← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 208

Sashe 33

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ka yi kanin nashi ne? Ai agola ne zuwa da shi gidan wanzamai Innar sa ta yi." Shamsu yaji zafin naushi ganin har jini ya fito shima ya dunkule hannu ya rama ko kafin su Nasir su shiga tsakani sun kaure da dambe dole mutanen dake cikin masallaci da waje suka zo rabon fa a ciki har da su Baba anjuma da su Baba anlami har kuma da mahaifan su Nasir. Shi kan shi Shamsun har da uban sa. Sai da aka samu aka raba fadan amman fa Shamsu ya ci naushi duk bakinsa ya haye ga shi yana fitar da jini. Mansoor fitinanne ne yana da ba ar zuciya in dai iya fara fa a ba ya iya bari ana raba su fa domin aji ba'a si yana ara kaima Shamsu naushi. Baba sani ya yarfa ma Mansoor mari a gefen fuska yana fa in"Kai kaci gidanku kai ka ai ne mai zuciya anan wajen? Ana mgana ka bari kana kara wani hakilo to sai ka daki wanda za ka daka kaji ko? Ya fa a Saboda ganin yadda Mansoor in ya ke wani huci ya na kallonsa kirjinsa na sama da kasa zufa na keto masa gashi ya dumkule hannayensa guda biyu ya na jiran ya kai naushi. Baba Danjuma ya ce"Sani a bi a sannu don Allah." Baba anlami ya ce"Yaya anjuma ka daina saka baki in yaron nan na iskanci, ji abin da yake yi kamar shi ka ai ne mai zuciya anan wajen" Shi dai Baban Danjuma okarinsa a samu sasanci. Shamsu aka fara tambaya abinda ya faru ya maimaita karya da gaskiya. Baba anlami ya yi aramin tsaki kafin ya ce"To mi ye abun fa a anan ai ba karya ya yi ba me kuka ha a da Mu'azzam in? Kowa fa yasan zuwa da kai uwarka ta yi garin nan" Baba sani ya ce"Kuma ban da rashin tarbiya har da ce masa wai uwarsa ce ta auri Yaya anjuma ta haifi Mu'azzam kaji wani rashin yanzu ya dace aji wannan mganar a bakin yaro kamar Mansoor? Nasir ya yi karaf ya ce"To amman shi ina ruwansa da cewa Mu'azzam ba kaninsa ba ne, kuma ai yanzu shi ya fara ganinsa ya zage shi." Su Ahmad ma suka ba da shaidar haka har da Mu'azzam. Shi ko Mansoor an an yi ya yi mgana bakar zuciya ta hana shi, mahaifin Shamsu Mallam bala ya ba da hakuri ga Baba Danjuma shima ya bashi hakuri suna gayama juna a kowa fa ya haifa sai hakuri. Su Baba Sani ke ta manganganu suna fa in"Yaya anjuma duk kai kake sangarta yaron nan, yana iskancin da ya'yan mu ba sa yin irin shi." Da an yi mgana sai ka ce maraya ne ai kowa ma marayan ne muma ai marayun ne." Haka suke cewa sanda suke hanyar komawa gida, su Nasir kowa ya wuce gidan Mansoor kuma Baba Danjuma na rike da shi suna tafiya daga baya fa i yake yi"Ka rika saka ma zuciyarka salama kaji ko Baban Inna rayuwar nan duka duka nawa take? Cikin jin haushin ya ce"Me ya sa ya ce Mu'azzam ba anina ba ne? Ai ka auri Innata kuma ita ta rike Mu'azzam saboda haka kanina ne" Baba anjuma ya ce"Kwarai ma da gaske ba wanda ya isa ya ce kai ba Yayan Mu'azzamu ba ne, suna tafe ya na ta bashi hakuri shi kuma ya na faman saukar da zuciyarsa Mu'azzam shi ya yi saurin yin gaba ya je ya gayama Inna abin da ke faruwa ko kafin su Mansoor su shigo labari ya kawo cikin gida tunda su Baba Sani tun a tsakar gida suka fara mangaganun Yaya Danjuma na aure ma Mansoor kugu yana ma mutane rashin mutumci a gari da ko su ya'yansu ba sa aikata irin shi. Gaje ta ta e baki kafin ta ce"Da an yi mgana sai ace ya na da bakar zuciya ga shi ba ka isa ya ganka ya gaisheka ba a wulakance sai dai yace wai barka." Suna cikin mganan Baba anjuma ya shigo rike da Mansoor su Gaje suka gaishe shi ya amsa kai tsaye akin Inna Meri ya wuce da shi ya na kiran ta kamar yadda ya saba. "Meri meri, ina Merin take ne? Su Baba Sani da matansu suka bi shi da kallo Baba anlami ya nuna Yayan nashi lokaci aya yana fadin "Ji be shi, yadda ya ke rawan jiki da yaron nan na tabbata ko Auwalu baya yi ma haka' Magajiya daman na cikin akinta tana sallah tana sallamewa ta fito tana fa in" ko Auwalu da ya haifa baya masa son da yake ma agolan nan da Meri ta zo da shi gidan nan anlami, yanzu haka su yana nan nan da su amman Auwalu bai san ma in da yake ba sai can in ya ga bai ganshi ba ya fara ma mutane fa an wai Auwalu ya koyi yawon dare, to ai gwara ya koya tunda bai iya jan sa a jiki ba sai Agolan da ba jininsa ba." Baba Danlami ya