara dariya kamar za ta shi e tana fa in" Cikina na ciwo don Allah ka bari." Sai da ya ga tana hawaye sannan ya kyaleta ya koma ya na sumbatan bakinta. Daga nan suka rike kan juna suna sumbatar bakin juna cikin shau i da soyayya. Sun auki lokaci suna farantama juna rai sannan suka saki juna suka koma su ka sake rumgume juna suna maida numfashi, kan Mimi na saman kirjin Aji shi kuma ya saka hannunahi ya na shafa gashin kanta, Idanuwanta a lumshe tana jin wani irin farinciki na ratsa ta a nan duniya gani take yi kamar tafi kowa dacen samun abokin rayuwa nagari, shi ma a bangarensa addu'a yake yi Allah kada ya bashi ikon kuntata ma Mimi, Allah ya zaunar da su lafiya ya ka e fitina. "Me za mu yi breakfast da shi yau Aji? Haka Mimi ta fa a, tana ame dashi, kai tsaye ya ce" Duk abin da Mimi ta shiryama Aji kinsan bai ta a juya mata baya ba." e idanuwanta ta yi kafin ta ce" Ko mu soya kwai ne mu gasa buredi, mu sha Tea ko? Sai ya gya a mata kai kafin ya ce" Ni fa ba ruwana da wannan bangaren, ke dai kawai ki ciyar da ni, ni kuma ina yin aikina na ci da ciyarwa." Ya fa a lokaci aya yana kashe mata ido aya, Sai kawai Mimi ta daki kirjinsa cikin sigar wasa tana masa mirmishi, sannan ta mi e lokaci aya tana fa in" Rana ta yi, bari mu karya karfina ya dawo jikina tukunna." Da kallo ya bita za ta shiga kitchen sai ya kwala mata kira ta juyo kai tsaye ya ce"Ba na hana ki shiga kitchen ba takalmi ba dankwali ba? Sai Mimi ta dafe kanta kafin ta shagwa e tana fa in"Na manta ne Aji." ewa ya yi bayan yac e mata bari ya zo cikin bedroom in su ya shiga ya auko mata hula da silafas inta na cikin hida ya zo har gabanta ya duka ta saka takalmin sannan ya kama kanta ya saka mata hular sannan ya kalleta kafin ya an rankwasheta yana fa in"Ba ki san saka Dankwali ko? Sai na yi miki aski" Baki ta tura kafin ta ce"Aski? To sai ka kalli gashin wa? Ya na juyawa zuwa kan kujeran da ya tashi ya ce" Aure zan ara, ba zan zauna da mai kai kamar na maza ba." Tsaye ta yi ta na buga kafa za ta fara masa kukan shagwa a, ya na jinta sai ma ya auki romot ya ara aran talabijin in lokaci aya ya na fa in" Fatima ina jin yunwa fa. aya saura na rana ban karya ba fisabilillahi fa" Haka ya fa a ya sa ta fa a kitchen in lokaci aya tana fa in"Da laifin ka me ya sa baka tashe ni ba? Bai san ko ta ji ba ya ce"Mace tagari ba ta jira miji ya tada ta sai dai ta tada shi, amman ke sai barci kamar kasa, zan ga ranar da za ki haihu Fatima." Ita ba ta ji sa ba. Ta kunna gas ta fara ora ruwan tea in bayan ta saka kayan amshi da ganyen shayi, sannan ta fara ko arin Kwaso wan da za ta soya buredi ya na can saman dinning wanda za ta gasa ga shi kuma sai da ta fara fasa kwan ta tuna sai kawai ta fito bakin kitchen in tana kiran sunan Aji bai jita ba sai da ta walaa masa kira da Karfi sannan ya juyo lokaci aya yana na rage aran talabijin "Miye ne? Haka ya ce mata yana ha e rai, shi fa baya son mace ta ri a saka shi aiki kuma ya lura halin Mimi ne ta ri a saka shi aiki kamar wani anta. "Buredi za ka auko a saman dinning.." Ta fa a cikin yar shagwa a, hararanta ya yi kafin ya ce"Ke fa? Kafar ki na ciwo ne? Wani kallon asa asa ta yi masa kafin ta aga masa hannuwanta lokaci aya tana fa in" Na saka hannuna a kwai ne, don Allah ka kawo min." Kamar ba zai ta shi ba haka ya tashi yana tura baki kamar mace ita kuma tana danne dariya yana ganinta sai ya dakata yana fa in" Dariya ma kike yi ko ? To Allah ba zan auko ba." "Afuwan haba Nawan, Aji na ajin zuciyata." Haka ta fa a har ta na masa fari Mirmishi ya yi kafin ya ce"Eh mana tunda kin sakani aiki ba, dole ki yaudare da kalamai mana." Haka ya je ya auko mata shima ba ta kar a ba, ta ce hannunta ba kyau ya kai mata kirchen, da sauri ya shiga ya sauke mata samman wani faranti har yana sauri ya fita ta bi shi tana Fa in" Ka tayani mana,ko gasa buredin Aji" Ko juyowa bai yi ba ya fice yana fa in"Yunwa nake ji, don Allah ki yi sauri." Daman ta san ba zai tsaya ba ba ta san me ya sa ba baya son ta yata aiki ba, aiki in dai ba shi ya yi niyya ba ita kuma tana so ta ga suna aiki tare cikin soyayya da auna. Bayan ta gama fasa kwan sai ta tuna bata yanka albasa da kayan miya ba, wanke hannayenta ta yi ta yanka buredin ta saka masa butter ta saka shi cikin oven yunda Aji ba ya son gasaahen buredi da wai ya fi son shi da Butter ya yi taushi. Gani ta yi aikin baya mata sauri tana yanka su tattasai, ta walama gogan kira ya i amsa mata sai ta da ara aga murya sai ga shi a bakin kitchen in lokaci aya yana fa in"Wai na ci miki bashi ne Mimi? Kada ki ce za ma ki ara aike na domin nima yunwa ta saka ba ni ma da kuzari." Ya fa a yana har e hannayensa a saman irjinsa, har ya na wani kauda kai ganin haka ya sa da sauri ta marairaice tana fa in" Aji to ka kama min na gama da wuri mana." Hararanta ya yi kafin ya yi mgana da tare shi da shagwa a tana fa in" Don Allah haba mana." aure fuska ya yi kafin ya ce"Me kuma zan yi yanzu? "Albasa za ka yanka min don Allah." Ido ya zaro kafin ya ce"Albasa? Mugunta ko? Kin san fa ranar haka ki ka sakani ina ta kukan dole." Dariya takke so ta yi amman sai ta kanne ta lamgwabar da kai kamar za ta yi kuka kafin ta ce"Shike
Chapter 177 · 0% Book details