← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 208

Sashe 3

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya yi da hannuwansa guda biyu ji kake bum! Ta tsorata ta sulale kasa ta auka dukanta zai yi ta kamkame jikinta waje aya. "Kin manta akwai hisabi tsakanin mutum da mutum? Ya yi sanadiyar lalatamin duka mafarkin rayuwata rana tsaka sai ace na yi hakuri bayan an da e da cutar da zuciya ta? me ne laifina saboda kawai nace ina son ki? Soyayyar ce ba ta min adalci ba,ita ce ta ja ni ta kaini inda aka kusa kasheni da rai na, Ina ba zan iya ba, sai Allah ya yi mana hisabi da ni da Mahaifinki, domin ya cutar dani." arishe fa a kamar zai yi kuka domin muryarsa ta fara disashewa. Kan Mimi na cikin gwiwoyiyin kafafunta ta ce" Shi ma ai ba shi da laifi saboda uba yake a gare ni, ba ya yi hakane ba ne saboda son zuciya, ya yi haka ne saboda ya ba ni kariya da kuma sauke nauyin shi na matsayin mahaifina shi ma ba shi da laifi ka yi masa uzuri.." A fusace ya ce" Ban yi masa ba, ba kuma zan ta a yi masa ba, na ce ba zan iya yafe masa ba har gaban ABADA." _*Ban ce ba wanda ya fini ba, amman na ce al alamina na dabam ne, kun gwadani kuma kun ga irin salon rubutuna. Ku bani kyakyawan shaida da ya ini ni kuma zan baku abin da kuke so in sha Allahu. Free page zai fara zuwa muku ranar 10/08/2024 in sha Allahu, sannan kamar yadda tsarina yake book1 kyauta ne ya yin da book2 and 3 zai zo a matsayin paid kamar yadda muka saba. Sannan za ku iya fara biyan ku in karatun ku daga yau har zuwa ranar da zamu gama free pages, babu wasa ko jira a cikin tsarina da ikon Allah cikin ankani lokaci zamu are wannan labarin kamar yadda muka saba*_ _*Na gode da soyayyarku da amincewarku akan rubutuna Allah ya ha amu a Aljanna firdausi Amin Amin.*_ *KAMAR YADDA TSARIN YAKE, BOOK 1 ZAI ZO MUKU A MATSAYIN KYAUTA BOOK 2 TO 3 PAID NE, TSARIN FARKO NA REGULAR GROUP NE N500. SAI TSARI NA BIYU KUMA GIDAN VIP NE, N1K NE, KU FARA BIYAN KU IN KARATUN KU TA WANNAN ASUSUN BANKIN 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK, SAI KU TURA SHAIDAR BIYA TA WA ANNAN LAMOBIBIN KAMAR HAKA* *09069067488, 08032773332, 07030645342* *MASU BUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU A CIKIN WANNAN LABARIN SU TUNTU ENI TA WANNAN LAMBAR* *09069067488* *#Love story* *#Marriage* *#Family issue* *#Janafty* *#01/08/2024* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FpA4NvQPg3XIRUQOgytNh5 y issue* *#Janafty *IDAN AN CIZA..!* *Wattpad:Jamilaumar315* *Arewabooks:Jamilaumarjanafty* *Mallakar:Janafty* *SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA.* *MADALLAH DA SURAYYA DEE, ALLAH YA CIKA MIKI DUKA BURIKAN KI NA ALHERI YA BA KI SANYIN IDANIYA AMIN.* *FATAN ALHERI GA AMINIYATA AISHA MUHAMMAD ALTO(SISINAH), ITA IN TA DABAM CE A WAJENA. NA GAISHE KI* *NA GAISHE DA IYAYEN AKINA* *ZAINAB INUWA(AUNTYSIS)* *HAJIYA LUBABATU MUSA* *KHADIJA SALISU YUSUF(UMMINA)* *HAJIYA HABIBA ABUBAKAR IMAM* *ANTY ZAINAB ABDULWAHAB* *HAJIYA HALIMA ALHA SHEHU.