Sashe 204
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
satin nan zai zo gida zai yi mgana da Mimin shi ya auka Fatima na da tunani ashe dai da sauranta. Mu'azzam suna waya amman bai gaya masa ba. Sannan ko Walida da ke gidan ta kwana ta tashi ba ta san wani abu ya faru, sai ya bari kawai sai ya dawo gidan ya samu lokacin da zai yi ma Mimin fa a sosai ko ta dawo cikin hayyacinta ya je ma ya kara ganin Mommy tana hawaye ta na gaya masa duka yaran sun juya mata baya harda Mimi sannan ta hada shi da Al ali har ga Allah bai ga illan shi ba, kamili mai mutumci sun samu uba amman suna haukan banza. Ranar jumma'a ya dira gombe, ko a fuska bai nuna ma Mimi wani abu sai da ta gama bikin tarbansa bayan ya yi wanka ya ci abinci ya so ya yi mata mgana amman sai kewarta ta hana shi a ka kwana ba ma juna Soyayya da asuba ya tafi masallaci bayan ya dawo ya koma barci asabar ne ba ta fita aiki bai tashi ba sai goma na safe yana fita falo ya iske ta, tana goge goge ga Ummi saman kujera an jinginar da ita alamun an fara Koya mata zama. Ita kuma matar gidan tana ta gogen tibi wayarta na saman kujera ta saka speaker suna mgana da Madiha abun da kunnuwansa suka jiye masa shi ne Madihan na cewa" Ni fa na gayama Khadi in har Mommy na son mu sai dai ta za a ko auran ta ko mu." Mimi ta ce",Wlh nima fa ko kiranta ban sake yi ba, in har tana son mu sai ta za a ko wannan mijin ko mu ayanta." Yana tsaye ya ji Madiha na zuga Mimi da kada ta ara kiranta ta bar ta in suna da amfani za ta neme su. Saboda haushi ko Mimi ba ta san ya shigo falon sai da ta ji muryansa yana fa in" Ko shekara ari ta yi ba ta neme ku ba, ba abin da zai sameta amman ku sami ko wata uku kuka yi ba ku neme ba ta tsinuwan Allah da ta mala'iku sai ta tabbata a kan ku, sannan ku sani ita ce ta haifeku ba ku ne kuka haifeta ba, aure ta yi ba zaman zina take yi ba, ko da saka albarkan ku ko babu za ta zauna lafiya.Ku ne in ba ta yafe muku ba ku ke cikin bala'i da masifa, sannan zan miki garga i na karshe in har ba alheri za ki kira matata ki gaya mata ba, to don Allah kada ki sake kiranta ina son ta samu rabauta a duniya sennan ta samu lahira ke da kika juya ma Albarka baya je ki ki yi ta fushin ki ki jira ranar da mahaifiyarki za ta zabi sunnar ma'aiki a kan ki, ga ki kamar mai hankali maimakon ki zama jagoran annen ki wajen fa a musu gaskiya sai ke ce ke ara zugasu kuna kauce hanya, girman banza gareki sannan takmar ilimin ki bai yi miki wani amfani ba, ki je can ki yi ta sakarcin ki amman na gaya miki wlh tallahi ka da ki kara kiran matata kina zugata." Yana gama fa in haka ya kashe wayar, Mimi ta dankare a tsaye tana kallon Aji cikin mamakin manya manyan kalaman da mijinta ya sauke ma yayarta, ta bu e baki za ta yi mgana itama ya aga mata hannu ya fara zazaga mata nata fa an tas ya yi mata sai ta fara kuka tana fa in" To koma menene sai ka gaya ma yayata mganganu haka? Kai tsaye yavce" An gaya mata in kuma za ki rama mata ne, bismillah ina ruwana da girmanta tunda girmanta bai mata amfani ba,.Mahaifiyarku ce fa amman saboda rashin tunani kuna neman sa a mata saboda haukan banza in ba'a aure za'a haifeta? Ita ba tana gidan Mijinta ba ne? Sai ta hana ta auren ita? Ba ku da adalci ba ku ba yara anana ba amman kuma kuna yin abin da ko yara suka yi sai an yi mamaki, har saboda haka Hibba ta yi miki murna ki ka bi ta da zagi saboda ke kin isa ina laifin wanda abun alheri ya same ka yace maka Allah ya sanya alheri? Sai ki zage ta? Mimi na kuka wiwi ta ce" Ni fa ban zageta ba, ita ce ta min dariya to abun dariya ne? Shima ya taso mata da cewa to abin kuka ne, ko so take yi ta ta ya ta haukan da take yi na fa a da mahaifiyanta saboda ta yi aure. Mimi duk yadda ta so kare kanta Aji bai ba ta dama ba, ya yi mata fa a sosai ya kuma bar ta, tana kuka ya auki Ummi suka shige aki ranar gidan yini ya yi ba da i ko abun kari ba ta yi ba ta shige aki tana kuka shi kuma ya auki arsa suka fita zuwa gidan Inna ya karya ita kuma Inna ta yi ma Ummi wanka tunda Aji cewa ya yi Mimin ba ta jin da Saboda nono ne ya