← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 208

Sashe 55

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

har a wannan lokacin Mimi ba ta daina son wannan masifaffan gayen ba, ga bakin fuska ga bakin rai da fa in rai Allah dai ya sauwake. Ko da Mimi ta koma a falo ta tsaya saboda Anty Sadiya babbar iyar yaddiko ta ja ta da hira daga ita har Hajiya ba su samu kansu ba sai da bakin Kumo suka tafi sannan su ma su Anty Sadiya suka tafi. Sannan Hajiya ta koma wajen Inna Meri Baaba Uwani ta sako abinci sai Hajiya ta saka a kai ma Inna Meri na ta a akin Hajiyar daman tana so su yi mgana, Hajiya dai ta saka a gidan su ka yi sallar azahar kuma ta matsa ma Inna Meri sai da ta ci abincin da aka kawo mata. Lokacin da ta ce a oshe take sai da Hajiya ta ce mata" Nan fa gida ne Meri, kar ki manta har abincin nakan saka ki aukan ma yara kada rayuwa ta sa ki sauyamin don Allah." Jin haka ya sa ta saki jiki ta ci doya da miyar wai in da Baaba Uwani ta yi bayan ta gama ta sha ruwa. Hajiya ta zaunar da ita su ka fara labarin bayan rabuwa da rayuwa. Hajiya ta kalli Inna Meri tana fa in "Meri ina an Inna? Ina shi Baban Inna? Ina fatan duk suna nan lafiya" Inna Meri tace"Suna nan lafiya, an inna na kano yana aiki an Sanda ne yanzu. Ya yi aure da matarsa Hibba da ansu mai sunan Mallam, Baban Inna dai bai yi aure ba yana nan yana buga wallon kafa auren dai har yanzu lokaci bai yi ba." Hajiya tace"Allah Sarki haka Binta ta gaya min kila ki kinsan kwanaki sun ha u wajen bikin anwar awarta in nan Rukayya da ta fita ko? Inna Meri tace" an Inna ya gaya min kinsan dai uban gayyar ba zai ta a fa a min ba." Hajiya na dariya ta ce"Ikon Allah Mansoor manya hali dai na nan an girman ma ba'a daina ba." Inna Meri ta yi wani mirmishi kafin ta ce" Wasu abubuwan sun ragu amman wasu kam kamar an kara ingiza su ne, fatan mu dai Allah ya shirya mana gaba aya." Hajiya ta amsa da Amin Amin, tana so ta dauko mganar amman kuma kunya da nauyi sun hana ta fara maganar sai kame kame take yi. Dakyar ta iya karfin halin cewa" Meri ki yafe ni don girman Allah ni nasan mai laifi ce a gare ki tun akan abin da ya faru a baya" Inna Meri ta yi saurin cewa" Ba komai Hajiya ni ban rike ki a raina ba, ko yanke hul a da na yi dake na yi hakan ne saboda samun mafita ba domin ina jin haushin ki acikin raina ba." Sai kawai Hajiya ta fashe da kuka cikin kukan take fa in "Wlh Allah aya ko Meri tun bayan abib da ya faru yaro nan Mansoor ke raina ina ta so na zo na duba shi amman kunya da nauyi suka hana ni, har ga Allah ban san abunda Kabiru ya shirya ba kenan da ban yarda na tura su wajensa ba, ki yafe min shima Kabirun ku yafe masa Wallahi tallahi kafin rauwarsa ya yi nadaman abin da ya aikata muku." nna Meri ta ri e hannayen Hajiya da sauri tana fa in " Da gaske na ke Hajiya ban ri e ki a raina ba wlh, kuma komai ya wuce tun a wanchan lokaci maganar kuma wanda ya rasu ai ba komai tsakanimu sai fatan Allah ya sa ya huta." Hajiya na jan majina ta ce"Amin Amin Meri na gode. Wlh ina gaya miki ana gobe za su taho nan shi da Murja a daran ya rasu, kuma da niyar yazo ya roke ku gafara tare da neman afuwan Mansoor sai dai Allah bai nufa ba, bai wayi gari da rai ba." Inna Meri ta hi tausayin Hajiya Itama kamar ta yi kuka ta ce"Allah Sarki ai Allah ya ga niyarsa, bakomai wlh Allah ya ji an sa da Rahma daman can Allah ya kaddara sai hakan ya faru." Hajiya ta saki hannun Inna Meri ta na tsane hawayenta da hannu ta ce" Kabiru ya rasu da sunan Binta a bakinsa ya na matukar tausaya mata tun bayan abin da ya faru Binta ba ta kara ba ma wani namiji dama ba, da gaske ya ke yi kafin rasuwarsa Murja ta ce ya ce har azumin kaffara zai yi in har Mimi na son Mansoor har yanzu to shi ya saki ya kuma ba ma Mimi dukkan daman rayuwa da wanda take so." Hajiya ta karishe fa a tana kallon yanayin Inna Meri wacce ta yi jim ka an tana nazari, ita fa ta ga ya ma Hajiya komai ya wuce Baban Bintu ma haka amman babban matsalan shi ne uban tafiyar duk da itama za ta iya rantsuwa ta ba da shaidan har gobe ya na son Binta kuma dalilinta ne yaki ba ma rayuwarsa haske ko ka an sai dai in ina ita ina taran Baban inna da wannan