← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 208

Sashe 134

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

in aka yi maka sai ranka ya aci, Sannan sai ka ri a gayyato mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ka ri a saka su cikin Fushin ka, mu ina Laifin mu a cikin abin da ya faru? Ko laifin wa anda ka ha a kana Jin haushi? Ita kanta Mimi ba ta da laifi har ga Allah Mahaifinta ne kuma ya rasu Aji me ya sa ba za ka bar zuciyarka ta huta ba? Sai ka ri a fushi da wanda ta shi rayuwar ma ta are tuntuni, Allah ma fa muna yi masa Laifi ya yafe mana duk girmansa. To kai me ya sa ba za ka kasance mai afuwa da yafiya ba? Duk abubuwan nan da suka faru rashin Afuwarka ne da maida komai ba komai ba ne da a ce ka kasance mai barin abin da ya faru a matsayin kaddara da ka kasance mai sanyin zuciya da kyakyawan da ia a cikin mu." Ya karishe fa a yana mai kallon Aji ido a cikin Ido kuma ya ga maganganunsa sun shige sa sosai, domin shuru ya yi na wani lokaci kafin ya fesar da numfashi ya ce" Yanzu kana ganin ni da a ka sa awa in na nuna an atamin sai ya zama Laifi? Nasir ya girgiza kai kafin ya ce"In ka nuna an yi maka ba dai dai ba, ba ka yi laifi ba amman ri on nan ba shi da wani amfani Aji, mutumin nan daga baya ya yi nadama ya aiko har gida a ka zo a ka baka hakuri Saboda su wanke laifin su, suka auki Mimi suka aura ma a bisa tsarin ka shin ko zaman da yarinyar ta yi da kai duk da ka yake mata wasu ha inta ba ta chanchanci saboda ita ka manta abin da ya faru ka Fuskanci gaba ba? Aji ya yi shuru domin ya san gaskiya Nasir yake fa a masa sai ya kasa mgana domin nadaman abin da ya aikane ya zo ya ara lullu e sa. Nasir na ganin haka ya cigaba da fa in" Don Allah ka manta baya mansoor ka bar zuciyarka ta samu salama, ka auka a ranka da duk abin da ya faru Ubangiji ne ya shirya sannan ka rika tuna lokaci, a can baya Allah ya rubuta a wancan lokaci ba za ka auri Mimi ba shi ya sa abin da ya faru ya faru a baya, sannan a lokacin da ka aureta a lokacin ne Ubangiji ya ce Kum fa yakun Mansoor shi ya sa kagl ga alokacin ka aureta, abin da kake nunawa dai dai yake da ka na ja da addaran Ubangiji akan rayuwarka Mansoor." Kansa ya jinjina kafin ya ce" Haka ma Mimi ta ce min jiya, wai ina ja da kaddaran Allah a kan rayuwata." Nasir yace"Yes! Is Truth, duk abin da ta fa a maka gaskiya ne, gwara ka bu e zuciyarka." Aji ya yi shuru kafin ya sauke numfaahi lokaci aya yana fa in" Na ji, to yanzu in ina so na manta abin da ya faru ya zan yi? Ko ina so na manta sai na kasa saboda zuciyata ce ta kasa manta abin da ya faru a baya." "She an ne ke rinjayar ka, amman ka fara Koyon ya i da abin da ke cikin zuciyarka ka yi yakinin cewa na yafe ma duk wanda ya ta a cutata, sannan sai ka fara kokarin manta baya ko da zuciyar taka tana dawo da kai acan baya sai ka yi saurin neman tsarin Ubangiji ina mai tabbatar maka cikin lokaci za ka manta komai sannan zuciyarka za ta samu salama da amincin da ta jima ba ta samu ba." Nasir ya gama fa a hannunsa saman Kafa an Aji, wanda ya runtse ido lokaci aya sannan ya bu e yana fa in" Shike nan zan yi kokarin na gwada haka." Nasir ya gya a kai kafin ya ce"Allah ya sa, sannan don Allah ka rage kafiya da zafin zuciya, kuma ka daina jin cewa a cikin ranka sai abin da ka ga dama za ka yi, ka yi tunani da kanka ka gani ka girma yanzu kana bukatar natauwa waje aya da kyakyawan zamantakewa a wajen matarka." Kansa na asa ya fitar da Iska ta bakinshi kafin ya ce" Na ata komai Nasir, jiya nan na gaggaya Mimi mganganu ni har Babanta ina ji na kira da azzalumi." Nasir ya zaro ido lokaci aya yana fa in" Innalillahi, Aji garin ya ya ka yi wannan anyen aikin?. Mansoor ya saka hannu ya shafo kansa sannan ya fara fa a ma Nasir abin da ya Ffru tun na kan tafiyarta Abuja zuwa jiya daga karshe yac e" Inna ma ta ji komai Nasir kuma kasan halinta, Ni banjin Mimi saboda nasan ta na sona za ta gama fushinta ta hakura, kuma ni tun jiya na yi nadaman maganganun da na fa amata, Inna nake ji za ta auki fushi da ni, ka gani ma Mu'azzam na ta kirana shi da Baba kuma nasan kan mganar