Sashe 101
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta ce" jiya na gaji ne, shi ya sa da na dawo ban sauka gidan Hajiya na ijiye ta ba." Sai ya girgiza kai kafin ya ce" Tabdijam in aka sace wani abu a jikin motar fa? kin san wajen ba tsaro." Ba ta yi mgana ba a lokacin amman sai da ya kalleta lokaci aya yana fa in" Ko da ya ke yar Major ce, kuma ya mutu ya bar muku dukiya mai yawa ba laifi in barayi sun kwashi na son rabon." Ta kan rasa wata irin tsana ce Aji ya yi ma Abi, ko alama babu alamun sassauci a kalamansa, shi ko kunyar ta ba ya ji duk mganar da ya ga dama sai ya fa a mata ga wani arin abun haushi abu ka an sai ya ce eh ita yar Major ce guda ko ya ce Babanki kaza kaza alamu dai na ba girmamawa ko ka an bai iya tuna auran ta yake yi ba ko domin wannan darajan ya kamata ya daraja Abi ko da kasa ta shafe masa ido. Ba ta biye masa saboda in ta fa aya shi in ya tashi mai da mata amsa sai ta yi kuka, A cikin satin nan Hajiya take fa mata Yaddiko ba ta da lafiya suger in ta ya tashi har ta kwanta a asibiti tun tana asibitin ta fa a ma Aji domin har Mommy sai da ta kira ta, ta ce ta ko arta ta je ta duba ta amman ta yi ta masa magana ya i cewa komai saboda wani lokacin bayan gaisuwan sannu da zuwa ina kwana ba abunda ke shiga tsakanin su, har Yaddiko ta koma gida ba ta je ba. Ranar da ya zo da daddare bayan ya shiga akin Inna ya gaisheta ya shigo akin daman dalilin haka ta yi zaman jiran sa a falo. Da ya shigo ta yi masa sannu da zuwa ya amsa yanayin sa kamar an yi masa dole, ba ta yi rawwn jikin kawo masa wani abu domin ba ci yake yi ba, wani lokacin akin Inna ya ke ci ya oshi tunda ita girkin ta daman sai weekend to itama daga akin Inna ake ba ta abincin. Kai tsaye ta ce" Maganar zuwa duba Yaddiko, har an sallameta ta koma gida, yau daga wajen aiki nake so na biya na gaishe ta." Shima kai tsayen ya ce" Tunda an sallame ta alamu ne na taji sau i, ina ga ba sai kin je ba." Wani kallo ta yi masa kafin ta ce" Saboda me? ciiwo fa ta yi har da kwanciya a asibiti sannan ka ce wai ta ji sauki ba sai na je ba ina ga ka manta Yaddiko anwar Abi ce kamar matsayin uba take a wajena." Maganar da fa a mata yasa dole ta tattara sanyayyan jikinta zuwa cikin akinta ta kwanta tana kuka. "Ke ki ka san ta ma, nima ai ina da annen uban a auye kin ta a cewa za ki je ki gaishe su? Gwaggo yalwa ma bayan komawarta daga bikin mu ta yi ta rashin lafiya amman ban ji kin ce min za ki je ki gaisheta ba, koda yake kinsan an masu ku i suna yamar an talakawa, kuma ga shi sai hakuri kin ha a dangi da talakawa tunda talaka kika aura duk da ba haka Babanki ya so ba." A cikin ranta tana tunanin tabbas ba ta yi hasashe dai dai ba, da ta ke tunanin har yanzu Aji na sonta in har ya na sonta ba zai ri a saka ta kuka da ba en mganganun sa ba, iri iri ta ke tsoron magana ta ha a su Slsaboda kalamansa a kanta ba ma su kyau ba ne. Kuma bai barta ta je ba sai da Hajiya ta kira Inna Meri ta yi mata mganar sannan ta ce masa Walida za ta raka Binta ta je ta gaishe da Gwaggonta ba shi da mafita illah na amsawa shi ne farkon dalilin fitan ta zuwa gidan Yaddiko ta yi ni walidan ma ba ta samu zuwa ba ta na zazza La'asar na yi ya kirata ya ce ta dawo, sai kuma ta zo tafiya ta kunna motar ta sai arfen nasara ya yi gaddama ta ki tashi sai ta bar sallahu akan za ta kira bakani en ta zai zo ya duba, Yaddiko ta ce Munzamil ya auke ta a mota ya mai da ita gida. Ashe ashe yana kofar gida suna mgana da Auwalu da yake an fara gyaran Inda Saddiqu zai zauna, lokacin da ya ga Munzamil ya sauke ta a mota kallon da ya yi mata sai da ta ji hanjin cikinta ya tsinke, ta na gaishe shi Auwalu ka ai ya amsa amman shi wani irin kallo kawai yake yi mata. Tana shiga gida kamar ta sani ta yi zaman ta akin Inna wajen su Yaya Amina sun zo sai da aka kira mangariba ta koma akin ta, ashe ya lna ri e da abun ya na shigowa ya iske ta a falo tana ko arin saka wayar ta a chaji kai tsaye ya