Sashe 8
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
amma ya maida mata martanin mirmishinta. Wanda in za ta iya tunawa daga wannan mirmishin Allah ya ha a zukatansu waje aya zata iya rantsewa da Allah ta fara son shi ne daga wannan ganin farko da ta yi masa tana yar shekara goma sha shidda a duniya wacce ta yi jarabawar JSCE. Tana wannan tunanin ta na tuna shi a can baya acikin idanuwanta, tana wannan kukan ta tashi ta yi sallar la'asar ta yi sujjuda mai tsawo tana rokon Allah ya cire mata soyayyar MANSOOR acikin zuciyarta da tunaninta gaba aya, haka da ta yi sallar mangariba tana addu'a tana kuka domin ta gaji ta sare ta na bukatar ta yi rayuwa cikin zuciyarta ba wannan nauyin da wannan ciwon. Me ya sa ya kasa fita daga cikin zuciyarta? Me ya sa take ganin duka maza a matsayin mata in har bashi ba? A wajenta shi ka ai ne namiji kwara aya da ta yi tunanin zata iya zaman aure da shi, shi kuma rayuwarsa ta yi ma rayuwarta nisa.Babu abin da ke kara sakata kuka in ta tuna RANAR! ranar da ta sanya mata suna bakar rana a wajenta. Kalamansa har gobe in ta tuna su sai ta ji kamar ta mutu. _In har ni Mansoor na haifu cikin uwata Meri da uba na Ibrahim arka ko ita ka ai ta rage a duniya nan sai dai ta mutu nima na mutu ban yi ba aure ba_ _Nayi alkwarin toshe kunnuwana daga jin ta da ganinta na yi alkwarin sauya duniyata daga duniyarta, na yi alkwarin sauya mattacen mafarkina a kanta, na kuma gode maka da ka fahimtar dani darasin rayuwar da na da e ana fa a min ban auka ba, na kuma fahimci akwai tazara mai kimanin kilomita tamanin tsakanina da arka, na kuma fahimci matsiyaci kamata ya yi shisshigi wajen tusa kansa in da bai dace da shi ba. Yadda ka saka iyayena kuka a kaina kai ma wat rrana sai ka yi kuka saboda arka.._ Kara tuna hakan da ta yi yasa sai da ta saki kuka ta fa i nan saman dardunan da ta idar da sallah ta na gunjin kuka, kamar kuma wacce aka tsikari haka ta tashi ta nufi waje makeken Wardrope in dake akin acan kasa ta fara lalubo wani abu. Wata jaka ta dauko karama daga gani ta jima a boye duk ta yi kura. Sannan ta zo ta zauna ta bu e jakar ta fito da wata karamar waya kiran Nokia ta da domin an jima da daina ya yin wayar a wannan zamanin. Ta saka hannunta na rawa ta kunna wayar sai ga shi ta yi kara da wannan yar wakar ta Nokia, yadda hannunta ke rawa haka jikinta ke rawa. Ta gama saituwa wayar ta nufi ma'adanar sakonni. Tunda hatta layin wayan bata cire ba, sai da jimawar da akayi ba'a yi amfani da layin ba Mtn sun kulle layin gaba aya amma abin da ta ijiye wayar saboda shi yana nan aciki. Kuma ta je ta ara yin rigister ta sabunta layin, ita duk tunanin ta watan wata rana zai neme ta! Wata ila zai tuna da ita. Sa onsa na karshe ta bu e kuma ajikin sunan wanda ya turo sakon ne kamar haka. "Aji Na.! _Kada ki ara kirana, ki manta dani daga zuciyarki da duniyarki gaba aya. Ki auka bamu ta a sanin juna ba, soyayyarmu alkwarin mu da mafarkinmu ki saka wuta ki kona su acikin tunaninki, ki kauce ma ganina kamar yadda zan kauce ma ganinki, ki kauce ma jina kamar yadda nima zan kauce daga jin ki gaba aya. A da ne na ke hango kaina a matsayin mai sonki ina tunanin wannan soyayyar ta isa komai a wajena ashe na yi kuskure, saboda haka ki auka ma baki ta a sanina ba kamar yadda nima zan shafe ki daga tunanina da zuciyata gaba aya._ Wasu hawaye ne masu zafi ke gudu kan kunci Mimi wasu na koran wasu, har da kwanan watan da sakon ya shigo da kuma lokaci 16 ga watan March 2012, da misalin karfe 9:45pm na dare ranar Laraba. Ba zata ta a mantawa da ranar ba, tun bayan tafiyarsu take ta kiran wayarsa ta ji ya suka sauka gida da kuma jikinsa tun da sun fita Mu'azzam na rike dashi yana ingisa kafarsa sannan ga raunika a jikinsa. Ammh wayarsa bata shiga ta kira na Mu'azzam shima baya auka. Wajen kwana uku tsakani sai ta koma tura masa sakon don Allah ya kira ta. Ba ta so su yi wannan rabuwar ba, ta so ko sallama su yi da juna. Ammh Mansoor ya tabbatar da kalamansa na shafe ta daga duniyarsa. A kwana na biyar ne ya tura mata wannan sakon kuma daga kuma ranar ba'a aara amfani da layin ba. Ita kuma ta kasa daina amfani da nata layin, wayar tafi shekara biyu a kunne kuma a tare da ita, tunani take yi watarana zai iya nemanta abin da bata sani ba, sai daga baya ba ita ka ai Aji ya shafe daga tunaninsa ba