Sashe 4
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
san Halinsa ai tunda a akin Inna Meri suka yi yaye, bai damu da kankantarsu a lokacin ba, da sun fara ma Inna kukan banza in da yazo gidan sai ya zane su. Da suka gane shi suna ganinshi suke shiga taitayinsu yara ne yan shekaru biyar zuwa shidda. Sai da suka Shige Inna Meri ta fara fa a masa cewa Bintu ce ta kira waya ta ce Walida tazo ta na son ganinta ashe wai fa a tayi da miji da kishiya shi ne ya sa ta ce Walida ta tattaro yaran ta kawo mata su yi kwana biyu a hannunta Cikin takaici ya xe"To Inna makarantar su fa? Inna ta ce"Walida ta ce ko an basu hutu, sai ranar litini za su koma, Bintu finitinanniyar yarinya ce Baban Inna ba ta jin mgana tunda Basiru ya aureta wlh bai huta ba, ta addabeshi ta addabi matarsa, kuma shi yana jin kunyar Babanku ne shi ya sa yake raga mata amma al'amarinta sai kara gaba gaba kawai yake yi, Walida ta gaya min ta ce sanda ta shiga gidan Bintu na tsakar gida tana na bala'i uwargidanta na cikin aki ba ta fito ba amma haka Bintu ke zage zage kamar iyar maguzawa." Mansoor ya yi shuru na wani lokacin yana jin Inna na fa in "Ku shiga mganar kai da Mu'azzam Babanku bazai iya da fitinarta ba." Sai kawai ya jinjina kai kafin ya ce"Ko Bintu ta fara hauka ne ba mu sani ba Inna? Inna meri kamar tayi kuka ta ce"To ga dai shi, abubuwan da take aikatawa ba na masu hankali ba ne." Kai tsaye ya ce"Inna laifin ku ne, kunsan cewa Bintu bata san ilimin zaman aure ba me ya sa kuka aurar da ita? kuma shima Bashir in wawa ne kamar shi yana namiji ashe ban sani ba sakarai ne? ta ya ya yana namiji zai zauna mace arama kamar Bintu na juyasa? Ita ke auransa ko shi ke auranta? Ya karishe fa a cikin acin rai, yana jin takaicin yanzu nan in ransa ya aci sai ya ta ka ya je har gidan ya ci mata mutumci tunda ya fahimci ta fara zama mahaukaciya. Ganin ya fara harzuka ya sa Inna Meri ta sausauta tana fa in"Ka bari zuwa gobe ka kira shi Bashir in da ita kanta Bintu ka ji abunda ya faru, nima ban ce ka raga mata ba, ka ci min mutumcinta tunda sakara take mara wayau." Karamin tsaki ya ja kafin ya walama Walida kira ta fito da sauri tana fa in gani yayammu. Idanuwansa har sun fara sauya launi ya kalleta yana fa in"Me kika je kika iske Bintu nayi a gidanta? Walida ta ce"Sai fa aa ta ke yi tana zage zage wai duk wanda yaci amanarta ba ta yafe ba tac e na tafi da su Hassan sai Yaya bashir ya gane bashi da wayau." Inna Meri tace"Kai Jama'a me Bintu take son zama ne ni Meri? Shuru ya yi yana wani tunani, bai auka haukan Bintu ya kai haka ba. Yana ji Inna na fa in "Fitinar Bintu ya yi yawa, fitannannu biyu Allah ya bani cikin ya'yana da kai da Bintu kai na samu saukin naka Fitinar itace yanzu take son kasheni da bakincikinta." Da sauri ya ce"Ki daina ha aani da ita Inna ni halina ba irin na Bintu ba ne, wannan fa mahaukaciya ce." Inna Meri tace"Hmm ka ma fita, yanzu ne ka daina jawo fitinar da ta fi karfinka Baban Inna." Ya na jin ta auko wannan mganar ya yi saurin mikewa ya fice yana ce mata an kira sallar Isha'i zai je ya yi sallah ya dawo. Daman tasan bazai zauna ba, shi da bayason mganar kwata kwata. To kuma gaskiya ne shi ai fitinarsa ba mai iya kwantar da ita sai Allah. Ga bakar Zuciya kamar Kuturi ga kafiyan tsiya ita fa tana ganin Bintu ko kama kafar Baban Inna ba ta yi ba wajen fitina da taurin kai. Shi zata iya cewa ta wajen dangin Ubansa ya auko wannan hallayar, ita Bintu fa? Ta rasa gidan uban da ta auko hallayan fitina da rashin son zaman lafiya. Tana jin Walida na fa a mata akin Bintu duk an fasa kwalaben turaren wuta tana tunanin kila ma dambe tayi da yaya bashir in kafin ya fita. Inna Meri ta mike tana fa in"To Allah shi ya ye ma Bintu wannan bala'in bani iyawa da halinta ni kam in ya gaji shi basirun ya sakota ta dawo gida ta zauna." Daga haka ta mike ta shige ciki domin ta da sallah. Su Hassan sun yi barci ba mugun wasa. A can masallaci Mansoor ya ha u da Baba da abokinsa makocinsu Mallam Hashimu, albarkacin Baba yasa suka dawo masallaci tare da su Baba Sani, a kofar gida suka tsaya wannan yace bashi da abinci Baba sani ke fa in ko wayan hatsi babu a bangaransa Mansoor ya taimaka masa. Baba Danjuma na gefe kamar ya saka kuka gaba aya an uwansa sun zubar da kimarsu da Allah ya basu, sun koma maula wajen wanda ya ke matsayin a a wajensu. Bai