fara challangin inta akan wanda ya auko ta a mota cikin kaushin murya. "Munzamil ne, motata ce ta ki tashi sai na bar ta can Yaddiko ta ce ya auko ni zuwa gida." "Ni ba sunan shi nake tambaya ba waye shi? Me ya sa ni ba ki kirani kin fa a min ba, shi ne kika hau motar wani balagaggen katon banza ya kawo ki gida ko? Sai ta kasa magana domin in ta ce za ta yi masa vayani ma sai abun ya lalace, kanta ta dafe domin ta rasa mafita ya manta shi da kansa ya ta a ce mata shi ba direban ta ba ne, shi ya yi mata girma da ya zama mai hidima mata, amman ji yadda ya ke masifa saboda wani ya auko ta. arin ta fa a masa Munzamil kamar an'uwa yake a wajensu amman bai gane ba sai faman fa i yake yi" Ni ba za ki iya kirana ki fa a min ga abin da ya faru ba? Kinsan ai ina gidan tun azu." Ba da wata manufa ba ta ce" Na ga ba mota a hannunka ne shi ya sa." Sai kawai ya yi yar dariya kafin ya ce" Oh na manta ba mota a hannuna sai mashin, ar Major guda ai ba mutuncin ta ba ne a ganta tana yawo a kan mashin ta fi arfin nan, sai yanzu na gane." Idanuwan Mimi suka tara walla cikin tsuma ta ce" Wallahi ba haka.." "Ban ce ki yi min rantsuwa ba, kashedi na karshe shi ne ban yarda karti suna mana zarya a kofar gida da sunan wai an'uwan ki ba, in na ara ganin wani ya sauke ki ko waye shi sai ranki ya yi mugun aci, ko da na ke talaka an raina arzi i na ba salallame ba ne ni, ki kiyaye." Daga haka ya fice daga akin a fusace ya bar Mimi nan ta na hawaye wannan bala'in ya fara isar ta tun ba'a je ko'ina ba ta na kokarin yin nadama. Komai ta yi ba ta tsira ba duk yadda ya kuntata ma rayuwarta ba ta ta aga kai ba domin dai a zauna lafiya ya fahimci tana son shi shi ya sa yake yi mata abin da ya ga dama, kuma sai ya ri a kuntata mata da kalamai da shigen bakar zuciyaras sannan ya ri a nuna yana kishin ta amman har yau ya kasa aikata wani abu guda aya da zai nuna ya na sonta har yanzu. Dalilin haka ya sa ya auke kafa a gidan ashe wai baya gari sun tafi wani traning a Jos itama a bakin Walida take ji, ita ba ta da wannan mutumcin balla tana ya sanar da ita, da gaske har rama ta fara yi a tsaye amman sai ta duba da fita aiki da kuma kai da kawo sai a Hankali. Ya na can Jos in mamansu Rukky ta kwanta rashin lafiya duk yan wajen aikin su, sun je sun gaisheta amman duk yadda take da Rukky ba ta je ba, domin ta yi ta kiran Aji bai auka ba ta kuma turamai sa on tana son zuwa duba maman Rukky ya yi kamar bai gani ba, kuma tana da tabbacin ya ga ni, ita kanta ai ta auran ma kanta bala'i wlh an sauya Aji yanzu gaba aya dabi"un sa ba su da kyau mugunta kawai yake yi mata sannan yana danne mata ha inta ga uban dokiki ga sharu ai, ta fara tunanin anya ba ta yi gaggawa wajen yarda da wannan auran ba? Haka tana ji tana gani ba ta je duba maman Rukky ba, ita har kunya ma take ji, ta yi ta ba ma Rukky uzuri har dai aryan ta ta are, Aji kuma kusan sati su ka yi a Jos lokacin da ya dawo Mu'azzam sun zo garin shi da Hibba, sun zo ganin gida sannan Yayar Hibba za ta yi aure shiyasa suka ungumo gaba aya. Shi ya sa har ta ga Aji ya zo gidan zuwan su yasa sai gidan y ke cika da su Bintu ga bikin Saddiqu ma ya kusa Magajiya ba zama ana ta shirye shirye domin so take yi bikin ya fi bikin Mansoor da a ka yi domin ta nuna ma Meri ta sha gabanta. Lokacin suka zo Mansoor ba ya garin lokacin shi ya sa sai ta sauki Hibba da Junior a akin ta Saboda sun saba da ita sosai tun bayan siyan hijaban nan suna chart kuma suna waya, sannan Mu'azzam na burge ta ya tara dukkan hallaya masu kyau da su ka yi hannun riga da na an'uwansa. Ya kan kira ta lokaci bayan lokaci su gaisa kamar wani yayan ta haka ta auke sa, to suna akinta tana ta hidima da su tunda tun ana saura sati aya ita ta fara zuwa sai daga baya Mu'azzam ya biyo ta, ta fara sauka anan gidan ne kafin bikin ya karato ta koma gidan su. Mimi ba ta san har ankon bikin an yi mata ba, Mu'azzam ya yi musu dukkan su har da su Yaya Amina sai da a ka zo