Sashe 2
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
don yana wallo sai ya yi mata wannan tozarcin wallahi ya ci sa'a ya bar wajen nan da sai ya raina kansa wlh." Nasir ne ya ara ba ta amsa kai tsaye da cewa" Sai dai ki raina kanki, ke baki ga abunda ya yi ma ita awar ta ki ba ne,? Rukky za ta kara magana Usman ya tare ta da fa in"Ki yi hakuri Anty Baby ko an yi miki bayani ba za ki gane ba, Aji abokina ne tare muk tashi dukkanmu nan tare muke wannan kuma da kike gani aninsa ne Mu'azzam" Ya fa a ya na nuna mata Mu'azzam wanda ya yi shuru kamar ruwa ya ci sa. Cikin ufuluwa Rukky ta kallesa kafin ta ce" Miye ha an uwanka da awata da har yake da damar zai mata wannan wulakanci.? Sai ya kasa ba ta amsa Nasir ne ya ce" Ala ace mai karfi a tsakaninsu ko ke ba ki gane haka ba? to tsohuwar budurwansa ce bayan wasu shekaru yau suka ha u shike nan kike son ji? Ya fa a ya na mai kureta da ido, ta kasa mgana saboda mamaki dai dai lokacin da Mimi ta kariso wajen jikinta kamkame da rigar da Aji ya ba ta kamar wani zai wace mata. Tana zuwa wajen ta saki baki tana kallonsu cikin mamaki ta ce"Su waye nake gani haka? Ai ba za ta a mantawa da su ba sai ta tuna islamiyan mallam Dahiru cikin bu e baki tare da murnan ganinsu ta fara nuna su aya bayan aya. ****** Me ya faru kike kuka? Ko ba ki da lafiya ne? Ya jefa mata tambayoyin a tare sai ta yi masa banza kamar ba ta ji ba, sai ma ta ara gyara kwanciyarta, har ga Allah ya auka da gaske ba ta da lafiya ne. Sai ya fara takawa zuwa gabanta lokaci aya yana fa in" Don baki da lafiya shi ne ba za ki iya mgana ba? Kuma don kuma sangarta sai ki zauna kina ta kuka kamar wata aramar yarinya?. Wani ulilin ba inciki ya turniketa wato bai ma san abunda ya aikata ba har yana okarin fa a mata mgana. "Ko saboda kina ganin kin fi kowa gata ne shi ya sa za ki zauna kina ma mutane kuka? ko da yake ai yar Major ce sannan iyar ar lauya ce an riga an shagwa a ki shi ya sa in kina ciwo ma ba za ki iya mgana ba sai dai kuka." Kai tsayen shi ya fa i haka, Ita kuma sai ta ji kamar wani abu na tunkaro zuciyarta idanuwanta suka rufe saboda bakinciki ba ta san ta mike ba sai ganinta ta yi tsaye kan kafafunta a gabansa idonta ma ya rufe saboda acin rai cikin aga murya ta ce"Ya isa! Na ce ya ishe ka haka Mansoor." Sai kuma kawai ta saka kuka ta koma ta zauna har da shessheka. Mamaki ya kama shi kawai sai ya bu e baki ya na kallonta kafin ya ce"Ikon Allah! daga magana? me na yi miki? Ko don na ce iyayenki sun sangartaki? to arya na yi? E, mana ai sun sangartaki da gata shi ya sa kike wani abun kamar wata aramar yarinya, ban da haka ba ki da lafiya ba sai ki yi mgana ba, ga mutane a cikin gida in ni ba za ki iya kirana ba? a ya na tsareta da ido ganin kukanta ya fara fitar da sauti, da sauri kuma ya aura da cewa"Ke ya isa mana, me ke damun ki ne?. Ai kamar ana ara ma mata kaimi sai kawai ta ara fashewa da kuka, sai ya matsa baya lokaci aya yana aga hannunsa sama kafin ya ce"To na gane, Allah ya baki hakuri ki yi a hankali kar Inna ta jiyo kukan ki, ko da yake na Inna mai sau i ne, Kar daga gidan ku a ji kin yi kuka yanzu nan na ji kiran sammaci daga kotu, shi mai barazana da sojoji ya tafi in da ba a dawowa ballantana ace zan yi kwana zaune." Yana gama fa in haka ya juya zai fita sai ta ji kamar ta tashi ta sha o shi sunan mahaifan nata ne abun kira a wulakance a wajen shi? ***** Ya yi okarin ara kiranta ya fi sau goma ya na fasawa ana sha aya ne wayar ta shiga, kuma sai ya ji girmansa na fa a masa ka kirata ma ta aga kiran ka kuma ba ta kira ka daga baya ba, sai kuma kai ka sake kiran ta? ta ma isa kenan. Sai kawai ya kashe wayar ya na huci amman abun mamaki sama da mintina goma Mimi ba ta biyo bayan kiran shi ba, abun sai ya ara ata masa rai. Sai kuma wata zuciyar ta ce ka kira ta ka ji dalilinta na yi maka wannan wulakancin, sai kuma ya kira har ta shiga sai ya kashe. Ya yi haka yafi sau biyar. A bangaren Mimi kuma duk kiran nan da