← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 208

Sashe 42

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

aure yanzu? Duka duka nawa yake? A lokacin sai Hajiya ta ce"To ai ko ba yanzu ba Meri sai iyaye su shiga mganar, kamar yadda ya ke son zama Sojan nan ya je can ya na karatunsa itama tana nan ta na yi sanda ya gama ya dawo itama ta gama sai su yi auransu ai ba wani abu, ni fa ba na yamar zuru'arki Meri ke macece mai kirki da mutumci ya'yanki masu tarbiya ne, kuma maganar ruwa ba'a san kwando ba ne bai taso ba abin da Binta ke so shi nake so, matukar kuma ta ce Mansoor ta ke so ni kuma zan shige gaba wajen na ga ta samu abin da take so." Tunda lokacin Maganar sai ta fara damunta ta turke Mu'azzam kuma ya tabbatar mata da gaske Baban Inna na son Mimi irin soyayyar da ba zai iya kwantatawa ba, in ba ta manta ba yana da kuma ra'ayin aure tunda ya na da ananun shekaru, ita abu daya ke damunta da shi nacin tsiya da kafiya sannan ga auko fitinar da ta fi karfinsa in ba neman jawo zaune tsaye ba ina shi ina Binta yarinyar da Ubanta ma akan dole ya bar ta hannun mahaifiyarsa ita fa tana hango ma Baban Inna nadama kan wannan shegen kafiyar nashi. Kan nacin sa da zama Sojan nan har Mallam Sidi ta shirya ta je bikin yaron yalwa da shi ma taso tafiya ya ce shi ba zai je ba, ta ma ta zencen Babansa yakubu ya kira shi ya je can Bauchi ya same shi ya yi masa fa ya ji Yalwa ta ce to in Yakubun yazo ko in sun yi waya tunda yanzu ya yi arfi kasuwanci yake a Bauchi yana can shi da iyalansa. To kila dai ba ta samu magana da shi ba ne, bai aiko ba kuma sannan ba ta kara ji daga Yalwa ba, ta so shi Yakubun ya kira shi ya matsa masa kila ya watsar da wannan ra'ayin na sa na zama Soja ya nemi wata hanyar. "Inna me kika dafa ne? Mu'azzam ya katse mata tunani sai ta yunkura ta mike tana fa in "Tuwo ne miyar yauki bari na zubo muku." Ta zubo musu kenan sai ga Baba anjuma ya shigo gaba ayan su suka yi masa sannu da zuwa ya amsa ya na okarin sakin fuskarsa. Cikin an na shi ya zauna suka ci cin tuwon Mansoor ne ya fara oshi ya tashi Baba Danjuma ya kallesa yana fa in"Ka osh ne Baban Inna? Yana nufar randar Inna ya ce"E Baba.!" ruwa ya di a a buta ya shiga makewayi ya kama ruwa sannan ya wanke hannunsa ya kuskure bakinsa. Bayan ya fito sai ya zo ya durkusa gaban Baba anjuma kansa na kasa, Inna Meri na gefe tana kallonsa kafin ta yi mgana Baba Danjuma ya ce"Ya aka yi ne Baban Inna? da wata matsala ne." "Baba Aure nake so na yi.." Gaba ayan su suka kalleshi a tare Mu'azzam sai da ya ware da tuwo duk da ya san hakan zai iya faruwa amman bai tsammanci maganar da wuri ba, inna Meri ta yi tagumi kawai tana kallon Baban Inna yaro arami na neman saka kanshi a wahala shekararsa fa duka duka ashirin da uku ne tsawon kafa ke jansa yake ganin ya isa ya yi aure har ya ri e mata yana zaune ba shi da sana'a naira biyar ma na bashi sha'awa. Baba anjuma sai ya dakata da cin tuwo ya mi e yana fa in"Babban mgana, taho ka zuba min ruwa na wanke hannuna sai mu yi maganar sosai" Haka ko akayi ya zuba masa ruwa a bakin magudanar ruwa ya wanke hannunsa sannan ya koma ya zauna yana kallon Mansoor mirmishi ya su uce masa ai shima ya ta a gaya masa haka tun bai kai haka shekaru ba. "Baba ni fa ba zan bari sai na fara tsufa zan yi aure ba, da wuri zan yi aure saboda ba na so ya'yana su taso su ganni arfina ya are." Ko a lokacin da ya ce masa haka sai da ya yi dariya kuma yana da ya inin Baban Inna zai maimaita mganarsa lokaci ka an tunda shi baya fa in abin da ba shi ne acikin ransa ba, Inna Meri ya kallah kafin ya ce"To ke fa Meri kin ji, za ma ai bai gan ki ba Baban Inna Aure yake so yayi" Inna Meri ta ja katon tsaki Mtsewwww kafin ta ce"Ai sai ya yi auran tunda auran fa e ne a fatar baki, ban da shegen rigima kana yaron ka da kai ba ka ba wani ajiya ba, kai ba ka ijiye mai ba ka ba sai kawai rana tsaka ka ce wai aure za ka yi? Anya Baban Inna..!" Ta fa a tana nuna shi da yatsa kai tsaye ya ago yana kallonta kafin ya ce"Inna ina da gado na, a saida gonakin baba na Mallam Sidi ayi min aure da shi." Ai sai Inna Meri ta hau tafa hannu tana fa in" Yai naji