ce"Magajiya lamarin Yaya Danjuma fa akan agolan nan na Meri sai Allah kawai, in muka yi mgana sai ya ga kamar muna nuna ma yaron bambamci ne, kuma mu tsakani ga Allah gaskiya muke gaya masa sai ya rika nuna mu ba mu san girman Amana ba, kuma sai ya rika nuna wai yaron maraya ne." Magajiya ta ta e baki kafin ta ce"Ai ga shi nan ya za me ma Agola uba ya kuma maida ayan sa marayu" Duk kuma manganganun da suke yi a kunnen Inna Meri da Baba anjuma, dake kofar akinta saman tabarma. Hatta Mansoor in da Mu'azzam suna zaune, Bintu da walida dai suna cikin aki tare da su Amina da ba su jima da dawowa daga gidan ba. Kan Mansoor na kasa ya na huci Inna Meri ta cire tagumin da ta yi kafin ta ce"Ni na rasa yadda zan yi da yaro nan mallam, nasihan nan ko azu muna tafe a hanya sai da na yi masa, kai dai Baban inna kana son kowa ya rika kama sunanka, to ka sani ba ka san bakin wani ba in wani ya yi maka baki ka lalace ba ruwana." Baba anjuma ya sausaauta murya yana fa in" ki daina fa in haka Meri yarinya ta ne in ya ara girma zai daina in sha Allahu, ki zuba musu abinci su ci ko sai mun dawo salla ne?. Ya fa a ya na kallon samarin nasa guda biyu, Mu'azzam ya gya a kai shi ko Mansoor bai yi mgana ba. Inna Meri tace"Sai kun dawo domin ban jima da yin talge ba." Tunda daman tana da sauran miyan kukan jiya sai ta ce bari ta tuka tuwo. Su Amina sai bayan mangriba suka dawo gidan daga can bolara gidan kakaninsu Mu'azzam bai je ba sai su ka ai suka je su ka kwana biyu suka dawo. Da suna nan Amina ce babba ita za ta yi mata komai kafin ta dawo, tunda daman ita take bari a gidan in ba ta nan saboda ita Amina ta gama sakandiri ba kudin da za ta cigaba da makarantar. Duk fa an da aka yi ma Mansoor bai amsa ko aya ba kansa na kasa yana sakin huci har aka kira sallar isha'i baba anjuma ya kara saka su suka yi alwala suka koma masallaci. A na idarwa ya taso zuwa gida suna zuwa kofar akin Magajiya suka ga Auwalu na zaune na cin tuwo ya yi butu butu da kayan jikinsa tunda akwai hasken aci bal bal din da Magajiya ta kunna. Baba anjuma ya kalle sa kafin ya ce"kai Auwalu yau ina ka je ban gan ka ba.? Auwalu na sosa kai ya ce"Mun je aiki ne Baba." Kafin Baba anjuma ya yi mgana Magajiya ta tare shi da cewa"Ina ruwan ka da in da ya je tunda baka damu da shi ba, ai kana da makwafinsa Meri ta kawo maka Agola sannan Habiba ta mutu ta bar maka an so duk duniya ba ka ganin kowa a gabanka sai yara nan guda biyu, ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta." Mansoor na ganin haka shi baya juran ganin magajiya ma yi ma Baba tijara ya sa ya tasa Mu'azzam gaba suka shige bangarensu. Suka bar Baba anjuma na fa in "Ki ji tsoron Allah magajiya kin aure ma yaron nan kugu ya ki karatu na bokon tun tuni ya daina zuwa haka na arabin ma, shi zai yi takaici nan gaba ni dai Allah na gani na fita hakkinsa kuma maganar Baban Inna da kike yi ni fa na kar o shi amana wajen danginsa ba wai domin sun gaza wajen rike shi ba, sai domin ina so na samu ladan rikon maraya. Kuma ni ba na tuna bambamci tsakanin ya'yana duka aya suke a wajena ruwan ki ne, ki saka tunanin haka a ranki ko ki saka ina nuna bambamci Ubangiji na sama na kallon komai." Da haka ya juya ya wuce ya barta tana fa in"In da ka biya mishi ku in makarantar me zai hana shi zuwa? Ai an so dai su je su yi karatun mu ga sun zama shuwagabannin asar nan.' Inna Meri na kofar akinta tana kwashe tuwo sai da ta yi dariya. Duka an ta makarantar Gwammati suke yi. Su Amina kuma dangin mahaifiyarsu su ke tallafe sda manyan bukatunsu, ita dai ta na auke mu su kananun da ba'a rasa ba da aikin da take yi a gidan Hajiya Fatima Dabo da shi take taimakon kanta da mijinta da ya'yanta amman sai Magajiya da sauran matan gidan su ke ganin kamar a kan ta da an ta Mallan anjuma ya tare ita da anta Mansoor da mutuwa ta yi sanadiyar auranta da Danjuma da ko a mafarki ba ta taba tunanin haka ba. Babu amfanin zama ka yi ma wanda ba zai Fahimce ka bayani ba, tunda aka auro ta tazo garin nan tasan magajiya fitinanniya ce, kuma ba ta da kirki in da tana da kirki ai ba sai an aurota ba za ta iya ri an mijinta gam a hannunta ba tare da sai ita an aurota saboda ta zo ta ri an matarsa
Chapter 33 · 0% Book details