* *ANTY HADIZA MAHE MUHAMMAD* *ANTY SALAMATU ABUJA.* *ANTY FADILA KABIR* *ANTY FIDDAUSI KABIR* *FATAN ALHERI NAGODE* *INA GAIDA MARUBUTA, KARAMCINKU ABUN YA O NE. ALLAH YA ARA BASIRA AN BAIWA AMIN.* *Page 2* A tsakiyar falon ya ci karo da Inna Meri tana tsaye ita da Walida, ya yi sallama suka amsa gaba ayansu. Tun kafin ya bu e baki ya fara gaishe da Inna Walida ta yi zaraf ta ce"Yayanmu barka da dare" Saboda sanin halinsa yanzu tana cewa ina yini sai yace bai ga yinin ba, sai dai ta ce masa barka da dare. Cikin mamakin ganinsu a tsaye ya ce"Barkan mu lafiya na gan ku a tsaye, Innanmu lafiya kuwa? Inna Meri wata bakar dattijuwa kallon farko za ka yi mata ka fahimci ta fito daga shiyar sokkoto ne, sannan ta ha a jini da Arawa, saboda gefen bakinta dama da hagu ga zanenta na Arawa nan aro aro ya bayyana duk da ko ta na ba a na iya ganinsa. Sannan sai alokacin na fahimci in da Mansoor ya auko tsawon sa, Inna Meri doguwa ce sosai mai kaurin jiki kuma. A shekarunta iyakarta 56 zuwa da bakwai a duniya ba ammh yanayin jikinta bai nuna wahala ba sosai tana sanye da hijabi ne a jikinta hannunta kuma casbaha ne, daga gani ta idar da sallar mangariba ne tana lazimi. Cikin yanayin maganarta ta ce"Tun da naji Kwakwazon Magajiya na ce to Baban Inna ya shigo gidan" Mirmishi ya yi ba tare da ya yi mgana ba, Walida tayi saurin shimfi a masa darduma sanin halinsa bai son zaman kujera duk ko da irin tuma tuman kujerun alfarman dake mamaye da falon na inna Meri ko wata amarya albarka. Cikin natsuwarsa ya zauna itama Inna Meri sai ta samu daga gefensa ta zauna saman cafet mai taushi dake malale a cikin akinta. Cikin yalwataccen fara'an da ba a raba fuskarta da shi ta ce" Tun fa azu muke ta duban hanyan ka ni da Babanku muka ji ka shuru." Daman yasan tuni labarin dawowarsa ya zo musu tunda Mu'azzam ya ji labari. Kansa na kasa ya ce"Innarmu kun yi mgana da Mu'azzam ne? Cikin jimami ta ce"Ya kirani kamar ya yi kuka Baban Inna ba ka kyauta ma an Innna ba gaskiya, me ya sa ba ka je ka duba an uwanka ba? Kai tsaye Ya ce"Inna wasa muka je bugawa kamar kuma wani mace sai a ganni daga zuwa wasa ina faman biye biye Inna Meri ta ce"To menene? ba wajen an uwanka za ka je ba? ya ce matarsa ta kasa zama waje aya saboda zuwanka maganar gaskiya Baban Inna ba ka kyauta ba." Ba ya son jan mganar ya sa Ya ce"Shike nan ki yi hakuri Innarmu, Ina Baba ko a masallaci ban gan sa ba? Inna Meri tace"Tun azu abokinsa Mallam Hashimu ya kirasa kan dai zaman da ake yi akan auran arsa maigado shi ne ina ga har yanzu ba su kai ga matsaya ba." Cikin mamaki Ya ce"Auran ya mutu ne? Tana gyara zama ta ce"To abin dai nasu sanin gaskiya sai Allah ita ta ce ya saketa shi kuma ya yi rantsuwan bai furta mata saki ba sun dai yi sa'insa har ya dake ta" Mansoor ya yi shuru bai yi mgana ba, yana ji Inna Meri ta cigaba da ba sa labarin yadda akayi jin ta kawai ya ke yi hankalinsa na wani wajen kuma. Walida ya ke hangowa ta cikin uwar akin Inna Meri ta na karatu sai dai baisan me ta ke karantawa