← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 198 OF 208

Sashe 198

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gobe suna ta zo ita da Mu'azzam da Atamofi guda biyu sai na Bby sai 30k daga Mu'azzam. Ranar azumin farko a ka yi shagalin suna duk da azumi ne Mimi ta ga taron mutane kaf yan'uwanta sun zo har da Madiha gida cike kuma isu isu tunda su Bintu suna can gidan Inna suna na su taron. Mimi ta sha kunshi da kitso. Sannan ta shiga ta fita ita da Maryama wacce Mimi ta ce za su ri a ma lakabi da Ummi tunda yar wajen Mu'azzam Ammi suke kiranta. Sannan har Makeup an yi mata sannan sun sha hotuna, an yi tsire ga wanda ba za su tsaya a sha ruwa ba, a wata yar jeka sai a saka sinasir ko waina sai naman kaza ko na rago sai a saka maka cake ko samosa sai lemu da ruwa, duk sun yi zobo mai rai da lafiya da kunin aya amman zobon wannan na uban gayya ne za su yi walima da daddare a can Camp in su. Sinasir in da waina Mimi ta ibar masa kula aya sai fride rice da yasa Binta da su Yaya Amina za su yi masa, sai soyayyen Naman kaza pepe sai kayan Snaak in da Mimi ta ba da a ka yi gaba aya bayan an kawo ta di ar masa tsire kuma daman na Aji ne sai aka raba uku aya Mimi da danginta aya kuma na su Inna da yan'uwansa ayan kuma nashi. Matan su Nasir duk suna gidan Mimi har da matar Ahmad.Tun da ya ce shi zai koma amman ita sai bayan salla anan za ta yi azumi sannan cikinsu ba wacce ta zo hannu rabbana. Daddy kuma turmi biyar ya yi mata da kudi 100k an yaddiko ma haka kowace da zaninta har Rukky da Jaheed sun tura mata ku i sannan an ma'aiikatansu suma ba su zo hannun rabbana ba. sun ha a mata kudi sun siya mata zannuwa da kayan jarirai tunda lokacin bikinta ya zo a kurewar lokaci ba su samu sun yi mata ba. A ji dai suna gidan Makama gaba ayansu ya sha farar shadda tana kyalli.Nasir ya so har wasa a buga Aji ya ce a'a Walima dai ya shirya domin a taya shi murnan samun aruwa. Bayan an sha ruwa Walida da Mariya suka kawo musu abun bu e baki anan gidan Makama suka ci suka sha.Sallar mangriba ma sai Ahmad ne ya yi musu limanci, suma in duk sun ha a masa kudi ya ce ba zai amsa ba su kace ya raina ne sai ya kar a ya saka albarka dagan gida ya koma saboda ya yi wanka walimar karfe takwas na dare abunci kuma da ababen shan su Mu'azzam za su auka zuwa can Camp in su.Gayyar da ya yi ka an ne daga yan Tream in su sai abokan shi sai kuma yan nasaran Team Tudun Wada team da sauran Clubs wallon kafa na Gombe manyan ciki. Sai Coach din su na gombe United da sauran shugabbanin ananun kungiyoyinsu. Ko da ya koma gida, ba'a wani ragu ba yawanci duk nan za su kwana sai illa yan Kano ne suka koma gidan Hajiya. Yana shigowa falon su khadi ne da su Bibi sai su Yayan Yaddiko. Khadi tana ganinshi ta fara sakin gu a tana masa kirarin Angon karni baban Maryama mjin Fatima. Karon farko da ta ga dariyansa hayaniyarsa ya fito da sauran da ke ciki, ana cikin haka sai ga su Yaya Amina da kaya niki niki na suna shi yas a ya sulala zuwa akinsa ya aga waya ya kira Mimi sai gata, ta zo ita da Ummi sun sha kwalliya ya kama su ya rumgume sannan ya sake ta ya ce zai shiga wanka ta za a masa kayan da zai saka kafin ya fito ta fito masa har da takalmi shadda mai ruwan sararin samaniya har da babban riga ya fara korafin babban rigan tana damin shi ta shagwa e mass lokaci aya tana fa in" Don Allah ka saka, kai fa yanzu ka girma sunan ka Baban Maryam." Da kalaman ta samu ya saka ta saka masa hula da agogo ba e ta fesa masa turare, Ya yi kyau har sai da ta auki wayarsa ta yi musu hoto.Nasir sai faman kiran shi yake yi ya ce su na can ga su ma za su yi sallar sai yace shi zai tsaya a hanya ya yi sallah sannan ya ariso. Zuwan su Yaya Amina ya sa har ya fice ba ba a lura ba ana kallon kaya ana saka albarka, yana hanya Daddy ya kirashi ya na masa tsiyan haka ake yi shike nan tunda yana uba baza'a gayyace shi waliman ba ne? Sai Aji ya ji kunya kwarai ya ba shi hakuri da cewa bai san ya na son zuwa ba. Nan Daddy ya ce ya bashi address in ya tashi daga in da ya je zai biyo ko da bai da e ba nan da nan ya tura masa adireshin Camp in su dake cikin gari. Ko da ya isa hall in cikin