maganar? Ai wannan bakar zuciyar tasa kamar ta kafuran farko ba za ta barshi ya baiwa zuciyarsa abin da take so ba. "Kin yi shuru Meri, ko kina ganin da matsala ne? Hajiya ta fa a ta na kallon Inna Meri, ita kuma sai ta rausayar da kai kafin Ta ce" Hajiya da gaske nake yi da nace komai ya wuce kuma har abada bazan i Binta a matsayin Surukata ba, sai dai abu aya ne matsalan Baban Inna a gaban ku ya yi rantsuwan ko zai mutu bai yi aure ba ba zai iya auranta ba, Hajiya kin san wasu daga cikin hallayarsa kafiya da naci ga zuciya da riko har gobe Baban Inna ya kasa manta abunda ya faru tun daga lokacin rayuwarsa ta sauya ya daina shiga mutane ya koma rayuwa shi ka ai, ya daina nuna ya na jin da in duniyar nan ma Hajiya mun yi mun yi akan ya daina tuna baya ya fuskanci gaba amman har gobe ya kasa gina ma kansa wata rayuwar, kina ganin a wannan halin da ya ke ciki zai kar i maganar Binta a karo na biyu.? Inna Meri ta karishe fa a tana kallon Hajiya itama sai ta kalleta cikin tunani da nazari, Inna Meri ta yi ajiyar zuciya kafin ta ce"Shi ne hanzarina Hajiya, da kamar wuya gurguwa da auren nesa wannan zuciyar ta Baban Inna ni kaina ta na bani tsoro bansan adadin sallar daren da na yi a kan sa ba, ina rokon Allah ya ya ye masa wannan bakar zuciyar ko ya samu shima ya yi rayuwa irin ta kowa" Yadda Inna Meri ta karishe a raunane ya sa Hajiya taji itama jikinta ya yi sanyi sai ta kasa mgana. Illah kai da ta ka tana fa in "Kafin rasuwar Kabiru Murja ta jaddaddamin ya ce a yi ma Binta duk abunda ta ke so, ni kuma nan duniya ban ga abunda Binta ta jima ta na so da kauna tare da bege irin Mansoor ba." inna Meri ta ce"Ikon Allah! A cikin ranta kuma sai tace ai shima har gobe bai daina begenta ba, Hajiya duk sai gwiwanta ya yi sanyi sai dai ta cigaba da gaya ma Inna Meri irin wasiyar da Kabiru ya bari kafin ya rasu har acikin ran Inna Meri ta tausaya kuma ita ba ta da matsala mai yin shine matsalan da kansa. Sai ga Inna Meri sai a'asar su ka bar gidan Hajiya shima Baban Inna ke ta faman kiran wayar Inna Walida ta auka cikin muryansa ta koda yaushe ya ce"Ina Innar ? Lokacin tana akin Hajiya sai ta yi masa aryan tana sallah. Cikin yanayin maganarsa Ya ce"Ina kuka je na zo bakwa nan gaba aya.? Sai Walida ta rasa bakin mgana Binta na yi mata ra an ta ce sun je gaisuwa dakyar ta iya ce masa suna cikin gari sun raka Inna gaisuwa amman ga su nan zuwa. Lokacin Mimi na akin amman hankalinta na kan waya ne, Walida na sauke wayar Bintu ta ce"Da kin sake kin gaya masa in da mu ka je da yau sai yayi biji biji dake." Walida tace"Ina sane shi ya sa na rasa abin da zan ce." Allah ya taimaka sai ga Inna Merin ta ce su zo su tafi, Hajiya ta ji da i ita da Mimi har bakin get suka rakasu Hajiya na jadaddama Inna Meri sai ta zo da kanta har gida in sha Allahu. Sai a hanya ne suke fa ama Inna Meri Baban Inna ya kira. Cikin fa uwar gaba ta ce"Allah ya sa dai ba ku ga ya ma sa in da mu ka zo ba ko?. Bintu ta ce"Wa zai je ya yi karo da Kura? Ce ma sa walida ta yi muna cikin gari gaisuwa." Inna Meri ta ce"To gwara hakan, ba na son fitinarsa da yamman nan." Adaidaita suka hau saboda su Hassan s una zuwa Kofar gidan Wanzamai suka ci karo da shi tare da Baba Danjuma sun fito sallah. Suna ko arisowa wajen su su Bintu na rige rigen gaishe da Mansoor ita da Walida sau aya ya amsa, yana sanye da riga da wando baki da fari a jikinsa. Kansa da Pcap kamar ko da yaushe. Shi Baba Danjuma bai san Mansoor bai san inda su Inna suka je ba kawai sai ya kalli Inna yana fa in"Na ga kun jima ne? Ko Hajiyar ce ta tsaida ku? Inna Meri ba ta kawo zai iya cewa wani abu ba kawai sai ta ce"Eh wlh shiyasa mu ka jima." Mansoor ke yi ma Inna barka da zuwa, Sai kawai Baba anjuma ya kallesa yana fa in"Daga gidan Marigayi sulaiman Dabo su ke, da yake Mu'azzamu ya yi waya da ita Innar taku ya ce sun dawo shi ne ta ce za ta je ta yi musu gaisuwa na ce hakan na da kyau an yi zaman amana a baya Allah dai ya jikan sa." Ba su Bintu ka ai suka tsure ba har Inna Meri, shi ko tun kafin Baba anjuma ya gama mgana sauran rahaman dake saman fuskarsa ta gushe bai kara mgana ba. Inna Meri ta tasa
Chapter 55 · 0% Book details