← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 208

Sashe 130

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

marigayi Sulaiman Dabo da taimakon kwatancen da ta yi masa. Ta sauka ta ciro ku in sa a cikin jakar dake hannunsa ta bashi ya kar a yana ta mata godiya ganin ta ba shi har dubu aya sannan ba ta tsaya yin mganar kar an chanjin ba har ta kai jikin get in gidan ta fara bugawa. Megadi na zaune ya ji ana ta buga gida sai ya taso zai bu e amman yana tambayan waye?. Cikin Sha ewar murya Mimi ta amsa masa da ita ce Binta ce, da sauri ya bu e karamar Kofar sakamakon akwai hasken wai wuta a wajen sai ya samu sararin ganin fuskarta tar da ta yi wani ja ja alamun ta sha kuka sannan Idanuwanta sun yi jajir sun kuma tasa. "Binta? Ke ce tafe da daddaaren nan? Ya fa a cikin mamakin ganinta. Domin har bayan ya le a bai ga motar ta ba sannan bai ganta tare da kowa ba, halin da take ciki ne ya sa ba ta tsaya ma sauraran megadin ba ta wuce shi da Sauri zuwa Kofar da za ta sadata da falon Hajiya, shi kuma sai ya bi ta da kallo domin wannan zuwan dai daga yanayin Bintar ma za ka fahimci ba Lafiya lau sai ya fara tunanin ko dai wani abu ne ya samu Hajiya? Gabansa ya fa i a sarari ya furta" In sha Allahu khairan." Kofar falon a rufe ta ke sai da ta buga, Baaba Uwani akin na falo ne amman ba ta ji bugun kofa ba, ta yi aikace aikace ta gaji daman tana da nauyin barci, Mimi har ta ga ji da buga Kofa ta dakata tana okarin lalubo wayarta ta kira lambar Hajiya. Sai ta ji kamar ta shin magana daga cikin falon, Ashe Hajiya ce ba ta yi barci ba ta ji bugun Kofa Daga akin ta shi ne ta fito ta le a ta na kiran Sunan Baaba Uwani sai da ta tashi Sannan ta ce ta ta je ta bu e Kofa ta ji kamar ana bugawa. "Buga ofa kuma Hajiya? Baaba Uwani ta fa a da sigan tambaya ta na kallon Hajiya. Lokaci aya kuma tana duba agogon dake cikin akin da ya zama nata tun farkon zuwanta gidan. Karfe 11:04pm dai dai na dare a lokacin. Hajiya na tsaye a kofar akin ta ce" Fito ki Saurara ki ji, ni dai tabbas na ji ana buga Kofar falo." A tare suka umgumo zuwa falo dai dai lokacin Mimi ta ara buga ofar sai Baaba Uwani ta kalli Hajiya itama sai ta kalleta gabansu a tare ya fa i, Hajiya ta yi Saurin cewa" Ko dai Hamza ne? Allah yasa lafiya hanzarta ki bu e Uwani." Baaba Uwani jikinta na an rawa ta arisa wajen Kofar ba ta bu e ba sai da ta fara da tambaya. "Waye?.." "Ni ce Baaba Uwani!" "Ke ce wa? "Bintu ce Baaba Uwani.." Mimi ta fa a lokaci aya tana okarin maida kwallar da ta taso mata, Hajiya na bayanta ta ji muryan Mimi, Baaba Uwani ma sai daga baya ta gane muryanta jiki da zuciya na rawa ta bu e kofar dai dai Hajiya ta kariso wajen tana fa in'" Bintu kuma? da wannan daren? Maganarta ta tsaya ne lokacin da Mimi ta shigo falon.Duk iya kokarinta na kar ta yi kuka ganin Hajiya sai da kuka ya kwace mata kawai sai ta tafi ga Hajiya ta fa a Jikinta ta fashe da kukan da take ta ri ewa mai karfi yana kuma fitar da sauti, kukan zafin zuciya ne, kukan abin da kake tunanin kana so ashe shi tunanin shi ba shi a kan ka, kukan takaici da ba in ciki wanda ka yi ma soyayya gaskiya shi kuma a na shi bangaren ba haka ba ne. "Innalillahi wa'inna alaihirraju'un! Hajiya arama lafiya kuwa? Baaba Uwani ta fa a cikin tafa hannayenta, Hajiya kuwa daman tuni take ta salatin ta a cikin ranta, ammam Mimi ba ta san suna yi ba ta kamkame Hajiya tana ta kuka nan tsayen ta saki jakar hannunta da mayafin jikinta kayan barcin dake jikinta suka bayyana Sai baaba Uwani ne ta duka ta auke mata sai faman salallami take yi. Ita kuma Hajiya sai ta ri e Mimi cikin Kwantar da murya ta ce" Binta Allah ya sa lafiya? Ko wani abu ne ya samu mijin naki? Sai ta girgiza mata kai alamun a'a Hajiya ta ara tambayanta ko wani abu ne ya samu Merin? Nan ma ta ce a a. Gaban Hajiya na fa uwa ta ce" To me ya faru kika biyo wannan daren ke ka ai kina kuka? Ko wani abu ya faru tsakanin ki da mijin naki ne? Jin haka ya sa Mimi ta ara sakin kukanta lokaci aya kuma ta rabu da jikin Hajiya ta kama hanyar akinta tana Cigaba da kukanta kamar wacce a ka ce mata an yi mutuwa. Hajiya da Baaba Uwani suka bita da kallo, Baaba Uwani ta yi wani iri tana duban Hajiya kafin ta ce" Hajiya me