Sashe 68
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mallam." Shi kuma kai tsaye ya ce" bakomai ki bari in ya zo sai mu yi mgana." Inna Meri tace" Don Alah kada ka biye masa" ya na yar dariya ya ce" Ba ruwanki tsakanin uba da a ne." Ba ta ce komai ba amman ita kam ba ta san abun rigima. Ya gama cin abincin kenan sai ga Walida sun dawo makaranta, sai ya mike yace an fara kiran salla zai je masallaci kokacin Inna Meri har ta gama kwashe tuwo sai walida ta kwashe tabarma da kwanukan da Baba Danjuma ya yi amfani da su. Kamar yadda ya saba a masallacin anguwan yake sallah in dai zai zo gida, yau ma a nan ya yi anan ne ma ya ga Saddiqu domin shi bai san ya dawo ba ya yi mamakin girmansa domin ya da e bai gansa ba gaskiya sun gaisa tunda ya bashi hannu sun yi musabaha askin da ke kansa ya ke kallo wani irin aski daga gani ba na mutanen kirki ba ne, kamar zai yi mgana sai kuma ya fasa. Baba sani da Baba Danlami ma ya ba su hannu sun yi musabaha suka amsa a cune saboda suna ganin ya rena su ba ya iya gaishe su, sai suka ga har Baba anjuma ma musabaha ya yi da shi, ballatana su yan karan ka a miya. Ya jima bai zo anguwan ba ya yi azumi bakwai uku na kaffara hudu kuma tsakaninsa da ubangijinsa. Sun buga wasaani biyu a kwanaki nan shi ya sa ba ya samun zama sai a hankali. Baba anjuma ya tsaya wajen abokinsa mallam Hashimu shi kuma sai ya riga sa shiga gidan a tsakar gida ya ga magajiya na girki mamaki take ba shi ko da yaushe ba ta tashi girki sai dare ya yi, barka da dare ya yi mata sai ta yi kamar ba ta ji ba Mariya ce da ta ji muryansa ta fito tana gaishe shi ya amsa bai ko kalleta ba, Yau a maahin in haya yazo motarsa ba mai, mashin in kuma ta yi kura yaji yamar hawanta a haka tunda ya jima bai yi amfani da mashin in ba. Suna cin tuwo ya same su a tsakar lungun Inna Meri har kasa ya duka ya gaishe da Inna ya na sanye da mayan kaya har da hula ya rufa sumar kansa duk da anan wai ya rageta. Inna meri ta amsa masa a dakile tunda ya ga haka ya san akwai mgana Walida ta gaishe shi ya amsa ya na kallonta ta gefen ido. Nan Inna Meri ta yi banza da shi a durkushe ba ta ce akawo masa ruwa ba, kuma ga shi ta a son yana son tuwo shi kuma ganin haka yasa ya cigaba da tsugunno har Baba anjuma ya shigo ya gansa a haka shi ya ce ya tashi ya zauna saman babbar tabarman dake wajen, shine fa ya cire takalmi ya zauna Baba Danjuma ya ce a zuba musu tuwo dole Inna ta ba su amman da ba ta yi niyyar Baban Inna ya ci tuwon da ta yi yau ba. Suna cin Tuwon suna yar hiran su ita kuma Inna na gefe, Kiran wayarta ma ya ta da ita Mu'azzam ne sun jima suna mgana ya ce cikin sati nan a ranakun karshem mako suna nan zuwa Mansoor na jin murnan Inna Mu'azzam zai zo amman shi ba ta masa wannan Murnan in ta gan shi. Sai da su ka koshi su ka wanko hannu sai kuma aka kira sallar Isha'i dole suka mike suka tafi masallaci bayan sun idar ne su ka sake dawowa. Walida ta shige ciki ta bar su tun da tasan mgana za su yi. Inna Meri ta tsare Mansoor da ido kafin ta ce"To Sarki tunda sarautarka ba ta barka ka yi mana bayani ba, to su wa anda ka yi ma bayanin sun kiramu sun fa a mana." Kai tsaye ya ago yana kallon Inna Meri kafin ya ce"Na me fa Inna? Inna Meri haushi ya hana ta mgana Baba anjuma ne ya famsheta ya warware masa abunda ke faruwa sai a lokacin ya tuna ma, shi bai auka ma sun ji mgamar ba. Kai tsayen kuma ya kara cewa"E, da gaske ne, ni nace anan za ta zauna tare da Inna" "A wani akin za ta zauna kenan? Inna ta jeho masa tambayar shuru ya yi na wani lokaci kafin ya ce"Nan na kusa dake Inna." Inna ta juya ta na kallon akin cikin jin haushi ta ce"Gidan ka fa?, Ado ne a wajen ka, ba wajen saka mata ba ne.? Kansa na kasa ya ce" ko za ta zauna a gidana ba yanzu ba Inna." Inna ta tare shi da fa in"To sai yaushe? nan in ma ai ba gidan ka ba ne tunda baka da gado acikin sa ka ga ko baka da wannan hurumin." Kai tsaye ya kalli Baba kafin ya ce"Wajen Baba zan kama haya. za ka bani Haya ko Baba? Inna Meri bakinta ya kasa rufuwa Saboda mamaki. Baba Danjuma ya buga kafa ar Mansoor kafin ya ce"ba Haya