← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 153 OF 208

Sashe 153

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

za ta je, amman ta san duk in da Baban Imna zai kaita in da za ta samu natsuwa ne amman ba auranta ba ne ya mutu gidan ne kawai ta fahimci alheri ne ta bar shi. Shi amfanin zama da mutane lafiya yana da kyau haka makota ke ta sharan hawayen barin Inna anguwar nan saboda kyawawan hallayanta wasu har suna fa in ita ce Alherin gidan wanzamai wasu kuma su ka ce tunda Innar Mu'azzam ta bar gidan nan Sun daina shiga gidan daman saboda ita ce mace mai kirki da karamci mai zumunci duk abin da ya faru in dai ta ji sai ta je abun kaico kaico da abun Allah ya sanya alheri ga hannun kyauta ga son mutane da mutumci hatta da su Gaje sun koka wlh, Baba Danjuma duk jikinsa ya yi sanyi amman shima gwara haka ita kuma Magajiya ga ta ga gidan sai ta zauna. A gaban mota Inna ta zauna su Walida har da Mariya da tana kuka ta ce za ta bi su ta ga in da za su koma suka shiga baya, Sai Baba Danjuma ya ja mansoor gefe yana tambayan shi in da zai kai Inna?. Kai tsaye ya ce" Gidana za ta koma Baba." Cikin mamaki ya ce"Gidan ka? To kai fa? Mirmishi ya yi kafin ya ce" Kada ka damu Baba, zan iya siyan wani gidan ko na gina wani, Allah ya rubuta daman gidan zai zama na Inna nw wata rana.". Sai kawai Baba ya dafa kanshi yana ta saka masa albarka. Makota kuma ma su jajen tafiyar Inna ta ce duk su yi hakuri in har ta ga in da suka koma za ta sa Bintu ta zo ta gaya musu sai su zo su ga in da take amman zumunci ba zai yanke ba. Haka aka yi dafifi wajen motar Mansoor suna agama makota hannu suma suna aga musu, hatta su Baba Sani sun kasa motsi kamarin ya girgiza su, Magajiya na cikin gida ta kasa fitowa domin ta rasa me ke mata da i, Zuwaira na fadin daman ya san yana da in da za kai uwar tasa ya barta anan ta ce ma magajiya ai gida ya zama naki yanzu, Saddiqu kuma sai kumfar bakin sai ya auko ma Mansoor yan daba sun yi masa dukan tsiya yake yi Matarsa kuwa ta ja jikinta aki ba ma wanda ya ara ganinta tuni aka manta da dukan ciki ballantana maganar zuwa asibiti. Magajiya aki ta shige, tana zaune Zuwaira da Saddiqu suna mganganu amman ba ta sauraransu ita ka ai ta san hqlin da Zuciyarta ta ke ciki. Kamar ta ora hannu ta rusa ihu. Ga shi dai Meri ta bar mata gidan amman ta kasa farinciki sannan ji irin yadda Mutane suka taru suna kukan tafiyarta wai har da su Gaje, sannan ita me ya sa ta kasa farinciki? Ina za ta koma? Ko dai gidan shi zai kaita? Ta na hasaso wanman katon gidan domin lokacin da aka gama ginin Danjuma ya matsa sai da su ka je gidan suka saka albarka, in dai Meri ta koma wannan gidan ai ta ci gaba ita kuma ta bar ta a gidan gado? Kamar ta saka kuka haka take ji Kallon Zuwaira ta yi Idanuwanta sun kala sun jajir kafin ta ce"ina Mariya? Saddiqu ya ce"Kila ma ta bisu, tunda daman ba ta da kishi, duk irin su Auwalu ne." Sai Magajiya ta yi tagumi domin ta rasa kuma wani nazari za ta yi. Ga shi dai gida ya zama sai ita ka ai amman kuma ba ta jin farinciki sab oda tunanin in da Meri za ta koma ya fi in da ta ke sau ari da saba'in keman ita ta ci gaba ita kuma ta na nan a waje aya. Duk mganganun da su Zuwaira ke yi ko aya ba ta ji ba, ta yi nisa cikin tunanin makomar rayuwarta a wannan gidan ga shi dai burinta ya cika gida ya zama nata amman kuma a kasan ranta ta kasa farinciki. ***** Bangaren su Inna Meri kuwa daga nan ofar gidan Wanzamai sai gidan Mansoor, dake anguwan Tunfere, Ya nan a yadda yake kamar sabo tunda ba zama aka yi a gidan ba shi ne kuma regular ne wata rana ma ya na cinye satin shi a Camp. Bintu ya ba ma Key din gidan ta bu e shi kuma ya riko Inna Meri har tsakiyar falon gidan da ba komai sai katon tibi da cafet, Inma sai kallon gidan take yi, Bintu da Walida kamar za su suma saboda da Gidan akwai kura saboda ba mutane a ciki amman komai sabo ne. Sannan gidan 4Bedroom ne, Sai daga waje haraban parking in da mashin insa take sai akin megadi da wani aki daga waje sai Fulaowin da ya shuka suka arama gidan kyau a ciki akwai katon Kitchen sannan kowani aki akwai Tiolet a ciki daman a cikin aya yake zaune