← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 188 OF 208

Sashe 188

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta yi ta buge kafarta da gefen gado azaba ya isheta sai da ta yi yar ara. Ta yi kasa tana rike kafarta shi kuma ya nufeta yana fa in" Mu gani me ya same ki? wace kafarta ta yi, ta matsa baya tana kuka. Kofar akin suka ji ana bugawa, da kuma Kiran sunan Mansoor da inna take yi lokaci aya ta na Fa in" Baban inna ka zo ka bu e nin kofar nan ko na sa a maka." Ba shi da mafita illah zuwa ya bu e kofar ya na bu ewa Inna Meri ta shigo da muciya a hannunta daman ta auko ne za ta yi talge ta ji Kukan Binta, ba ta yi wata wata ba ta maka masa muciyan a gadon baya ya duke yana fa in"Inna.." arin ara maka masa take yi sai Mimi ta ri e muciyan lokaci aya tana fa in"Don Allah inna, kada ki yi masa lahani." Sai Jikin Inna ya yi sanyi ta sauke muciyan tana hararan Mansoor da ya sadda kai kamar mutumin kwarai. "Fita ka ba ni waje, kaji kunya ita tana tausayinka amman kai ba ka tausayin ta, Yaron ciki gareta ita da ke bukatar kulawa amman kai kake saka ta a damuwa." Sai ya kalli inna cikin mamaki sannan ya kalli Mimi da kanta ke kasa kunya ya kamata ya a ka yi Inna ta san tana da ciki? "Inna yaron ciki? Wai mimi ke da ciki? Muciyan ta aga za ta kara buga masa ya sa ya fice da gudu da rakashi har falo tana fa in" Zan maka rubiti da abin hannuna In baka fita daga idona ba. Takardanta za ka kawomin ka ji ma na gaya maka." Kawai sai ta ga yana mirmishi kafin ya ce"Inna ba kyau sakin aure da ciki, ki yi hakuri kawai ki ba ni matata mu koma gida mu daidai ta." Sai Inna Meri ta kasa mgana. Wani kallo ta yi masa sannan ta shige kitchen ta barsa nan farinciki ya cika sa, shima zai haihu Allah sarki rayuwa. Wata zuciyar ta ce da sanadinka cikin ya zube fa? A fili ya furta" da ba zan yafe ma kaina ba." Mansoor ya ki tafiya ko'ina Inna kawai ya ke ma magiya har ta gama tuwonta kuma ba ta saka masa ba, ya ce rabon sa da abinci tun jiya Inna Meri ta ce ina ruwanta ai tunda bai san baiwar da Allah ya yi masa yanzu ya fara zama da yunwa kiri kiri Inna Meri tahana shi, ruwa kawai ta bar shi ya sha sai fa a take yi tana fadin ya fita ya bar mata gida in kuma yana takaman gidan shi ne sai su su fita su bar masa gidan. Yana jin haka ya mike ya dau key in motarsa ya fice yana fa in" Inna gidan nan fa naki ne, me ya sa za ki ce haka?. Inna ta ce"To ba zan ce ba, ka zo ka min zaune kamar wani an kaciya" Ai da gudu ya bar gidan kafin Inna ta saka a yi masa a tare, gida ya koma ya yi wanka ya sauya kaya sai ya kira Mu'azzam yana fa a masa yadda suka are da Inna. Mu'azzam ya ce"Ga shawara ka je ka samu Baba na san shi ne ka ai zai sauko da fushin Inna." Sai a lokacin Aji ya tuna da Baba ai nan da nan ya kirasa a waya sai ya ce baya gida zuwa anjuma in ya dawo Mansoor in ya zo ya same shi. Shi ya sa bai sake fita ba. Dakyar ya iya dafa ruwan zafi ya sha tea Rana aya kawai ya fara raina kansa, amman da ya tuna Mimi na da ciki sai ya ji kamar an saka sa a cikin Aljannah. *Janafty* *INZB3017* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke bu ata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. Bai fita ba sai bayan mangariba bayan ya sake kiran Baba ya gaya masa ya dawo gida ya zo ya same shi. Shigar manyan kaya ya yi harda hula sannan ya hau motarsa ya nufi anguwan Arawa, yana hanya ya ji ana ta kiran sallar Isha'i ya iso kofar gidan na su ya iske Baba na alwala shi da amininsa Mallam Hashimu sai shima ya bi a yarin su ya auro alwala suka karisa masallacin suka yi sallah. Bayan sun idar ma sun an dade a waje matasan anguwan nan suna ganin Aji suka dafe masa sai da ya ji da su sannan ya samu ya sulale. Ya samu Bab da su Baba Sani suna mgana. Bayan sun gaisa sai suka yi musu sallama suka shiga gida, tunda yanzu sun gane karatun sun rage ro o sun fahimci ko ba su ro a ba Meri ta riga ta yi tarbiyan an ta da alheri gaba ayan su. Baba anjuma ya so su shiga ciki amman Mansoor