tsakanina da kai, ka zo ka gyara ka yi duk abin da ka ga dama da shi." Kansa na kasa ya ce"Na gode Baba Allah ya kara girma" Inna Meri ta na numfasa kafin ta ce"Mallam kasan ba zai yuyu ba ko? Miye ya shirya ne? Me ya sa ba zai kai ta gidansa ba? Tsakani ga Allah a wannan akin ai ya yi ma ka an a ce mace ta zauna ko ni uwarsa babban aki ka gina min, in har ba ka son yar mutane ka bar musu a barsu ba na son fitina ba na son fitina na fa a maka Mansoor." Kansa na kasa bai yi mgana ba Baba anjuma ne ya ce" Ba ruwan ki sun rokesa kuma yaji rokonsu kuma ya ce yana da shara i suka kuma amince sannan bayan na ya fa i shara insa sub kuma amince to miye naki aciki? fatan alheri ne namu yanzu da saka albarka, mganar aki kuma da bangaren nan da na Magajiya kinsan duka mallakina ne ina da ikon na yi kyauta da shi a yadda naga dama." Sai Inna Meri ta kasa mgana kai kawai ta jinjina kai kafin ta ce"to sai ka gaya masa shi a ke jira" Baba anjuma ya ce"Wannan ba matsala ba ne sai mu je a yi mgana ko ba haka ba? Ya fa a yana kallon Mansoor da ya jinjina kai kafin ya ce" Duk yadda ku ka tsara ba matsala Baba." Shi kuma sai ya ce"Ka ga ya musu za mu zo sai mu yi mgana a gudanar da neman auren" Sai Mansoor ya jinjina masa kai Inna Meri haushi ma hana ta mgana ya yi daga karshe ta yi shigewarta aki ba ta ma san tafiyarshi ba. Washegari da kanta ta kira Mu'azzam tana fa aa masa abunda ke faruwa Mu'azzam na wajen aiki fa i ya ke yi "Finally Inna Yaya Mansoor zai yi aure Alhamdulillah" shi duk abunda ta ke kokarin ganar da shi ya kasa ganewa ya ce in ya koma gida zai kirata. A lokacin ya aga waya ya kira matarsa Hibba ya fa a mata itama cikin mamaki ta ce"Wa zai aura? Kai tsaye ya ce"Mimin sa mana." Baki ta rike kafin ta ce"Lalle matar mutum kabarinsa." Mansoor ya doka ma kira bayan ya katse na Hibba ya na aga kiran kawai sai ya ce"Angon Mimi an gaishe ka." Daga can bangaran Aji sai ya yi tsaki ya kashe wayarsa ya bar Mu'azzam na dariyan farinciki da sai ranar Jumma'a za su taho amman ya fasa yanzu ranar Alhamis za su isa Gombe In sha Allahu. ***** Mimi na wajen aiki sakon Aji ya same ta ba ta yii tsammani ba kalamansa ba su da yawa. _Ki sanar da magabatan ki, waliyina zai zo ya kawo sadakin auran ki._ Iya abunda ya ce mata kenan mamaki ya kamata shi kuma na shi salon kenan? Sai da ta koma gida ta sanar da Hajiya kai tsaye Hajiya ta ce" Yaushe ya ce miki? Kai tsaye Mimi ta ce"Bai ce ga rana ba Hajiya" Hajiya ba ta damu da ita ke bi sai ta kara kiran Inna Meri ta na tambayanta rana tace ba ta sani za ta yi ma mallam mgana. Da Baba Danjuma ya dawo ta yi masa mganar kai tsaye ya ce"To ban sani ba amman bari na kira Mansoor din naji tsarinsa." Nan ta ke ya kirasa sai bai aga ba sai da ta katse ya bi biyo bayan kiran suka tattauna Inna Meri na zaune kuma wayar Baba Danjuma irin Tecno ne masu kara duk ta ji abunda yace a ranta ta na tunanin ta haifi Mamsoor amman ko ita ba za ta iya tantance hallayarsa ba ka rasa ina ya dosa, yanzu ma cewa ya yi duk ranar da Baba yace sai aje, zai ba da ku da za a je da shi su fa i sadaki a biya kuma baya son ya au lokaci in an jima wata biyu. Inna Meri ta kira Hajiya da safe ta fa a mata tunda Baba anjuma ya ce zai fa a ma su Sani da abokinsa Hashimu ranar asabar Inna Meri ta ce ya yi lokacin Mu'azzam na gari shima. Hajiya da ta ji haka sai ta ce ta kwana gidan sauki itama a nan t ke ta kira Daddy ta ce ya zo gida tana son ganinsa sannan ta kira Yaddiko ma tunda itama kamar uba take Ta kuma kira Mommy ta sanar da ita, domin itama ta sanar da sauran an'uwan Mimi. Sai abun ya yi ma Mimi wani iri? Wai za'a kawo sadakinta Aji za ta aura ashe dai da gaske wata rana buri zai iya zama gaskiya. *Janafty* *19Aug/2024* *INZB2002* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK, 09069067488* *FARA MAI DA I MAI INGANCI, PECK 800 NE, 08169937644 RIJIYAR ZA I KANO STATE.* Ina kuke mata yan kwalisa.. *KHADYS EMPIRE* Ta Kawo muku kayan mata masu kyau da saukin kudi kamar haka. *Zumar Matsi Guarantee 3500* *Maganin sanyi komai nacinsa 4k* *Zumar kacha kacha 2500*