ba. Ya bu e baki zai kwala mata kira kenan Inna ta riga sa, tana fitowa ta kalleta tana fa in"Ke mara wayau baki kawo ma yayan naku ko ruwa ba? Da sauri Ya ce"Ba na jin kishi Inna". Kallonsa ta yi kafin Ta ce"To abinci fa? Kai tsaye Ya ce"Inna zan ci tuwo ammh ba yanzu ba sai na kusa tafiya." Daga haka ta girgiza kanta kafin ta ce"Shike nan kun dawo oafiya ko? Ina fatan an samu nasara? Cikin sakin fuska ya ce"Lafiya lau Innarmu, an samu nasara in sha Allahu." Nan Inna ta cigaba da kwararo addu'o'i yana amsa mata da Amin Amin. Walida kuma tsalle ta buga tana fa "Yayanmu kun ci an kano kenan? eyye na ji da i daman yau a makaranta ana ta labarin wallon da aka buga tsakaninku da yan kanon" Kallonta ya yi lokaci aya yana hararanta kafin ya ce"Ke ba karatu ki ka je yi makaranta ba labarin kwallo yake kai ki kenan ko? Ta na jin haka ta yi sum sum ta wuce ciki Inna Meri ta ce"A'a yalemin Auta, ita ke bani labaran wallon naku ni kasan ba gane abun na ke yi ba, ranar ma a tibi ta ga an nuno wasu ta ce min Innarmu wata rana za ki kalli Baban Inna acikin tibin na ce Allah ya nuna mana." Yana Mirmishi ya amsa ma ta da Amin. Hira suka cigaba da yi Inna Meri na fa a msa ta yi waya da mutanen mallam Sidi sun ce ya ji ma bai je ba Goggonsa yalwa har ta yi rashin lafiya kwanaki. Yana duba agogon fatan da ke hannunsa ya ce"Zan je Inna ba na samun zama ne, ammh zuwa karshen watannan zan ga abin da Allah zai yi." Inna Meri ta ce"Ya dai kamata ko ba ka kwana ba, Mu'azzam yafi ka son zumunci yanzu haka duk zuwan da zai yi garin nan sai ya leka wajen yan'uwan mahaifiyarsa ya gaishesu ka ga hakan ai yafi da ace mutum kwata kwata baya zuwa." Kai tsaye ya ce" Hakane Inna zan kokarta in sha Allahu." Wayarsa a ka kira yana ganin Coach ne ke kiransa ya aga suka gaisa nan ya ke fa a masa gobe da safe suna da morning Training, da kai ya amsa mishi sannan ya sauke wayar dai dai ookacin da ya ji gudu da dariyan yara daga koridon shigowa shashen inna Meri kafin ya yi mgana ya ji Inna na fa in"To ga shugabanin yan kiriniya nan sun dawo." Kafin ma ya samu zarafin mganar sun fa akin da gudu sauran ka an su ture Mansoor dake zaune. Sai da ya daka musu tsawa sannan suka fahimci yana akin. Sai suka natsu sum sum suka koma bayan inna Meri suka tsaya suna fiki fiki da ido kamar za su yi kuka. Inna Meri ta juya ta kallesu kamar tayi dariya sai kuma ba ta yi ba. Ta jawo Hassan jikinta shi kuma Hussaini ya lafe a bayanta. Cikin sigar lallashi ta ce"To sojojin Inna ba ku gai da kawun ku ba." Daga jikinta suka had a baki wajen fa "Kawu ina yini." Kai tsaye ya ce"Barka da dare ake cewa ina yini ba gaisuwa ba ce kun ji ko? A tare suka aga masa kai, yan biyu ne masu tsananin kama da juna. Inna Meri ya kallah kafin ya ce"Daga ina suke Inna? kuma wa ya kawo su? Inna Meri ta mikar da Hassan ta na ce musu su shiga ciki wajen uwarsu Walida, sum sum suka wuce suna tafe suna ta a juna ba Halin su yi mugun wasa yanzu kawun su ya za ne musu jiki su
Chapter 3 · 0% Book details