ya ce su dai tsaya daga wajen zai fi. "Me ke faruwa ne Baban Inna? Na gan ka kamar a gaggauce ne? Mansoor ya yi shuru kansa a asa. Da kunya ya fadi abin da ya aikata amman kuma ba shi da wata mafita dole ya bu e baki ya warware ma Baba Danjuma duk abin da ke faruwa har zuwan shi gidan Inna da matsayar ta ya arishe fa a cikin bayyana nadamarsa lokaci aya yana fa in" Wlh Baba sharrin she an ne ban san abin da ya shiga kaina ba ne a lokacin, na tuba na kuma gane kuskurena in sha Allahu ba zan kara ba, ka shigemin gaba mu je ka ba ma Inna baki ta taimaka ta ba ni matata Baba." Baba anjuma ya kalli Mansoor cikin wani yanayi kafin ya ce" Innalillahi wa'inna Ilaihirraju'un haba Mansoor haba. Sau nawa na sha fa a maka ka ri a tausasa zuciyarka sannan ka daina yanke hukunci cikin fushi, itama mahaifiyar taka ko da yaushe nasihan ta kenan ka rika ha uri sannan ka san yadda za ka yi ka sarrafa fushinka saboda gudun faruwan abin da ke faruwa yanzu. "Ka yi hakuri Baba, na yi nadama kuma in sha Allahu zan iya bakin arina wajen sarrafa fushina in sha Allahu." Mansoor ya fa a kamar zai yi kuka har ya na marairaicewa. "Amman ka san wannan abin da ka aikata ba mai kyau ba ne Ko? Sannan kana sane da cewa zargi na daga cikin abin da ke ata aure ko? Baba anjuma ya fa a yana kallon Mansoor in wanda ya sadda kai asa kamar bashi ya aikata ba, ya yi nadama shima ba laifin sa ba ne laifin soyayyar Mimi ne da ya yi masa yawa shi ya sa yake kishinta kishi mai zafi amman yanzu ya fahimci komai sai ka bi shi a sannu ya sani zai fara sarrafa fushinsa amman ba zai iya daina kishin matarsa ba har abada. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Na sani Baba, in sha Allahu hakan ba zai ara faruwa ba." Sai Baba ya ka a kai kafin ya ce"To bari na shiga ciki na sanar da Magajiya sai mu je tare na yi mata mgana." Tare suka shiga cikin gida, Mansoor ya ce bari ya gaida magajiya, suna shiga suna ma tsakar gida ne ita da Mariya suka shigo ya rankwafa ya gaida Magajiya da irin salon gaisuwarsa ta amsa cikin sakewa kamar yadda ta saba yanzu ta daina aure musu fuska, ko da ma da sauran wani abu a cikin ranta ta boye ma zuciyarta Mariya na gefe ta gaishe shi ya amsa lokaci aya ya na fa in"Ke kina nan? yaushe rabon da na ganki? Kanta na asa ta ce"Kwanaki mun je gidanka ba ka nan Anty Mimi kawai muka samu a gida." Sai ya jinjina kai Magajiya ta ce" Ranar lahadi tunda tana gida sai ku je ke da Walida ku gaishe su." Sai ta amsa dai dai lokacin da Saddiqu ya shigo gidan fakan fakan kamar mahaukaci, daman ya samu labarin yanzu sai yawon gari can lagos in dama yar buga buga ce kuma jari ya su uce. Har da Auwalu sun yi mganar ya ce ya zo ya fara harkan gini ya ce ba zai iya ba ya koma sai zaman shagon wani abokinsa. Dole Maeeshan ta nemi aikin koyarwa tana zuwa domin ta rufa ma kanta asiri. Ko Magajiya bai gaisar ba. Sai ita ce ta ga zai wuce zuwa bangaren matarsa ya sa ta ce" Kai Saddiqu ba ka ga Yayan ka ba ne? Sai ya juyo ya na kallonta ya na kuma kallon Mansoor tunda akwai wuta haske ya gauraye tsakar gidan. Sai ya kasa mgana Yana mamakin yadda Magajiya ta koma ruwan sanyi shi fa jin su kawai yake yi, ba bu wani abin da mutum zai yi maka wanda Allah bai maka ba. aramin tsaki kawai ya ja ya yi wucewarsa mirmishin gefen baki Mansoor ya yi domin wanda bai daraja uwarsa ba har yaushe kake tunanin kai zai iya daraja ta ka mahaifiyar? Magajiya kunyar duniya ya kamata saboda abin da Saddiqu ya yi mata. Dai dai lokacin da Baba ya fito cikin shirinsa yau kwanan Magajiya ne sai gobe ne yake gidan Inna shi ya sa yana fitowa ya kalli Magajiya lokaci aya yana fa in" Magajiya Mansor zai auke ni zuwa gidan Meri zan dawo zuwa anjuma in sha Allahu.". Sai Magajiya ta kallesa a sanyaye kafin ta ce"Ina fatan dai ba wata matsala? Da Sauri yace"Lafiya lau, wata yar matsala ce amman kada ki damu." Ganin bai fa a mata ba ya sa ta ka a kai kafin tace to Allah ya sa a dawo lafiya. Mansoor ya yi
Chapter 188 · 0% Book details