Aji ke yi mata ya na kashewa wayarta na hannunta kuma tana gani, kiran farko ma da ya yi mata har sau biyu ba ta auka ba domin haushin shi take ji har ga Allah, Shi ya sa ba ta ga amfanin kiran nashi yanzu ba, ta tafi Abuja wajen mahaifiyarta amman bai ta a kiranta domin ya ji yadda take ba sai yanzu? Ai ya baro shiri tun rani shi ya sa taki aukan wayarsa kuma sai da suka bar gidan sannan ta fito daga cikin akin. Tunda ta fahimci kowa abunda yake so ya ke yi itama abin da ta ga dama shi za ta yi ba za ta ara barin sa ya takura mata ba. shi kanshi Ajin ya fara fita daga kanta ta ji ta na bukatar zama ta yi tunanin wata mafitar domin mai rai ba zai dauwama cikin rayuwar da ba ta da amfani ba. Kuma yadda yake kira yana kashewa yasa tasan rigima yake ji, ita kuma ta ce ba za ta kira ba in ya gaji da girman kansa da kamewarsa sai ya kira ita kuma tana dai dai da abunda ya zo da shi. Shi ya sa sai da ta bari ya ara kira ta yi sauri ta aga kiran. "Hello! Lafiya kake ta kira kana kashewa? In ba ka yi ra'ayin kira ba ne, me ya sa dole sai ka kira? Sai jin muryan Mimi ya yi daga sama. Sai ya ji wani iri a cikin ransa, kamar ma ya kasa magana amman kuma bai kamata ya nuna ya gaza ba. Kai tsaye ya ce" Eh ban yi niyyar kira ba, ke me ya sa ba ki kirani ba? Ko ba ki ga missed call ina ba ne azu? Cikin gadara Mimi ta ce" Na gani mana, na auka ba ni kazo kira ba, shi ya sa ban biyo bayan kiran ba." Aji ya yi shuru ya na jin yadda Mimi take masa mgana cikin isa sai kawai ya girgiza kai kafin ya ce"In da ban yi niyyar kiran ki ba, ke ba ki isa ki saka ni na kira ki dole ba." "Na sani, shi ya sa na da na ga kana ta kira kana katsewa ban damu da na biyo bayan kiran naka ba." Ya na mamakin yadda bakinta ya bu e haka, ita ko cikin uwar akin Yaya Amina ta ma ale ta samu damar maida masa da Martani. "Yaushe za ki dawo? "Sai ranar da na ga dama." Baki bu e Aji ya ce"Mimi..! " E! Kai kace naje sai ranar da na ga dama sai na dawo, to ka bari duk ranar da na ga daman sai na dawon ko? Ya kasa mgana sai kawai ya ji ta ce. " Sai da safe." Kafin ya yi wani yun uri ta kashe masa waya a kunnensa, Aji ya yi wani sansarerai kamar mara kuzari yana faman tuno maganganun Mimi yanzu yanzu nan. Duk kuma saboda bai bita Abuja ba, ransa ya ara aci saura ka an ya ha a wayarsa da bango sai ya fasa ya koma yana harbi Iska da Kafafunsa alamun acin rai shima Allah ya ara masa me ya sa ya damu da ita da zai kirata? Ta yi ma kanta in ma rigima ce ita ba ta san shi ya san kan rigima ba. To ai sai su zuba su gani tsakanin shi da ita zai ga waye zai yi nasara. ****** Idanuwan Aji sun rufe gani yake kamar abunda ya faru a shekarun baya ne zai kara faruwa a yanzu, ita kuma Mimi wani irin kuka take yi ganin yadda Aji ke mgana kamar zai dage ta. Takure kanta ta yi a jikin wardrpe akin lokaci aya tana fa in" Me ya sa kai ba ka yafiya ne? Ya yi nadaman abunda ya faru, Hajiya da Mommy sun zo sun nema masa gafaran ka? na auka ka manta na auka ka hakura na auka ka yafe masa sabo da ni ban dauka har gobe kana kallona da wannan abin da ka san nima ba'a son raina ya faru ba. Me ya sa kai ba ka da afuwa ne? Kai ma ai an adam ne kana laifi sannan Ubangiji mai rahama ne mai jin ai yana yafe maka dukkan zunuban ka, me ya sa kai ba za ka yafe masa ka manta baya ko saboda ni ba, ko saboda darajan soyayyar dake tsakanin da kai" Take fa a tana kuka riri, sai dai kawai ta gan shi a gabanta ya saka hannuwansa ya tare gefe da gefen da jikin wardrope in da take jingine cikin tsawa ya ce" Kin ta a ganin an fasa gilas sama da shekara goma rana tsaka a zo a ce za'a yi masa gyaran waskwarima? Ai ko an gyara shi ba zai ta a komawa dai dai ba, ban yafe mishi ba kuma su ma na fa a musu ban yafe masa ba, kuma zan iya yafe masa saboda ke ba." "To ai ya rasu, kuma ya tafi in da ni da kai wata rana za mu je can, miye amfanin wannan abunda kake yi don Allah.? Irin kukan da ta ke yi bai saka ya saduda ba sai ma buga wardrope in da