sa ya maida Ummi gidan a mamakinsa sai ya ga Mimin ta tashi har ta yi abinci ta gyara gidan,ganin haka ya sa bai sake fita ba ya zauna ya na ara mata da nasiha, ita kuma ta baahi hakuri ta ce za ta,kira Mommy ta ba ta hakuri ita da Hibba. A gabansa ta kira Mommy ta ba ta hakuri, Mommy kamar ta yi kuka farinciki ya cika ta, ta yi ta sakama Mimin albarka tana fa in" Wlh Allah saboda ku na yi wanman auran saboda na kare muku mutumcin ku da na ayan ku." Mimi na hawaye tace"Hakane mommy ki yi hakuri, In sha Allahu ba zan kara ba suma su khadi duk za su daina." Mommy tace bakomai ita ba ta rike su ba ta yafe musu tun kafin ma su roke ta Haka ta kira wayar Hibba bayan ta cire ta a blaklist ta ba ta hakuri itama ta ba ta hakuri shike nan sai mgana ta wuce. Amman fa Madiha sako ta turama Mimin da cewa ta gode tunda ta ba da damar da Mijinta ya zage ta har Dr ta kira ta gaya mawa shi kuma ya ce abunda Mansoor in ya yi daidai nw in ita ba ta da hankali sai ta yi ta yi,Khadi ma ta kira Mimin ta mata surutun ta za i namiji a kan su an'uwanta tunda a gabanta ya zagi Madiha ta kasa mgana ita dai sai hakuri ta ba su, tunda ko ita ba ta tsira da fa an ba kuma suna nan a kan bakansu na ba su som auren. Sai ga shi wata aya da wani abu da auran mommy Khadi ta samu matsala da dangin mijinta sai ga ta gaban Mommy tana kuka, Mommy ita ta kira mijin khadi ya zo har gida suka yi mgan matsalace ta gida yayyensa ne suke son ya kara aure, karshen dai Alkalin da suka raina suke jin haushi ya tsaya mata tare da Mommy dashi suka maida ta kaduna suka kuma nuna ma mijinta ba ruwan Khadi da auransa amman ya kare mutumcin matarsa tunda yayyen nasa har gida suke zuwa su ci zarafinta, tun daga nan Khadi ta saduda itama Madihan ganin ba ta da abokin adawa yavsa ta fara saki amman ba duka ba. To ta na da wacce tafi Mommyn ne? itama Madihan ku i ya hado su da Mijinta tunda Ku in na su a waje aya ne suna kasuwanci ti shekara ta yi kuma an zauna ana ta lissafi an gano dai shima yana karkatar da wasu ku i rigima har Abuja wajen Mommy. Sai ga shi Alkali Mustapha shi ya warware matsalan a ka samu sulhu, itama daga nan ta fahimci aure ga mace sutura ne komai tsufanta kuwa, ta saki suka rumgume al ali a matsayin uba sannan akwai yarsa Batula dake aure a lagos Lakcara ce a Legal ya ha a su suna zumumci itama Khadi akwai namiji a kaduna yana aiki da NNPC Shima tare da iyalansa sun zama an'uwa tare da Khadija akwai wacce ke kano, sunanta Badiyya likitan yara ce ashe ma asibiti aya suke aiki da Sulaiman ya san ta ta san shi sai wannan dalilin ne zumuncin su ya ara zama na sosai Iyalanta na zuwa gidansa shima iyalansa na zuwa, ayan namijin Soja ne yana Abiya tare da iyalansa amman suna mgana a waya dukkansu. Bayan wannan ya wuce an samu daidaito zukata kuma sun samu natsuwa sai Mimi ta kara bijiro da mganar ta na son siya wata sabuwar Motar, Aji dai da ta nemi shawaransa cewa ya yi" Ni tun a baya na baki shawara,sannan na yi miki al warin in na samu ku i da gumina zan siya miki mota amman na ga kamar kina sauri ne bazan hana ki siya ba tunda ku in ki ne amman da kin hakura da siyan wata motan ki cigaba da lallaba taki, ga tawa ma duk ki ha a ki ri a amfani da ita, in har Allah ya hore mana ko Jirgi ki ke so zan iya siya miki Mimi ba ma mota, gwara ki fara ko wani kasuwanci ne da kudin kamar zai fi,amman in ba ki ji shawarata ba shike nan ba zan hanaki yin yadda kike so da ku in ki ba." Da ta yi mgana da Mommy da Hajiya suma dai shawaran da suka bata kenan sai ta amince da shawaran ta fara kasuwanci amman ta rasa ina zata fara tunda ba ta da Ra'ayi ko ido a kan kasuwanci da ta yi mgana da Aji sai ya ba ta shawaran ta yi mgana da Yayarta Madiha ai yar kasuwa ce za ta ba ta shawarwari amman shi da ita sun tsaida shawaran ta fara kasuwancin saida Abayoyo da jaka da takalmi in ta kar u har shago za ta iya bu ewa. Ta yi mgana da Madiha kuma ta yi na'am da shawaran Mimi ta ce za'a ri a mata Oder jakunkuna wasu daga Lagos wasu kuma daga China ko India ko Italia,dogayen rigunan kuma daga daga Dubai,