ce bazai ba su ba, kudin da ke Jikinsa duka ya kwashe ya ba su 20k ammh ya ce musu in ya dawo zai ara musu, suka kar a ko Godiya domin sun raina abunda ya ba su. Ko kunya suka wuce bangarensu Baba anjuma ya sauke Numfashi kafin ya ce"Ka yi hakuri Mansoor kaji ko? Kansa na kasa ya ce"Haba ba komai Baba suma iyayena ne yadda zan yi maka abu suma suna da ha in na yi musu." Jinjina kai kawai Baba anjuma ya yi yana ta saka albarka. A kofar gidan suka tsaya Mansoor in ya kawo masa mganar Bintu. Baba Danjuma ya ce"To ni sha'anin Bintu ya fara isata yarinyar nan ba ta jin mgana." Mansoor yace"Baba ba ita ta haifi kanta ba. Ubanta zata ci wlh tunda na lura ba ta da hankali." Baba anjuma ya ce"To kila kai in ka yi mata magana ta gyara, ammh ni da Meri har mun gaji da yi mata nasiha mun yaleta, yaro nan kunyata yake ji shi ya sa bai auki wani mataki akanta ba, ammh sha'anin Bintu ya wuce hankali, kwata kwata ba ta daraja mijinta ta zame ma sa fitina a gidansa." Mansoor jinjina kai kawai yake yi yana tunanin gobe daga studion gidan Bintu zai wuce yana so ya ga Iskancin da aka ce tana aikatawa ne. Ga shi shegiya bata san komai ba sai hauka, ya'yanta ma ba ta iya kula da su sai dai ta kawo ma Inna ta dinga wahala da su, to a gobe zai saka Walida ta maida mata ya'yanta in bazata zauna da ya'yanta ba to ta aika su wajen kakarsu ta bangaren uba, Amma ba gidan su ba. Tare suka shiga gida da Baba anjuma, ranar Magajiya ke da Miji tana ganinsu tare ta fara masifa tana manganganu ganin haka yasa Mansoor bai tsaya akin Baba Danjuma dake tsakanin Korodon Inna Meri ba, sai ya shiga falon Inna Meri ya zauna Walida ta zuba masa tuwon masara da miyar kuka yana ci sun a hira da Inna har ya kamallah yace kuma a ijiye masa umame da safe in ya dawo training zai shigo ya ci. Karfe goma ya bar gidan ko akin Baba Danjuma bai leka ba tunda Magajiya na ciki yana shiga sai kuma ya jawo tijara, tunda ita kam tun yana arami yasan ta tijararriya ce ba ta raina abun mgana musamman ma shi da ta ke ganin ba an gida ba. Ya isa gida goma da rabi, da ne ya kan zauna majalisar su matasa a anguwansu amma yanzu majalisar ba kowa, dukkansu sun kama kansu wasu sun yi aure wasu kuma ba ma a garin suke sana'ar su ba ya na jin daga shi sai Nasir sai makama suke garin Gombe. Nasir kuma ya yi aure sannan anguwar da ya ke zaune da matarsa akwai nisa a tsakaninsu sai su jima basu ha u ba. Makama ne ka ai da shi suka rage ba su yi aure ba, ko kuma ya ce shi ka ai ya rage tun da Makama an kusa bikinsa ma'aikacin bankin First bank ne, shi ya sa in ya shiga anguwan sai dai ya zauna a gida ya yi hira da Inna ko Baba ya ci tuwo ya fito ya koma gida ya kwanta. Shi kanshi yasan rayuwarsa ta sauya, abubuwa masu dama sun sauya daga rayuwarsa. Mafarkinsa, burinsa da komai nashi ya sauya, shi ya sa yake jin kansa kamar bashi ba. Tabbas Mansoor Ajin yanzu ba shine Mansoor Aji a shekaru goma da suka ga ba ta ba. Wannan wani sabon Mansoor ne, wanda ya rasa mafarkinsa da burinsa wanda rayuwarsa ta juya daga farinciki zuwa ba inciki. ****** Washegari. *Karamchi Tv* 11:30am. Yau ba ita zata karanta labaran dare fa Salim Bunza ne, shi ya sa bayan ta gama karanta labaran safe ta tattara sauran takardun hannunta zuwa Office in manajansu bangaren labarai da al'amuran yau da kullum na gidan talabijin na karamci. Mai alhakin editer in su ba musulmi ba ne Peter tare da shi suka je wajen manaja tunda ranar lahadi da safe za su gabatar da shirin sharhin labaran karshen mako ita da Salim. Ta ji ma a wajen Manaja suna magana har peter ya fito ya barta sai daga baya itama ta baro bangaren zuwa rest room ma'ana akin hutawarsu. Babban aki ne mai cike da kayan alatu kamar falon wata mace, ga A.c ta ko'ina ga tuma tuman kujeru da suka zagaye wajen ga firiza domin sanyaya makoshin ma'aikata. Sanye ta ke da Abaya mai ruwan ash colur sai ta saka mayafin Abayan ta yi roling in shi a saman kanta. Kafarta sanye cikin takalmi sahu ciki kafin kaga Mimi da takalmi na sahu waje sai ka ganta da sau ciki sau goma. Tana son takalma masu rufi sosai, jakarta karama kalan takalminta ash mai duhuwa, a can ta samu debora mai kula da shashen bangaren kula da masu shirye shirye ita da Na Misau suna hira. Zuwan ta ya sa aka cigaba da hiran da ita, duk da jefi jefi hankalinta na kan wayanta Mimi bayan aikinta sai