Sashe 121
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
lalle Aji ya fara hankali tunda ya yi tunanin fara turo matarsa sada zumunci. Nan suka yini sai la'asar su ka tafi gidan Bibi itama Makama na gidan sanda suka zo shima sai da yace Aji ya yi abin da ba halinsa ba ne shi sada zumunci bai dame shi ba,da ka yi da shi da kar ka yi duk aya ne a wajensa shi tun yana matashinsa in ma gayya ta watse bai damu ba. Sai gabda mangariba suka dawo gidan suna shigowa Magajiya ta fara yi ma Maeesha fafan ta je ta zauna sai dare za ta dawo, ta in da take shiga ba tanan ta ke fita ba, Mimi da Walida su ka wuce bangarensu suna mamakin abunda Magajiyar ta fa a, wai har tana cewa ba hanyar su aya ba kar ta ara ganin ta ce za ta raka su anguwa. Maeeshan dai ba ta ce komai ba, amman kuma ba ta ba ma Magajiyar hakuri ba sai ma kafarta da ta taka zuwa akin ta ko kallon ta ma ba ta yi ba domin a cikin ranta fa e ta ke yi ita ba ta son takura. Har Saddiqu sai da Magajiya ta kira ta sanar masa, ya kira ta ya na yi mata mganar ba ya so, har ya na cewa ita matar Mansoor in tana shige mata ne da za ta ri a kas astan da kanta tana shiga lamarinta. Sai kawai ta saka masa kuka tana fa in" Ta fi ni komai, har mota gareta sannan akin ta ma yafi nawa girma har tiolet tana da shi a ciki fa." Sai ya fara lallashinta ai yasan halinta da kishin Tsiya amman sai da ta ace itama wallahi in ya dawo sai ya san yadda ya yi da ita, itama sai an yi mata tiolet a cikin akinta kamar Mimi, dakyar ya lallasheta da cewa in ya dawo za a yi mata in sha Allahu. Har gida ta je ta sanar da Umman ta akin Mimi ya fi nata girma sannan ita tana da tiolet a cikin akinta, Uwar kuwa ta harzu a har tana cewa" To agola ma ya samu waje ya zauna ballantana an gida? To wlh kema ya sa yadda zai yi dake, ga sauran kayanki nan a gida suna nan sun zama marasa amfani." Ita ta ara zuga arta ta ji gaskiya itama wallahi sai an zo an san yadda za a yi da ita ba za ta yarda ba. Kuma ta fara jin haushin Mimi saboda in ta ga wani abu a akinta sai ta yi mata iyayin itama ta na so ta siya, Mimi na jin haka sai ta ce ta auka bakomai, wato ta na numa mata ita ma'aikaciya ce sannan yar masu ku i, sai take ganin kamar ta raina ta sannan Zuwaira ma Magajiya ta fa a mata haka ta ke zuwa ta na zuga Maeeshan da cewa in ta na shigema Mimi wata rana sai ta renata ta yi mata goru, to ta fara gani sannan ta yi mata mganar tana son aikin gidan Talabijin in itama ta yi mata hanya mana bu e bakin Mimi sai cewa ta yi" Aikin gidan Tibi kuma? haba dai Maeesha irin karatun ki ai kamata ya yi ki samu yar wata private scholl ki fara Koyarwa." Har ta na yar dariya sai ran Maeesha ya aci, sai take ganin kamar Mimi ta ci mata mutumci ne har kuka sai da ta yi, sannan da Saddiqu ya kira ta sai da ta fa a masa sai ya ce" Daman ba na fa a miki ba, wata rana raina ki za ta yi ta ga kamar maula kike yi mata." Shi kuma ya sanar da Magajiya daman ta samu abun nema har aki ta bi ta ta na ara zugata daman Magajiya ai ba'a son ranta take shigema bangaren Mimi ba. Sai da ta tabbatar da ta gama ma Maeesha famfon da ko kallon dhashen Inna Meri ba za ta ara yi ba. Tun kuma daga lkacin ta auke kafarta daga bangaren Inna Meri ta yi cigiyarta da yasa Mimi ta le akin ta, a tunanin ko ba ta jin da i ne sai ta ga lafiyan ta kalau da ta ce kwana biyu ba ta leko ba sai ta ce ba ta yi Ra'ayi ba ne shi ya sa ba ta leko ba, tana magana tana wani cin mgani da Mimi ta fahimci haka take ta kama kanta da ita, Kowa sai ya zauna a muhallin sa, a cikin tsu in Saddiqu ya diro garin sai firita ya tashi sannan gasa take yi da Mimi ko kayan ne ta ganta da shi sai ta kutata ta siya irin shi, ko abinci ta ga ta yi itama sai ta gwada irin shi. Dawowar Saddiqu kuma sai ta ta da rigiman sai an yi mata tiolet itama acikin aki, ga shi kuma ba wajen da za a yi wannan aikin shi ya sa ma tun farko ba'a yi ba, Magajiya ma ta goya mata baya daman so ta ke