aya kuma ya saka kayan motsa jiki. Sai ya ce ayan su share ma Inna ayan kuma Walida ta zauna a ciki kafin ya san in da zai kai kayan shi. Su kam ai suna can suna faman zagaya gidab suna murna daman sau aya suka zo gidan tun bayan an gama shi tun lokaci suke santin gidan. Mariya ma ji ta ke yi kamar ta dawo nan itama su zauna tare da Walida. Inna Meri na tsaye ta kasa zama idanuwanta sun ciko da hqwaye, Mansoor ya zo ya ri e ta yana fa in"Inna ki zauna mana, an juma za'a kawo sabbin kujeru da sauram kayan amfani in sha Allahu." Inna kamar ta yi kuka ta ce"Baban Inna wamnan gidan ya yi mana girma da haya ka kama min" Cikin Mamaki ya ce"Haya kuma Inna? Wani irin haya kuma? Ina da gida kuma sai ace mahaifiyata sai na ne man mata haya? Inna na rike hannunsa ta ce" Kai fa? Ina Binta za ta zauna in ta dawo?. Mirmishi ya yi mata sannan ya kamata ta zauna saman Cafet shi kuma ya zauna a gabanta yana fa in" Inna ina da ku in da zan iya siyama Mimi wani gidan ta zauna ko na gina mata wani, amman daga yau wannan gidan ya zama naki halas malak Inna." Inna Meri ta fashe da kuka tana fa in" Allah Sarki haihuwa mai rana Na gode kwarai Allah ya yi maka albarka, don Allah Baban Inna zan ro e ka wata alfarma." Ta fa a tana riko Hannuwansa duka biyun da sauri ya ce"Fa i koma menene ni kuma Zan yi miki shi in har bai gagareni ba." Inna na hawaye ta ce"Kukan farimciki nake yi Baban Inma ba na ba in ciki ba. domin haihuwa ta min rana Ubangiji ya gama min komai. Ni kamin komai wlh na gode amman ina so kaima na ga ka samu Farinciki Don allah ka manta komai ka je ku daidaita da matarka ka dawo da ita ku zauna domin kaima ka samu farinciki ka tara zuru'an da za ka yi alfahari da su sannan ka samu rayuwa mai inganci Baban Inna" Inna ta gama fa a tana hawaye Sai Mansoor ya share mata hawaye kafin ya ce"Ina sha Allahu Inna, ba saboda mganarki ba ni da kaina nake son na dawo da Mimi in sha Allahu." Haka Inna ta ji da i ta rika saka masa albarka tana hawaye. Su Bintu ya kira yac e ta bishi su je gida su kwaso kayan sawan su, Inna na zaune ta ce" Har da ma sauran kayan amfanin ai ba sai an siya wasu ba." Shi kuma ya ce a'a ta bar musu gidan da abib da ke ciki kayan sawan su kawai sai abin da suke so za su auko Inna ba ta da abin cewa sai fatan alheri kawai. Daman kuma tuni Bintu ta kira su Yaya Amina ta gaya musu abin da ya faru mamaki ya kama su suka ce ga su nan zuwa, Da Bintu ka ai a ka koma can gidan ita ta ha o duka kayan sawan su Inna da duk abib da za su bukata har da kayan amfanin gida su mopper da botikai da sauran su sannan ta saka key ta kulle akin, daidai sai ga Yaya Halima daman sun yi waya ta ce tana gidan ta zo aukan kaya gidan shuru ba motsin kowa kamar ba nutane. Bayan mota sai da ya cika da kaya da booth, sai Yaya Halima ta bi Mansoor ita kuma Bintu ta hau adaidata suka isa can gidan Yaya Halima ta samu Inna na ta sharan kwallah ta fara mgana sai ta ce ke ni kukan da i nake yi Halima sai dariya kuma gabadayan su nan da nan suka mike suka fara gyaran gidan ba da ewa sai ga Yaya Amina ma ta ariso. Mansoor kuma ya ce bari ya je ya dawo Junior na ta murna ya ga irin gidansu na Kano. Tun da mansoor ya tafi sai bayan la'asar ya dawo ya je ya yi wanka ne ya sauya kaya ko da ya dawo ma sun yi dubaran yin girki Tunda Bintu ta taho da kayan abinci da gas tunda daman Inna na da shi ita ce ba ta cika amfani da shi ba. Sai ya ji da i daman yana can ya na tunaninsu sun yi waya da Mu'azzam ne wanda ya ce Auwalu ya kira shi ya fa a masa ga abib da ke faruwa sun yi mgana sabbin kayan gidan da za'a saka ma Inna suna gama waya Mu'azzam ya tura ma masa 100k yace a kara da shi ai ko ya sha fa aa domin Mansoor ya ce shi bai ce ya kawo wani abu ba, shi kuma ya ce ai Inna mamansu ce ga adaya shima ya na neman albarka sai bakin Mansoor in ya mutu. Nan ya ce su Yaya Halima su zauna su rubuta duk abib da za su bukata na kayan amfani gida oabulai kayan gadaje da Kujeru kuma ya ce har da su duk su je su za o Atm dinsa na babban bankin sa First Bank ya damka musu su kuma su ka ce tunda yamma ta yi sai da safe za su yi sammakon
Chapter 153 · 0% Book details