Sashe 64
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Meri ta amsa da cewa"Kuma ba'a son kafiya ba a son a yi ta ba ma musulmi hakuri ya nuna kafiyarsa." Kansa na kasa ya na jin wani iri zuciyarsa na wani irin zafi sai yaji kamar a yanzu komai ke faruwa. Taruwa suka yi da na su iyayen da na shi suna ta ba shi mgana. Mommy na kukan ta na fadin farincikin Mimi ya na tare da shi ne ya taimaka mata don Allah. Inna Meri na ta faman fadin ya Sausaauta ma kamsa in kuma ya ciza ya hura saboda kada ya zo ya yi nadama. "Inna na yi rantsuwa, kina so na yi azumin kaffara ne? Ya fa a yana kokarin saka wani tunani acikin ranshi, shi ya kasa ma sarrafa yanayin da yake ciki a lokacin Mommy kuma ta tare shi da fa in"Shima har azumin kaffaran ya so ya yi Allah bai amince ba." Mirmishi ya yi mirmishin da ko inna da Baba sun jima ba su gan shi cikin wannan Mirmishin ba. "Na amince zan yi azumin kaffara a kanta, zan aure ta." Hajiya da Mommy su ka ha a baki wajen fadin"Alhamdulillah." Inna Meri kuma kallonsa take yi domin a jikinta taji ba ta yarda da maganarsa ba. Baba Damjuma kuma na ta saka albarka ya na fadi "Ko kai fa? Ai gwara ka manta komai." Mommy ta rike Hannun Hajiya tana fadin"Habibi zai yi farinciki yau ya ga Mimi ta samu abin da take so." Munafukin mirmishi ya yi kafin ya ce"Kafin nan ina da wasu sharu a guda hu u, biyu zan fa e su kafin aure. Biyu kuma zan kafa su bayan auran." Ba tare da tunanin komai ba Mommy ta ce ba komai sun amince nan take Aji y ace zai tura ma Mimi sharud an ta wayarta da amincewarta zai yi amfani daga nan ya tashi ya fice kuma bai nuna alamun wasa yake yi ba kuma bai nuna alamun ya yafe ba. Inna Meri sai ta rasa gane in da ya dosa a jikinta taji kamar ya na shirya wani abu. Hajiya da Mommy suna ta godiya,Inna Meri ta rakasu har wajen mota jikinta duk ya yi sanyi Magajiya da su Gaje kamar za su rasu saboda son jin gulma ai tunda suka ga Mansoor suka san babban abu ne ke faruwa ita kuma magajiya ta so ta gane Hajiya Shiyasa Inna Meri na dawowa daga rakasu ta tare ta da Fadin"Ikon Allah wannan kamar Hajiyar da kika yi aiki a gidanta ko? Inna Meri ba ta iya karya ba sai tace mata Eh ita ce. Daga haka ta wuce bangarenta Magajiya ta yi wani munafukin dariya kafin ta ce"A yi dai mu gani." Gaje kuma fadi take yi"Kwanaki yar ta zo yau kuma kakar da kanta anya lafiya kuwa? Harira ta ce"Da fa wata mgana, duk boyen su dai ai za ta bayyana har mu sani." Duk Inna Meri na bangaranta ta na jinsu ta ma rasa abunda ke yi mata da Baban Inna yafi ba ta mamaki wai ya amince cikin sauki haka?. Ko da ta san shima ya na sonta ba ta auka lamarin na shi zai zo da sauki haka ba. Baba Danjuma daganan masallaci ya tafi saboda ana ta kiran sallah itama daga wajen ta auro alwala ta shiga daki ta yi nata sallar. ***** Mimi ta dawo wajen aiki ta ga Hajiya da Mommy ba sa gidan da ta yi ma baaba uwani mgana sai ta ce sun fita har ga Allah ta auka suna gidan Daddy ne yasa ba ta Damu ba. Sai kawai ta kwabe kaya zafi ya isheta ta koma ta kwanta tana duba wayarta kuma Hoton Aji ta ke kallo har barci ya auketa. Sai da taji muryan Mommy na kiran sunanta sannan ta farka. Ta ga Mommy na ta fara'a amman ba ta auka wani abu ne ya faru ba. Ce mata ta yi ta tashi ta yi sallah tana tashi ta shiga tiolet wajen Mommy ta gyara mata wayarta sai ta ga Hoton da take kallo tunda wayar nata ba tsaro. Mirmishi ta yi kafin ta ce afili"Kin kusa samun abin da kike so ata." Daga haka ta ijiye mata wayarta ta fita zuwa akin da ta sauka itama kwabe kaya tayi sai da ta yi wanka sannan ta yi sallah. Dukkansu suka hadu afalo su ka ci abinci har da Mimi sai bayan sun gama ne Mimi ta kalle su kafin ta ce"Mommy ina kuka je ne? Mommy ta yi mirmishi kafin ta ce"Gidan surukan ki mana" Cikin mamaki Mimi tace"Gidan surukai na kuma? Ta fa a da sigan tambaya. Mommy ta kalli Hajiya suka yi dariya kafin Hajiya ta maida kallonta wajen Mimi dake musu kallon tuhuma da mamaki. Cikin tausasa murya Hajiya ta ce" Eh mana mun je neman gafara abin da ya faru ne a baya." Mimi ta yi wani iri da fuska kafin tace"Ban gane ba" Saboda ita dai ba ta san da mganar ba. Nan Hajiya ta zayyana mata komai sai ta tuna lokacin rasuwar Abi Mommy ta yi ta jadadda cewa kafin