← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 208

Sashe 12

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da Hajiya zuwa Gombe nan suka bar Khadija tunda ita sai mijinta ya so za su koma tare. Ko bayan dawowarsu Hajiya ma ba ta kara ta da mganar ba, sai dai kwana uku tsakani ta dawo daga wajen aiki ta iske Yaddiko a gidan ta na ganinta sai da gabanta ya fa i domin tasan akwai mgana.ilai kuwa kan mganar jaheed ne tana ta ma Mimi fa an da ta ki an uwanta so take yi ta zauna ta cigaba da fita aiki tana nuna fuskarta a duniya bata da niyar aure. Daga karshe ta gatsa ma Mimi mgana da cewa" In ma wannan yaron kike ta jira to kin yi a banza, a gabanki a gaban mu mahaifinki ya ce ko bayan ransa kika auri wannan yaron bai yafe miki ba." Mimi ta fashe da kuka wiwi Hajiya ta fara yi ma Yaddikon fa an me ya sa take haka ne? Ita kuma ta ce ai gaskiya gwara ma ta rufa ma kanta asiri ta kar an uwanta yadda ma tun lokacin yaron bai kara nemanta ba zata fahimci da gaske yake yi abin da ya fa da ya ya ce ko su ka ai suka rage a duniya sai dai su mutu ba aure ba zai aureta ba." Cikin fa a Hajiya ta ce"To miye na sai kin ta do da abin da ya wuce Yaddiko, ko Kabirun da kike magana ya yi sanyi kuma shi da kansa ya ce tunda Binta bata so a bar mganar ba shi kenan ba." Yaddiko ta yi shuru ba ta yi mgana ba sai can ta ce"Ai shike nan ta share kafa ta ci gaba da zama, daga karshe su kansu in da take aiki ta na fara tsufa za su nemo wata domin suma da kyanta da Kuruciyarta suke amfani da zaran shekaru sun ja sai dai kuma ta dawo zaman gida." Kalaman sun yi ma Hajiya ciwo sai dai bata nuna ba cewa kawai ta yi"To mun gode sosai." Alamun ranta ya baci da Yaddikon ta ga haka ne sai ta koma kawo ma Hajiya illar zaman Mimi haka ba aure tunda tana da maneman ba wai babu ba ne. Hajiya ta yi mata bakam har ta gama maganganunta ta kira Jikanta yazo ya auke ta ya maida ta gida. Mimi kuma ranar kwana ta yi kuka sai dakyar Hajiya ta lallasheta tasha Tea ta kwantar da kanta a saman cinyar Hajiya tana na hawaye tana fa in " Hajiya ko wa ya i ya fahiimceni ko wa ya i ya fahimci ta inda na ke jin ciwon abun, Hajiya ta nan ne, anan ne na ke jin wani irin nauyi a kirjina ta nan wajen ne." Take fa i tana kai hannun Hajiya saitin wajen zuciyarta. Cikin damuwa Hajiya ke fa in "Ki yi hakuri Binta komai mai wucewa ne In sha Allahu." Tana kuka Hajiya na share mata hawaye, Kukan da ta yi jiya yasa washegari da safe tana karanta labarai haka ta je wajen aiki fuska duk a kumbure. Ta sha tambayoyi sai dai tace idanuwanta ke ciwo sai aka koma bin ta da sannu Allah ya sauwake. Rukky ta zo ta sameta a restroom tana hutawa ta ri a damunta da mgana. Ta gaji ta kalleta cikin wani yanayi kafin ta ce"Baby yaleni yau bana jin da i ne kwata kwata." Baby ta kalleta kafin ta ce"Daman tunda na ganki na fahimci haka, ki fa a ma Manaja sai kije gida ki huta in kin warke sai mu yi mganar bikin Biba ne daman" Shawaran Rukayya ta bi, taje ta sanar Manaja nan da nan ya ce ta koma gida daman yau da safe duk wanda ya kalli labaran Safe yasan wani abu na damun Mimi. Idanuwanta da fuskarta sun kumbura sannan ba ta da fara'a ko ka an shiyasa da ta ce ba ta jin da ba wanda ya karyata hakan. Dakyar ta iya tuka kanta zuwa gida sai dai Hajiya ta ga ta dawo ta ce mata kanta ke ciwo zata huta, Hajiya ta ce Allah ya sauwake ta kwanta zuwa azahar in ta tashi sai taci abinci ta sha mgani. akinta ta shige ta kwanta a saman gado ta na sauke numfashi. Ba kanta ke ciwo ba zuciyarta ne ke ciwo amm tunda zuciyar tana rufe ne ba wanda ya sani ballantana ya fahimci halin da take ciki. Aji. Aji. Aji. Shi ne ciwonta, shi ne kasarwata shi ne kuma rauninta shi ne ciwon da ya yi shekaru ya na cinta acikin zuciya. Ta yi addu'an har ta gaji ta bar ma Allah lamarinsa. Wasa wasa sai da shafe kwanaki uku ba ta je wajen aiki ba. A fuskar labarai Salim Bunza aka yi ta gani ba ita ba sai a ranar na ukun da ta dawo ne ta cigaba da kawo labaranta a yadda ysarin yake tun Farko. Sai dai kowa in ya kalleta sai ya ce ta rame idanuwanta sun zurma ciki sannan ta rage karsashi da fara'a. _Haka so ya ke iba ya maida kai bawa. Matsayin ka bai dubawa, balle yasan kai waye,ya saka ka yi jinya. Ka sauka kan Hanya ka manta al aarya ka yi kalan wawaye._ ******* *1rd March 2022* Anguwan Arawa da misalin karfe 8:30pm na daren ranar Alhamis.