ya ke faruwa? Hajiya ta yi shuru kafin ta sauke numfashi Tana fa in" Ban sani ba Uwani, amman mu ba ta lokaci ta samu natsuwa zuwa da safe mu ji, in taki mgana sai na nemi ita Merin naji abin da ya faru." Baaba Uwani ta ce a sanyaye" Hakane Hajiya, To Allah ya ijeshemu alheri." Hajiya ta amsa da Amin Amin amman Jikinta na ba ta wani abu ne gagarumi ya faru haka nan Binta ba za ta zauna tana wannan uban kukan ba. Kar an kayan hannun Baaba Uwani ta yi ta bi bayan Mimi ta auka tana akin ta sai ta isketa nan saman gadon ta ta dun ule tana faman kuka. Hajiya ta shigo akin ta maida Kofa ta rufe sannan saman kujera wara ayan da ke cikin bedroom in ta ijiye mayafin Mimi tare da jakarta sannan ta karisa bakin gadon ta zauna tana faman kallonta amman kamar ba ta san tana akin ba kuka kawai take yi mai karfi kamar ranta zai fita. "Fatima.." Hajiya ta kira sunanta cikin taushi. Amman Mimi ba ta amsa mata ba, kuka kawai take yi. Sai kawai Hajiya ta mi e kan madubin da ke akin ta isa ta auko wayarta lokaci aya tana fa in" Tun da i mgana ballantana nasan abin da ke faruwa bari na kira Meri, ila ita s ta fa amin abin da ya fito dake daga gidan mijin ki, kika zo nan kina ta min koke koke" Ba ta san lokacin da Mimi ta sauko daga kan gadon ba sai ganinta ta yi a gabanta lokaci aya ta warce wayar hannunta. Cikin mamaki Hajiya ke kallonta kafin ta samu zarafin magana Mimi ta ri o duka hannayenta ta jim e cikin nata pokaci aya tana okarin danne abin da ke ranta amman hawayenta ba su tsaya ba. "Hajiya in ro e ki wata alfarma? Na san tun tasowa ta a gabanki kike yi min duk wani abin da nake so, to ina so ki yi min na yau ko da zai zama shine wani abu na arshe da za ki yi min" Mimi ta arishe fa a cikin kuka. Ganin haka yasa Hajiya ta jinjina kai sannan ta ri o Mimin zuwa saman Kujera suka zauna sannan ta saka yatsun hannunta tana share mata hawaye lokaci aya tana fa in" To shike nan daina kukan hakanan kin ji ko?. Sai Mimi ta gya a mata kai, amman kukan na sake fito mata. Kanta na asa ta ara rike hannayen Hajiya tana fa in"Hajiya ki yi min alfarman ba za ki takuraman sai na fa a abin da ya faru ba, kuma ba za ki takuramin sai na koma gidan Mansoor ba." Hajiya ta ura mata ido lokaci aya kafin ta ce" Saboda mene? Sai kawai Mimi ta kwanta a jikin Hajiya tana fa in" Na hakura da AURAN nan Hajiya ba zan iya ba. Wallahi ba zan iya ba." Take fa a tana kuka, Hajiya ta yi shuru kafin tace" An ta a cewa an ha ura da Bautar Ubangijine ba tare da wani dalili ba Binta ba? Ta fa a lokaci tana dafa kafa an Mimin alamun lallashi, Mimi kuma sai kawai ta kara saka ma Hajiya kuka cikin kukan tana fa in" Hajiya ina da dalilaina amman ba zan iya fa a miki ba, ki bar ni a baya ni dai na ce ina so yanzu kuma na ce ba na so Hajiya domin Allah kar ki takuramin." "Ya sake ki ne da kike fa in haka? Mimi ta girgiza kanta kafin ta ce"Bai sakeni ba, amman zai sake ni dolen sa Hajiya." Sai lamarin ya fara ba ma Hajiya tsoro amman ba ta sake mgana ba, ganin irin kukan da Mimi take yi yasa ba ta sake jan ta da wata mgana ba sai ta rumgumeta tana lallashinta cikin taushin murya take fa in" Shike nan ya isa daina kuka ya isa Binta ya isa." Take fa a tana bubbuga bayan ta, Mimi tun tana kuka har ta koma sauke numfashi cikin dashewar murya, Hajiya ta lalla ata ta koma kan gado ta kwanta ta rufa mata bargo kanta ta shafa kafin ta ce" Ki daina kuka. Da safe sai mu tatttauna kin ji ko? Sai Mimi ta gya a mata kai lokaci aya tana jin yar salama tana da tabbacin cewa Hajiya za ta mara mata baya. Dukkansu daga Mimi har Hajiya ba wanda ya samu cikakken barci, Mimi damuwa da bakinciki ne suka hana ta kwanciya, Ita kuma Hajiya tunani da kuma damuwa suka hana ta samun barci da wuri. Ta yanke shawaran da safe za ta kira Hamza domin ya zo ya ji abin da ke faruwa ita a tunanin ta matsala ce tsakanin Binta da mijinta kuma shi aure yana da tsari da doka domin ta ce ta hq ura ba za a barta a zura mata ido ba ya zama dole a yi binciken abin da ke faruwa. ****** Yadda Hajiya da Mimi suka yi kwanan damuwa da rashin barci. Haka Inna Meri ta kwana salla tana kai ma Allah kukanta Hibba da Walida ma sun kusa raba dare ba su yi barci ba,
Chapter 130 · 0% Book details