rasuwar Abi ya so ya zo gombe ya nemi gafaran Hajiya ashe ciki har da Ajinta a ranta sai taji wani irin sanyi da Sauri tace"To shi ya ce yafe din Hajiya? Hajiya tace"Bai yi mgana ba amman mun fahimci yafiyar sa tunda ya kar i tayin mu ya amince zai AURE KI.!" Mimi ta waro ido cikin mamaki kafin tace"Aure kuma? Cikin matukar mamaki da ka uwa ta yi tambayan. Wannan karon Mommy ce ta ja arta Jikinta tana lallashinta lokaci aya tana warware mata yadda komai ya fara ta karishe da Flfadin"Habibi kafin ya rasu ya yi ta nanata min mi yi miki abunda kike so, ni kuma nan duniya na tabbatar da yaron nan shine farincikin ki Hajiya ma ta tabbatar min da haka, kuma silan shi ne kika sa ba ma kowani namiji dama ciki har da an uwanki Jaheed kina son shi kina kaunarshi tunda kuma har ya janye kalamansa kafin rasuwar shi kina da damar ki yi rayuwar farinciki" Kafin Mommy ta gama mgana ta fashe da kuka kamar wata karamar yarinya sai ta ji kamar a mafarki. Cikin kuka take kallon Mommy Lokaci aya tana fa in"Aure fa Mommy? Kuma Aji ya ce ya amince da bakinsa? Mommy ta gya a mata kai kafin ta ce" Eh duk da yace ya na da Sharuddansa bai fa a mana ba ya ce zai tura miki da kan shi in kin amince shike nan zai yi azumin kaffara." Mimi ta ji kamar numfashinta zai auke cikin wata irin murya ta ce" Mommy ni fa na hakura tun lokacin nan da kin fa a min da ban barku kun je gidan ba." Hajiya na yar dariya ta ce"Ba ki son shi ne? In ba ki so ba shike nan ba ko ba haka ba Murja" Mommy na taya ta dariya ta ce"To tunda ba ta so miye amfani Hajiya? daman daboda farincikinta ne" Mimi na jin haka ta yi saurin cewa"Mommy...! Sai kuma ta kasa mgana sai kawai ta tashi da gudu ta shige koradin in da akinta yake ta na Rufe fuska jinta ta ke yi kamar tana yawo a saman iska. Ta shiga akinta tayi tsaye zuru ta na tunanin ko dai mafarki ne har marin kanta sai da ta yi. Ashe ashe burinta zai cika? Ashe ashe za su iya zama ma'aurata ita da Aji. Tsalle ta buga lokaci aya ta haye gadonta tana birgima nauyin da ke saman Kirjinta ya na sauka a hankali farincikin da take ji ya sa ta manta ma a inda take. Mikewa ta yi ta fara uban tsalle asaman gado ta na cilli da fillows in kan gado, ji take yi kamar ta kurma ihu duniya su san yau ta na cikin farinciki. Ita ka ai sai dariya ga hawaye sannan ta koma ta rufe fuskarta da bakinta tana yar dariya ta yarda farinciki na saka mutum ya yi hauka bai sani ba. A falo kuma bayan fitan Mimi Mommy ta ce"Mimi na son yaro nan Hajiya, ni kuma sai naga kamar shi ya daina sonta ko abunda Habibi ya yi masa ya shafe kaunarta a cikin zuciyarsa ne? Hajiya ta ce"Ba na jin haka, ina da kyakyawan yakinin kamar yadda ba ta manta da shi, shima bai manta da ita i ba, in har ya daina sonta me yasa ya kasa aure? Sannan me yasa ya amince da bukatar mu a karon farko? Mommy ta yi shuru kafin ta ce"Haka ne to ya zamu bullo ma Alhaji Hamza da sauran an'uwanta? Hajiya ta ce"Ki bar ni da shi Hamza su kuma yan'uwanta in mgana ta tabbatar sai ki fa a musu iyaka dai su kawo dogon turancin su na yaran zamani kada ki sauresu tunda dai Binta na son wannan yaron da ikon Allah sai ta samu abin da take so." Da haka su ka cigaba da tattaunawa su tunaninsu bai kai ga in da tunanin Mansoor ya kai ba, a ran Mommy sai da ta jinjina zafin kan Mansoor ba ta auka haka yake ba. Mimi ranar kasa barci ta yi sai dai barawo kila ya sace ta, washegari haka ta tashi cikin annushuwan da ta jima ba ta aciki, Mommy da Hajiya su ka fara tsokanarta da Amarya tana jin kunya Baaba Uwani na wajen ta gyara zama ta na fadin"Wai ni Hajiya kun bar ni cikin duhu, Aure Hajiya binta za ta yi ne ban sani ba? Hajiya na yar dariya ta ce"Mu na saka ran haka" Tuni Baba Uwani ta saki gu a sai da ta ranga a guda uku Mimi na jin haka tayi waje tana dariya daman a shirye take wajen aiki za ta je. Baaba Uwani har haraba ta bi ta tana yi mata kirari da Amarya hak nnan ta zazzage mata sauran ku in jakarta Baaba Uwani fa i take yi" Ko waye wannan ya yi farar sa'a, ya tsinci dami acikin akala kyakyawan mace a jari ce ballantana Binta Fatima take uwar ado da kwalliya" Mimi farinciki ya sa ta kasa rufe baki haka taja motar ta zuwa wajen aiki ranar duk wanda ya ga Mimi sai yace me ya faru da