* Jiya ya dawo daga can kauyen mahaifin shi wato garin kwami cikin garin hedikwatansu na Mallam Sidi, gajiya ce jiya ta rufe shi ya sa ya wuce gidansa ya kwanta da rana kuma yana camp insu tunda evening training suka yi. Sai da suka tashi ne ya koma gida ya yi wanka ya auko tsaraban da suka matsa masa sai da ya auko, kifi ne da su dankali doya da sauransu. Tunda Allah ya albarkaci garin mallam Sidi da amfanin gona da kifin Kifin bushasshe ne, shi ba ya cin kifi tun da ya ji labarin sanadin kayar kifin ne ajalin mahaifinsa ya tsani kifi a rayuwarsa. A msallacin kusa da gidansu ya yi sallar isha'i yau da Motarsa ya zo shi ya sa matasan anguwa suka auki Ihu ga Aji ya zo, Aji yara da manya sunan Aji na bakinsu. Tare da su Baba Sani yau ma suka yi sallar har da Baba anjuma. Tsaraban da ya zo da shi yara ya sauke a kofar gida ya ce su shiga da shi shashen Inna Meri. Mansoor mutum ne mai kyauta hannunsa ya na sake ne, shi ya sa in dai yazo anguwan nan ya riga ganin mutane kenan. Ta bakin Inna Meri ta ce Baban Inna jama'a fa Rahma ne ka cigaba da aikin alheri wata rana in ka mutu wallahi da wannan shedar za'a tuna ka. Kuma tunda Allah ya rufa mishi asiri ai ya na da halin taimakawa. Bayan ya gama sallaman jama'an garin ya zo ya sallami gidansu. Tunda tun bayan da ya yi karfi a wallon kafa ko ya ce tun bayan da ya cike takardan Kontiragin in da ya yi da kungiyar wallon kafa ta Gombe United rayuwarsa ta sauya. Duk watan duniya nan ya na kwasan albashi mai tsoka, sannan kuma ga alawus in sun fita gari sun buga wasa. Ya fito ma ya fa i irin ku in da yake samu sai ma a karyata sa. Shi ya sa ya auki nauyin abincin gidansu duk wata sannan ku in makaranta Mariya da Walida da duk wasu bukatu na shashen su. Bangaren su Baba sani ma yana siya musu kayan abinci duk wata wani lokacin kudi ya kan ba su, ko kuma ya wakiltan Auwalu tunda in aka ba su kudi sokewa suke yi suki siyan kayan abincin. Auwalun ma daman ya kirashi tun shekaran jiya yana can kauyensu ya ce ya bari ya dawo, to shima anan gida suka ha u shima dai yana masa bayanin matarsa ke da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe ba shi da ku in ragon suna ballantana ku in hidiman suna. Kuma daman gini yake yi kuma yanzu aikin sai a hankali. Bai damu ba ya ce zai tura masa ku i ta asusun bankinsa ya cire kudin hidimarsa sauran ya siya ma su Baba sani kayan abinci. Anan kuma take ya ba su kowanne dubu ashirin na cefane. Suna ta saka albarka duk da yasan a bayan idon shi sai sun raina. In da zai rike abin da suka yi masa a baya ko kallo ba su ishe sa ba. Ba zai manta yadda suka ware shi ba, a cewar su shi Agola ne. Sai dai alherin Baba anjuma yake kallo a gareshi shi ya sa yake musu komai baya nuna bambamci. Ko gyaran gidan da ya yi kaf akunan matansu ya sa an sassake an saka musu tayels da kuma fentin zamani. Dakin Inna Meri da magajiya kuma ya maida musu shi kamar na yaran mata. Bai nuna bambamci ba duk abin da ya saka ma Inna Meri shi ya saka ma Magajiya. Amma bata ta a godewa ba, sai ma masifa da ta ke yi a bar mata akinta an ta Auwalu zai gyara mata, yaron da ke fama da kansa ammh fa da aka gyara akin ta ji da i ba ta dai nuna ba har ya'yanta da a shekarun baya sun sha su nuna bambamci kiri Kiri tsakaninsa da Mu'azzam. Tunda shi sun ha a uba shi kuma zuwa da shi Inna Meri ta yi agola ne mara galihu. Tare suka shiga gidan da Auwalu Magajiya na ofar akinta tana tatan nikan geron kunun safe da za ta dama suka shigo. Auwalu ya fara gaisheta ta amsa cikin fara'a amma Mansoor na cewa" Barka da dare Magajiya." im amsawa ta yi shi kuma ko ajikinsa ya tsallake zuwa shashen Inna Meri. Ya bar Auwalu tsaye ya a fa in "Magajiya kina jin Mansoor na gaishe ki kika amsawa? Sai ta masifa tana fa in"Ban amsa ba sai kuma na yi laifi? Ba ka ji irin gaisuwan na shi ba ne wai barka da dare kamar wata sa'arsa ai in uwarsa ce meri ba haka yake gaisheta ba." Auwalu yace"Magajiya tsakani ga Allah ko Inna Meri haka yake gaisheta ko Baba ne kuwa shi haka yanayin gaisuwarsa yake" Sai ta fara balla masa harara ta na fa in "Ta fi can sakarai mara kishin kai
Chapter 12 · 0% Book details