sheganta ka, zan ace ka Mansoor yanzu nan wlh." Baba anjuma da ya ga ranta ya aci yayi saurin tare ta da fa in" Kar ki yi masa fa a ai ba laifi ya yi ba, kuma bai yi anta ba, wa anda ba su kai shi ba ma su na yin aure yanzu dai mu saurare shi mu fara sanin in da ya samu matar" Inna Meri gabanta na fa uwa ba ta son ta ji ya kira sunan da zai ba ta tsoro. "Mimi ce, jikar Hajiya in da Inna ke zuwa aiki." Inna Meri ta ora hannu a saman kanta lokaci aya tana fa in"Na shiga uku ni Merama, da gaske daman son yarinyar nan kake yi baban Inna? Me ya sa ka cika fitina ne? Ina kai ina wannan yarinyar? Kai tsaye ya ce"Inna tana sona itama, kuma Hajiya ai ta sani kuma ta amince da hakan." Inna Meri ta aika masa da dakuwa lokaci aya tana fa in"Ka ga naka nan, In Hajiya ta sani Hajiya ce ta haifeta, babanta Soja ne kuma ko Hajiyar ba ya jin maaganarta wlh ba zai aura maka arsa kana zaune ba ka da wani tunani ba, ko a addini mai sana'a aka ce ba mai burin banza ba, ka fita idona da wannan mganar na ma gaya maka." Daga haka ta tashi ta shige aki tana ta fa a, shi kuma Mansoor yana gayama Baba anjuma ai ya na neman karatun Soja in ya samu zai iya rike Mimi, Baba anjuma ya samu ya lalla ashi yace za su yi mgana da Safe. A can akin su ma Mansoor Mimi ya kira a waya yana fa a mata ya fa a ma su Inna zai aueta, tunda itama yanzu tana da waya da ta saka Hajiya ta sa Daddy ya siya mata mai kyau da ita yar yayi. Mu'azzam bai isa ya ce ma yayansa wani abu ba, amman shi kanshi ya na hango ma kansa ya yi gaggawa sannan Soyayya ta rufe mishi ido ya kasa gano abunda Inna ke hango masa. A daran shima Baba anjuma yayi ta fama da Inna Mari ta sauka daga fushinta su yi mgana ta ce in ta sauka sai Baban Inna ya bar maganar Jikar nan ta Hajiya, shi ko Baban Inna ya yi nisa da ba ya jin kira yadda yake jin Mimi a zuciyarsa in ya rasa ta sai ya iya mutuwa. Kuma shi ya gayama Mimi da kansa cewa Inna Meri ta ce ta fi arfin shi. Kuma su sun tsara rayuwarsu da cewa zai tafi makaranta Sojoji kafin nan za'a aura musu aure sai ya barta wajen Inna ta cigaba da kararunta. Mmi kuka reras ta ri a yi ma Hajiya akan abin da Inna Meri ta ce, Hajiya ta ce za ta aika a kira mata Merin ta ji me ya sa ba ta son jikarta ta zama surukan ta? Ba ta ma kai ga aikawa ba sai ga Inna Merin ta zo ma Hajiya Godiya domin 100k ta ba ta da bikin nan bayan ananun alherinta a gareta sannan ta bata hutu ta ce har sai gajiyan Biki ya sake ta sannan ta dawo. Tana zuwa da niyar yi ma Hajiya godiya sai tace su shiga cikin akinta ta na son mgana da ita. Tana jin haka tasan kwanan zencen, illai ko Hajiya ta tsareta akan me ya sa ba ta son alaqar Mansoor da Binta? Inna Meri sai ta saka kuka cikin kukan take fa in"Haba Hajiya ban da neman rigima ina Baban Inna Ina Bintar ki? Hajiya tace"To Ubangiji ya ha a sai mu ce a'a tunda suna son junan su sai kuma mu hana su kudirin alheri." Inna Meri ta ce"Hajiya Baban inna yaro ne yarinta ne ke damunsa shekaransa ashirin da uku ne da wattani, da me zai ri e Binta? Sojan da yake ta ulafuci har yanzu bai samu ba kuma ya ki sauya ra'ayinsa don Allah Hajiya a bar mganar nan shakuwa ce kawai ba wai soyayya ba." Hajiya ta ce"Duk na fahimci tunaninki, kina da gaskiya abin da za'ayi ai shima kabirun Soja ne zan kira shi mu yi mgana sai a zauna ko shi sai ya ne ma Mansoor in makarantar Sojjojin a yi alkwari in Mimi ta gama karatu su yi auren su ba shike nan ba." Inna Meri dai ta kasa mgana amman tana hango wani abu da ba zai tafi dai dai ba amman gudun kar Hajiya ta ga kamar tana gudun maganar sai ta amince da hakan, Kuma Hajiya da kanta ta kira Mansoor ta zaunar da shi ga shi ga Binta ta ce ya fa a mata gaskiya yana son Binta? Kai tsaye yake kallon Hajiya kafin ya ce" ba sonta nake yi ba, kaunarta nake yi Hajiya." Itama Hajiya ta tambayeta lokacin Mimi an zama yan mata shekaranta sha tara, ta rufe fuska ta oye bayan Hajiya tama yar dariya. Hajiya ta ce kar su damu za ta yi mgana da baban Binta. A lokacin ita Mimi soyayya ta makantar da ita kamar yadda ya makantar da Mansoor dukkansu suka kasa gano abunda mutane ke hango musu. Hajiya
Chapter 42 · 0% Book details