← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 208

Sashe 135

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya saka ta a cikin wani hali, ina amfani wannan jin kunyar da ya jawo mata, kamar daga sama ta ji muryaansa a cikin falonta cikin kaushi yana fa in" Ina Mimin take? Sai falon ya yi tsit, kowa na kallon kowa ciki mamakin ganinsa ba su Bintu ba hatta su Yaya Amina sun kasa mgana domin suna ganin yanayinsa a fusace yake. Kawai sai ya fita har yana bangaje Nasir akinta yana bu e ne sai dai an sakaya ne shiga cikin akin ya yi yana kiran sunanta amman shuru shi ne har bedroom inta har toilet ya le a ba kowa ya duba kayanta na cikin wardrope ya ga ba'a ta a komai ba. Sai hankalinsa ya an kwanta da sauri ya fito daga akin ya sake dawowa akin Inna sai ya iske Nasir na durkushe suna gaisawa da Inna. "Inna me ya sa kika bari Mimi ta tafi? Ji wata tambayar renin wayau haka Hibba da Bintu suka ce acikin ransu, Inna kuma ba in ciki ya sa ta kasa mgana kawai mi ewa ta yi ta shige ciki ta bar shi nan tsaye jiki a sanyaye, Yaya Amina ce ta yi gyaran murya kafin ta ce"Tun jiya Mimi ta tafi gida nima ina fa an me ya sa suka barta ta tafi? Shi ne suka ce min Inna ta ce tafi,sannan sun yi sun yi su hana ta tafiya ta ce sai ta tafi." "Is ok! duk in da ta je ma ai za ta dawo, Nasir ta shi mu je." Haka kawai ya fa a cikin bacin rai sannan ya bar akin sai ma ya fice daga gidan gaba aya. Nasir mamaki ya kama shi Aji yaushe zai yi laushi ne ya gane Annabi ya fa u? A mota ya same shi yana cika yana batsewa sai da ya shiga motar ya rufe kawai sai ya ga Aji ya ja motarsa sun bar kofar gidan. Cikin mamaki ya juya yana kallonsa kafin ya ce" Ya haka? mu da muka zo ban ha uri? Kamar ba zai yi magana ba, hankalinsa na wajen tuki sai can ya ce"Inna ta yi fushi ba za ta sauraremu ba yanzu. Sai bayan kwana Biyu in ta huce." "Ita Mimin fa? Ba za mu je can gidan Hajiyar mu ba ta hakuri ba? Kallonsa Aji ya yi na wani lokaci kafin ya ce"Itama ka yaleta, duk in da ta je ai za ta dawo tunda da aurena a kanta." Nasir ya ce"Ina mganar da ka ce ta ce tana jiran takardanta in ka i, za ta kai ka Kotu.". Cikin mirmishi Aji ya ce"Kai ka yarda za ta iya kai ni kotun? To ta kaini kotun sai a ga ni shege ka fasa." Nasir mamaki ne ma ya hana shi magana har Aji ya maida shi gida. Shi dai har cewa ya yi ya kira ta a waya.Aji ya ce ko ya kirata ta hau dokin zuciya ba za ta auka ba shi kuma ba ya son ya kira ba'a auka ba in ransa ya aci abun ba zai yi mata da i ba. Yana ijiye Nasir a gidansa ya juya kan mota ya koma gidansa. Sai da ya yi wanka ya sauya kaya sannan ya kunna wayarsa ya kira Mu'azzam. Shima dai duk mgana aya ne bai kyauta ba Inna ta ce ta cire hannunta a kan shi, shi na Innar ya fi damun shi sai kawai ya ce"Mu'azzam kar ka damu kanka, ba sai ka taho ba komai zai dai dai ta in sha Allahu." Mu'azzam ya ce"Ta ya ya? Inna ta rantse da Allah ta baza ta saka baki ba. Na yi ta kuma Kiran wayar Mimi ba ta auka ba, mun yi mgana da Baba zan shigo jibi sai mu dumguma mu je mu same ta mu ba ta hakuri." Kai Tsaye ya ce"Ni ban aike ku ba, kowa ya cire bakinsa a mgana ta da Mimi, ba kuma wanda zai je ba ta ha uri." Daga can bangaren haka Mu'azzam ya saki baki ya kasa mgana. "Ka da ka ce za ka bar aikinka ka taho, na gaya maka ka yi zaman ka, matar ka kuma za'a turo maka ita gobe, Inna na cikin damuwa ku yi min alfarman barin mata Junoir awajenta tunda an yaye shi." Mu'azzam kasa mgana ya yi sai da ya ji ya ara fa in" Is an oder Mu'azzam." Shike nan kawai ya ce ya kashe wayarsa. Baba da ya kira shi daga baya abin da ya fa amai kenan kar ma wanda ya yi yunanin zuwa wajen Mimi su bar shi da ita, shi a tunanin shi Mimi ba za ta iya dogon Fushi da shi ba za ta dawo Saboda tana son shi sannan yana tunanin in aka bita kanta zai yi girman da za ta fahimci Aji na dai dai da ita zai tsaya ya ga iya gudun ruwan ta amman da gaske ne ya yi nadama sannan yana ta tunanin shawarwarin Nasir a gare shi yana kuma tunanin gaskya ya fa a masa Kamar lokaci ya yi da zai daina ganin laifi wani a kan wasu. Saboda