ne." Nasir ya kalli Aji cikin matsanancin takaici kafin yac e" To da gaske ashe baka son Mimi? Ka daina sonta ne daga baya ko daman can tun farko ba son ta kake yi ba? Wani sakaran kallo Aji ya yi masa kafin ya ce" Wannan wani irin tambaya ne Nasir? Kasam Mimi ita ce rayuwata." "Ba ita ba ce rayuwarka, domin da ita ce rayuwarka da ba ka ci zarafinta tare da na iyayenta ba sannan da ba ka baro ta tana kuka ka yi tafiyarka ko a jikin ka ba Aji." Nasir ya fa a cikin acin rai, Aji ya dafe kansa kafin ya ce"Oh! Na ce maka na yi nadama, kuma kar ka damu da ita tana sona ba za ta iya dogon Fushi da ni ba? "Haka kake gani ko? yanzu kana da tabbacin ba ta tafin kamar yadda ta bukata ka amsa mata ba? Cikin warin gwiwa ya ce"Yes! Ina za ta je? Na fa a maka ba za ta iya tafiya ba, ni ne rayuwarta kamar yadda nima take matsayin rayuwata" Sai da Nasir ya yi yar dariya a cikin ransa ya na fatan Mimi ta yi tafiyar ta domin har yanzu Aji bai yi laushi ba akwai jin kai a tare da shi. Aji ro ansa ya yi akan ya zo ya raka shi gida ya t ba ma Inna hakuri, karo na farko da Mansoor yake jin tsoron ha uwa da Inna, Sai Nasir ya ce bari ya shiga ya yi wanka wani harara Aji ya sakar masa kafin ya ce"Dilla mallam mu tafi, nima ai ba wanka na tsaya na yi ba." Nasir yace"Shike nan ba zan shiga na sallami Iyalai na ba? Kafin Nasir ya rufe baki sai gani ya yi kawai Aji ya ja mota sun bar ofar gidan sai Nasir kawai ya saki baki yana kallonsa shi kuma sai kawai ya auke kansa har ya na wani aga wuya lokaci aya da tattare naman goshin sa. Lokacin da suka isa gidan a kofar gida su ka ha u da Baba Sani da Baba anlami suna ta kuskus sun ha a kai, suna ganin Mansoor jikinsu na rawa suka tare shi,Irin gaisuwarshi ya yi musu, Nasir ne ya yi musu irin gaisuwar da suke so. Yana okarin ya wuce cikin gidan amman Baba Sani ya tare shi da fa in" A she kuma abin da ya faru kenan, To Allah ya kyauta na gaba kune yaran zamani in an gaya muku gaskiya sai kuka ga kamar ana muku bakin ciki ne, yanzu ina amfanin abin da ya faru? Baba anlami ya kar e da fa in" Ba amfani fa, shi ya sa a kace kowa ya tsaya matsayinsa, ina kai ina auran ar masu ku i? Da cikin yaranmu ka nema ai da ba'a ji kan ku ba, ina riba ace aure ko shekara bai yi ba ya are, abun dai ba da Mansoor ya yi kasa e kawai yana kallonsu Nasir ma su yake kallo sannan ya koma ya na kallon Aji cikin mamaki. Domin shima yana so ya fahinmci mganarsu ne. "Na ce ba, saki nawa ne ka yi mata? In ba uku ba ne sai a shiga a gyara lamarin saboda ko bakomai mu cece darajan wannan gidan kar a fara kirga ma an mu auri saki." Hankalin Aji sai ya fara tashi da sauri ya ce"Saki? wa aka saka kuma? Ya fa a yana kallon fuskokinsu, Baba anlami da Baba Sani suka kalli juna kafin Su ha a baki wajen fa in" Toh ba ka son a sani ne? To ai Meri ce da safenan ta ce ka rabu da matarka tana ma gidansu tun jiya." Aji ya zaro ido lokaci aya yana jin wani abu kamar zafi zafi na ratsa sassan jikinsa cikin mamaki ya ce"Mun rabu? tana gidansu? Sai kawai ya juya ya shiga gidan da sauri kamar zai kifa Nasir ya bi bayan shi. Domin in ya fahimta Mimi dai tun a jiya nan ta koma gidansu. A tsakar gida suka ci karo da Magajiya tana Aikinta tana wake wa enta cikin gara'a, abin da ya ba ta mamaki ganin yadda Mansoor ya wuce kamar zai ta shi sama, Duk da ba kasafai take amsa irin gaisuwar sa ba, ta san bai ta a shigowa gidan nan ya ganta zaune bai mata irin ta shi gaisuwan ba ko da ba za ta amsa ba, amman sai ta ga yau ya wuce fuu kamar Iska sai Nasir ne ya bari da gaisheta ta amsa a ranta tana tunanin me ke faruwa? Wata zuciyar ta ce"Me ko ya faru, abin da ya faru da safe ne uwar ta kira duka anta ta sanar da su, sun zo sun cika gida, yau ko sai dai a yi fito na fito." Tuna haka yasa ta ja tsaki kawai ta cigaba da aikinta. akin Inna cike da ayanta da jikokinta suna ta faman maida yadda aka yi tun bayan zuwan su Yaya Amiman, Inna Meri alwala ta yi ta koma cikin akinta kawai ta zauna ta rasa mafita. Domin ta gama yarda Baban Inna baya son farincikinta sannan Babban Burinsa ya ga ya ata mata rai
Chapter 134 · 0% Book details