har da dukkan mafarkan rayuwarsa da ya tsara tare da ita. Lokacin rabuwarsu sai da kamar Depression zai kamata daga baya ta auki dangana dalilinta na yin karatu a ibadan kenan saboda ta tsani Abuja ta kuma tsani Gombe a lokacin. Haka ta rika bin sakonnin nan aya bayan aya tana karantawa, akwai wani sako da har abada ba za ta ta a mantawa da dalilin turo shi ba. "Mimi Na nifa na fa a ma Inna da Baba aure zan yi." Inna ta ce da me zan yi aure? ni kuma na ce duk a saida gonakin Baba na mallam Sidi a nema min auran fatima bintuNa" Ta na karanta sakon tana dariya lokaci aya da kuka, ba za ta manta ookacin suna yin jarabawar fita daga babban Sakandiri ne bayan ta dawo daga makaranta. Hajiya ce ta ata mata rai akan sai ta shirya ta je gidan Daddy(Alhaji Hamza) ta kwana ita kuma ba ta son tafiya saboda Mansoor. Sai kawai ta yafo ankwalin doguwar rigan da ke jikinta ta fito haraban gidan tana kunkuni. Ta bar Hajiya aciki ita da Inna Meri ta na ba ma Hajiya Hakuri. Kamar ba za ta sai ta ganshi a gabanta cikin mamaki da zaro ta ce"Yaushe ka zo ban sani ba? Ba zata manta kayan da ke jikinsa ba alokacin tunda ranar jumma'a ce ya saka farin shadda har da hula. Yana mata irin kallonsa ya ce"Daga masallacin Jumma'a nake, na ce ba zan koma gida Mimi ba ta ga wankan Ajin ta ba." Sai da ya fa a taga darduma a hannunsa sannan ga kasa nan a saman goshinsa ya kuma bata tabbacin da gaske yake yi daga masallacin jumma'a yake. Ita fa duk damuwanta in ta gan shi sai ta ji farinciki ya cikata. Mansoor shine rayuwarta, suka tsaya suna ta hira yana bata labarin irin yadda yake wahala wajen neman makarantar sojoji tunda shi burinsa ya zama Soja saboda haka ma ya ata shekaru uku a gida bai shiga makarantar gaba da sakandiri ba. A lokacin tura bakinta tayi kafin t ace"Aji kabar wannan Sojan nan ka yi karatun ka kawai ai ba ka ta zama ba." "Ke bari Kamar yadda ba zan iya barin ki ba.Haka aikin Soja yake a wajena.." A lokacin fushi ta yi ta juya masa baya tana kunkuni kafin ta ce"To ai shike nan tunda ka fi son soja a kaina." Ta juya taa masa yar shagwa a ya yi ta kiranta ta ruga cikin falon Hajiya da gudu tana dariya. Shine da daddare ya turo mata wannan sakon na cewa ya fa a Inna aure yake so. Ta tuna har amsar da ta bashi da cewa ba Soja ka za a ba? Sakon gaba da ta karanta ne ya saka ta ara fashewa da dariya tana kuka, saboda kamar muryansa take ji alokacin yana yi mata mgana. _In ana salla ba'a mgana Mimi Na, sojan banza bari dai na fara samun ki, na tabbata in na same ki a hankali sauran burukana za su tabbata._ Kifa wayar ta yi a saman fuskarta tana raira wani irin kuka, ya za'a yi ma ta manta da shi? Ya ha a komai na bukatar kowacce mace ya yi mata wani irin son da ya ha a duka mafarkinsa a kanta. Kuka ta ke yi kamar ranta zai fita har muryanta ta sauya, sannan ta mike ta kashe wayar ta maida ta ma'adananta. Ta kuma maidata maboyarta, kuma a wajen ta dauko wani abu a nannade da kyalle ta warware shi. Sai ga hoto ya bayyana na jikin hoton yana tsaye a kamar studion ne akwai mutane a wajen. Yana sanye da kayan kwallo riga da wando ja da fari da takalmi ja mai igiyoyi. aga Kofi a sama ya na an mirmishi a kasan hoton an saka. MANSOOR AJI GOMBE UNITED CAPTAIN! lokacin da Katsina pillars suka zo suka buga wasan cikin gida suka kuma ci su da bugu uku ba ko aaya kuma duka bugun kwallon nan Aji ne ya buga su a raga. Rumgume hoton ta yi tana ji zuciyarta na bugawa sama sama. Tunaninta kuma ya tafi akan shin kamar yadda take bibiyan rayuwarsa shima ya na nibiyanta haka? Tsintar Aji a duniyar kwallon kafa ya sa ta sare ta yarda da mganarsa ya sauya mafarkinsa tuni. Ita ce shaidan yadda Aji ya so zama soja wallo ma ra'ayin Mu'azzam ne ba ra'ayin Mansoor ba, kuma ko a baya wallo bata burgeshi duk ya na buga wallo amma tasan ya na zuwa kallon wallo sosai. Sai gashi rana tsaka ta ganshi tsamo tsamo acikin ta, duk me ya faru bayan rabuwarsu? Shi ne ba ta da wannan amsar ta jima Rumgume da hoton tana kuka kafin ta gaji ta nannade hoton ta kuma maida shi ma'ajiyarsa. Sallar isha'i ta yi yunwa take ji har ta fara ganin jiri. Shi ya sa bayan ta idar da ta ji Baaba Uwani na buga mata Kofa taje ta bu Abinci ta kawo mata sai ta ce ta koma da shi ta ha o mata tea ne. Sai ta Juya ta na fadin"Binta ki fito falo Hajiya fa ta damu." Cikin dashewar