yadda ma bai saurari Mu'azzam ba, bai samu sanar dashi rigiman aki ba. ******** *MIMI* Mimi yadda ta kwanta da Kuka haka ta tashi da wannan kukan, Hajiya ce ke ta faman lallashinta dakyar ta yi shuru har ta samu ta yi wanka amman ta saka wani abu a cikin ta ta kasa, ji ta ke yi kamar ba ta da andano a harshenta sai da Hajiya ta nuna acin ranta sannan ta iya shan Tea shima ka an, ba ta da aiki sai kwanciya tana hawaye domin in ta tuna irin cin zarafin da Aji ya yi mata sai ta kasa tsaida kukanta. Hajiya duk ta damu ita da Baaba Uwani, ta kasa kiran kowa sai daga baya ta bi shawaran zuciyarta ta kira Alhaji Hamza ta ce ya zo gida in ya samu sarari yau tana neman shi ya ce sai zuwa dare domin baya gari ya shiga Bauchi. Mimi ta riga ta fitar da auran Aji acikin ranta a yadda ta ke jin kanta ba ta tunanin za ta iya kara zaman aure da shi, Shi ya sa ta na gani su Bintu da Hibba na kira ba ta auka ba ta ga har kiran Mu'azzam ba adadi ba ma su ka ai bakwata kwata ba ta auki wayar kowa ba. Daga karshe ma sai ta kashe wayar gaba aya tunda tana da tabbacin Shi uban gayyar ba zai kira ba, to wanda ya ce in ta tafin ma zai fi, kuma a mganganunsa babu so ko tausayi da gaske yake baya sonta kenan tuni ya daina sonta a tunanita yana sonta har yanzu ashe ashe bata sani ba shi baya wannan tunanin kanta ya aureta ne domin ya auki fansa abin da ya faru a baya shi ya sa ya ri a kuntata mata amman duk dai ta daure, Shi ya sa jauswaa suka ce IDAN AN CIZA a hura saboda kar a gaba a yi nadama ita dai ga ta cikin nadaman saurin amincewa da auran Aji da ta yi cikin gaggawa. Yini ta yi kwance a aki sallah kawai ke ta da ita. Bayan Tea in da ta sha da safe ba abin da ya ara shiga cikin ta. Baba Uwani Saboda ita ta yi alalan manja da rana amman Mimi ba ta iya ci ba, Hajiya ta ce a dama mata kunin gya a shi ne ma ta samu ya shiga cikinta a cikin kwana aya ta rame Idanuwa sun Kumbura kamar ba Mimi yar gayu ba, Hajiya kuma har waya sun yi da Mommy amman ba ta iya gaya mata wani abu ba. Sannan da yamma Yaddiko ta zo duba ta amman har ta tafi ba ta gaya mata Mimi na gidan ba, ta bari dai Alhaji Hamza ya zo shine matsayin uba a wajenta in ya Kirata suka yi mgana ila ta iya gaya masa abin da ya faru. Ta yi niyar kiran Meri amman sai ta fasa,a tunanin ita kanta Merin ya kamata ta nemeta amman shuru, ita kuma Inna Meri kunya da nauyi suka saka ba ta yi tunanin kira ba har tunanin zuwa gidan ta yi amman Kunya take ji ya sa ta rasa mafita a lokacin. Da daddaren bayan Mangariba Hajiya ta shiga akin ta iske Mimi kan sallaya da hijabi fuskar nan ba fara'a amman tana shekin damuwa. Hajiya ta tsaya a kanta ta yi shuru ta kasa mgana sai da Mimi ta gama laziminta ta mike ta na e darduman ta maida shi ma'ajiyarsa sannan ta koma gefen gado ta zauna. Hajiya tasamu gefenta ta zauna lokaci aya tana fa in" Binta ba na son ganin ki cikin wannan damuwar, kuma ni tun jiya kin kasa yi min bayanin abin da ke faruwa." Ta gama fa a cikin yar damuwa. Sai kawai Mimi ta murmusa kamar za ta yi kuka cikin sar ewar murya ta ce", Hajiya ina bukatar kaya na, ki fa a ma Mommy a kwasomin kayana daga gidan su Mansoor." Hajiya ta zaro ido kafin ta ce"Kaya fa kika ce Mimi? daman da gaske kike yi ba za ki koma ba?. Ba ta ce koma ba sai kawai ta juya ta kwanta tana fa in" Na fa a miki tun jiya Hajiya, aure tsakanina da Aji ya are." "Saboda mene? Ba ki fa a min dalili ba, kin kuma ce bai sake ki ba." "Eh bai sake ni ba! Amman zai sake ni dolen shi ballantana ma shima yana ra'ayin haka." Hajiya ta yi zuru domin Mimi rufe Idanuwanta ta yi kamar mai barci duk sai ta kasa gane kanamari haka ta mike ta fita Jiki a sanyaye bayan fitan ta Mimi ta mike zaune ta na bin bayan Hajiya da kallo. Ba za ta iya fa a musu abin da ya faru ba domin tama da tabbacin sai sun tsane shi ita kuma ba niyarta ta ata masa suna ba, su yi rabuwan Lafiya tun da baya sonta ba amfanin zaman aure domin alfarma. Ba ta san cewa Hajiya ta kira Daddy ba sai can wajajen tara na Dare har ta yi sallar Isha'i na tana kwance tana tunani Baaba
Chapter 135 · 0% Book details