a yi rigima Agola ya tashi ya bar ma masu gida gidan su. Magana har sai da ta kai kunnen Baba anjuma domin Maeesha gida ta yi tafiyarta tun da Saddiqu ya nuna mata ta yi hakuri in ya samu ku i sai ya kama mata haya su bar gidan, Baba anjuma kuma da ya ji labari ya ce shi ba ruwan shi a cikin wannan maganar Saddiqu yasan yadda zai yi da matarsa. Magajiya kuma ta ce ba a haka dole yasan yadda zai yi ai ansa ne kuma gidansa ne. Sai ya ce to shi sai ya tashi ya bar masa akinsa sai ya gina ma matarsa makewayi. Magajiya ta ce" Abin duk bai kai haka ba, kawai wanda ba shi da gado a gidan ya tashi ya barma ma su gado, kuma daman ai ha a mace yana da gidansa ya ta shi ya bar ma Saddiqu bangaren shi ya koma gidan shi." Baba anjuma sai ya kasa mgana sai ma a lokacin ya fahimci in da Magajiya da ita kanta matar Saddiqun suka dosa wato su so suke sai Mansoor ya tashi ya bar musu gidan, shi kuma ya ce Kar ma ya ji ta tada mganar nan wallahi in ya ji wata magana mai kama da wannan sai ranta ya aci, kuma yanayin da ya yi mganar ya sa sai ta ji shakkarsa ta san halinsa yana da ha uri in ransa ya aci da gaske zai aikata abin da ya fa a. Shi ya sa sai ta bar mganar, ta ce Saddiqu ya lalla o matarsa ta dawo ta ara hakurii zuwa gaba ka an sai Agolan nan ya tashi ya bar gidan tunda ba gidan uban shi ba ne. Inna Meri ba ta ma san halin da ake ciki ba, ballantana Mimi da ta auki Annual Leave za ta tafi Abuja Mommy ta kira duka anta da Mazajen su har da Mimi da Ajin ta, Saboda Abi ya shekara da rasuwa sannan ta ce tana son ganinsu Saboda mganace kan ku in gadon su dake hannunta ita da Sulaiman lokaci ya yi da za a dam ama kowacce abin da ta samu, Khadi da Mimi ne Ita Madiha ta kar i nata kason ta saka cikin Kasuwancinta. Mimi ta san daman da wuya Aji y je Abuja ta na ko fa a masa kai tsaye ya ce"Ni? Kafata ba za ta ara taka wannan ba in gidan ba." Mimi ta ji ranta ya aci amman ba ta yi magana ba da suka yi waya da Mommy sai take fa a mata ita ka ai za ta zo, Mansoor ba zai samu zuwa ba. Sai Mommy ta ce ta tura mata lambar Ajin za ta kira shi da kanta, kamar ta sani ta ce Mommy ta kyale shi, amman Mommy ta ce ta tura mata dai. Haka nan ta tura mata, ita kuma ta kira shi bai da lambarta sai da ta yi kira kamar sau uku bai auka ba sannan daga baya ya zo ya kirata sai ta masa bayanin ita ce mahaifiyar Mimi, bayan sun gaisa sai ta shigar masa da mganar ita ta neme su kan mganar gadon Mimi ne. Kai tsaye ya ce"Hajiya ni ba ni da hurumi kan gadon ta, ku in ta ne hakkin ta ne. Ba dole sai ina wajen za ta iya kar an abin da ya ke nata ba" Mommy ta yi mirmishi kafin ta ce" Duk da haka dai kai mijinta ne, kana da hurumin da za ka zama shaida." Sai kawai ya ce" Hajiya ki yi hakuri amman ina da abubuwa, kuma ba zan iya sakin su saboda wannan bukatar ta ku ba." Duk yadda Mommy ta yi tunanin taurin kan Mansoor ya wuce haka. Da Mimi ta kira ta domin ta ji yadda suka yi sai ta boye mata kawai ta ce su taho tare da Hajiya. Ta na jin haka tasan abin da ya faru ranta ya aci Aji baya daraja mata Iyaye sam, ina laifin Mommy? Itama ina laifin ta? sannan Shi kanshi Abin ya bar duniya amman sai shi ya kasa cire abun a ran shi. Shi ya sa tun daga lokacin ta yi masa gim da rai bai hana ta zuwa ba ya ce kuma ta je ta yi kwanakin da ta ga zai isheta. A na gobe za ta tafi lokacin tana ha a kayanta jirgin ma Daddy ne ya nema musu ita da Hajiya, maganar ne ba ta yi mata ba ya sa ta ce" A'a ka ba ni dai iya kwanakin da ka yi niyya." Kai tsaye ya ce" Ba ni da ta cewa, kar na ce wani abu Barrister ta kirani ta tuhume ni." Galala Mimi ta yi tana kallonsa cikin mamakinsa shi kuma kawai sai ya arisa da fa in" Babanki soja ne, in na ta a ki na kwana a tsugunne, mamanki lauya ce in na cuceki na shiga tasku lauyoyo su yi min caa a kaina gwara na bi a hankali, ki je ki yi duk kwanakin da ki ka ga za ki iya ki kuma dawo lokacin da kika ga dama ni ba ni da matsala a haka. Tunda daman