Camp in su da suka yin meeting ko wani taro ya cika da jama'a. Yana zuwa a ka fara gaisawa da shi ana masa fatan alheri ji kawai kake yi ana fa in" Congratulation Captain Allah ya raya mana mai sunan mama Maryama." Walima ce daman an ci an sha an yi badali da nama da Kaji, an ci tsire an sha lemuka an sha zo o da kunin Aya har da masu guzuru su Musa Zinder sun fi kowa murna da wannan walima domin sun ci sun sha sai hqmdala, ana gabda tashi sai ga Daddy ya zo ya dai gaggaisa da mutane bai tsaya ba sai a mota aka saka masa tsiren da Sank in sa zuwa goma na dare kowa ya watse bayan an gama yi ma Maryama(Ummi) addu'an rayuwa cikin aminci, bayan an gama taron yana wajen tawagan an Team in shi suka same shi da ro onsu suna son zuwa gidanshi su ga Maryama(ummi) sai ya ce su bari zuwa jibi sai mota ta kwashe ta kaisu su ganta Coach ma har gida ya je ya yi barka ya ba ma Mimi wani abu ya ce ta siya ma Ummi abun wasa. Ranar ba'a gida ya kwana ba shi da Mu'azzam suka kama hotel, a daran ne Aji ya ce dole suna bukatar wani gida in dan irin haka ya faru su samu wajen sauka. Zuwa washegari taron suna ya tashi saboda azumi daga Khadi har Madiha a ranar suka koma Jawahir daman tun 12 yan kano suka mika hanya. Gida daga Mimi sai Inna Zainaba, naman suna kuma daman yan kano kawai a ka dibarmawa da yaji sai gidan Daddy sai Hajiya su khadi duk ba su tafi da shi ba gwarama Jawahir an ce ta kai ma Dr, Hibba da Mu'azzam kuma ba su koma ba sai washegari duka duka kwanan su hu u ne saboda azumi a ranar kuma doguwar motar Team Gombe United ta kwaso su Zinder gaba aya dai yan Team din zuwa gidan Aji karo na farko suka yi ma Mimi barka. Kowanne sanye da kayan suna Bluee in riga da wando, daga ma morning Training suke Aji ya ce a kawo su. Ummi ta sha auka Kb har kallon Aji ya yi yana fa in"Captain ina kamu in ta girma." Suka fashe masa da dariya Aji ya yi mirmishi bai yi mgana ba ,Inna zainaba da suka ba ta sha'awa ta ce" Haba ina za ka jira ta? Kai da ko yanzu ka isa aure." Da sauri Kb ya ce"Ko ta uku ko ta hu u don Allah Captain." Ya fada har yana magiya harara Aji ya sakar masa kafin ya ce"Kun ganta ko? Maza back to camp now." A tare suka amsa da" Yes Captain." Ba Inna Zainaba ba har Mimi sun matukar burgeta, ta ji da a ce namiji ta haifa ba abin da zai hana bai gaje ubansa ba. Mimi ta cigaba da jegonta cikin gata ko sati uku ba ta yi ba inkinta ya warke tunda ta na samun kulawa ta koma asibiti an ce komai lafiya, Inna Zainaba ne ke kula da ita sai Hajiya da kan leko itama hakama Inna, an yi salla karama duk tana cikin Jego amman fa gaskyan Aji ne jegon nan ya yi mata matukar kyau kamar ba ita ba, Sannan Ummi ta yi wani irin kiba. Daman Aji bai yarda an yi wannan exculation in nan ba ruwnta a ke ba ta ya ce ba zai iya daukan hakki ba, bayan sallah da wasu kwanaki Mimi ta yi arba'in sai kuma ta fara gyara kanta daman kuma Inna Zainaba ta ma ta kokarin shiga cikin ruwan bagaruwa sannan Yadikko ta aiko mata da Gumba ta na sha da Madara ita kuma sai ta siya ha in kazan Uwargida na Surayya Dee, Bojuwa saboda ita dai Mimi ta amince da kuma yarda da ha in kazan Surayya Dee saboda ta na da ewa a jikin ta kafin ta gama aiki sannan uban gayyar yana ru ewa in ta samu gyara daga surayya dee bojuwa mai kayan gyara.+234 803 277 3332 kuma har ta aiko mata da shi har ta fara amfani da shi. Inna Zainaba kuma ta fara shirin komawa Kano, ta sha tara arziki ku i kawai 30k Aji ya ba ta bayan zannuwan da Mimi ta ha a mata Inna ma da omonta da sabulanta da yaji da ta saka a ka daka mata.Kwanansu Hamsn Inna Zainaba ta koma kano da sha tara na arzi Mimi ba ta je ko'ina ba bayan ta gama jego, Sai da Aji ya gama famshe kwanakin da ya yi kewarta ta ma kusa arba'in biyu sannan ya bar ta taje gidan Hajiya ta yini sai dare yaje ya dawo da ita gida.bWashegari gidan Daddy ta yini, ba ta kara fita ba sai bayan kwana biyu ta je gidan Yaddiko daga nan ta lelleka gidan yayanta dake kusa. Washegari kuma gidan Inna ta yi yinin ta, Inna ko Ummi na bayanta tun da suka zo, sai dare ya zo su ka koma gida daga nan jefi jefi tanq fita ta je can gidan wajen Magajiya
Chapter 198 · 0% Book details