Sashe 148
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke bu ata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. *BAYAN KWANA HU A cikin kwana hu un da suka shu e duk a daddafe Mansoor ya yi su, duk yadda ya so ya fushi da Mimi kamar yadda ya so a farko tun bayan dawowar shi daga Abuja saboda ta ba shi haushi. Sannan tunda ya fahimci wahala take son ba shi ko ta yi ramako dalilin haka ya so ya share ta ya fita batun ta ya ga dai aryan tsiya sannan kuma ya ga iya gudun ruwanta, shi ba ita ta fi ba shi baushi ba sai Iyayenta da suka zama tsoffn kawai suna kallon ta tana yawo gari gari da auransa a kanta amman a ka rasa mai tsawarta mata, ko ma me ya faru ai bai ce ya sake ta ba, ita ta ga dama ta yi tafiyarta shi kuma lokacin ransa ya aci ba zai iya tsayawa yana ba ta hakuri. Amman tunda ta tura masa sa on wai ta samu wani. Ya ji kasa sukuni maganar ta i barinsa ya zauna Lafiya barcin sa ma ragagge ne. Ba in kishi gare shi shi fa a tsarin rayuwarsa in har ya riga matarsa mutuwa Allah zai bar wasiyyan in ta sake aure bai yafe mata ba, ba zai iya aukan wannan kwamacalan ba a ce in da ya shiga ya yi nomansa wani ya shiga ya ba za ta shi hajar ba zai iya aukan haka ba. Ballantana yana raye a duniya nan Mimi ta je tana kula wani, ya fara tunanin waye ta ke nufi? Ko dai wannan sakaran an'uwan nata ne? domin ai ya san labarin shi a bakin Makama In ko hakane lalle daga Mimi har iyayenta zai aga musu hankali. Sannan ko da ya ce ba zai ara nemanta ba ya kasa, ya sake kiranta amman wayarta a kashe amman bai ha ura ba, karin abun ma ko barci yake yi sai ya ri a mafarkin ya ga Mimi da wani ta na ta masa dariya, a kwanaki nan barcinsa duk babu salama da sukuni a cikin sa. Duk yadda ya so ya nuna bai damu ba ya kasa damuwar har ta fara bayyana a saman fuskarsa baya samun cikakken barci haka za ka ganshi zuru zuru, duk kauce kaucen sa na kada a fahimci Mimi ta ci nasara a kanshi ya kasa. Duk kuma tunaninsa na ya share ta shima ya kasa tuni zuciyarsa ke rinjayansa ya bi ta can kano, wata kuma zuciyar na hana shi, amman kuma wata na tunku a shi saboda samun natsuwar shi, Ga shi har a Lokacin Inna sama sama take yi masa ya bata hakuri bai san adadi ba sai ta ce ita bai mata komai ba, ya yi mata maganar Mimi ya ce ta kwantar da hankalinta za ta dawo kai tsaye ta ce masa wannan kuma abin da ya shafi rayuwarsa ne ita nufinta ta fita a ciki, In ya neman masu mai fa a ne ya nemi dangin ubansa ita kan ta gaji da bin bayansa ba shi ka ai ta haifa ba. Har Baba anjuma ya gaji da yi mata mgana ta kafe ta ce ita wlh ta yafe masa acin ran da ya saka ta amman kuma ta i ta koma masa kamar baya. Yana ma dai zuwan gidan ne domin ya zame masa dole amman ba ya jin da in gidan kwata kwata. Sai dai saboda Junior in ya je gidan da ya gansa zai ane shi yana murnan ganinsa in ko ya ce zai fita da shi Inna ta fara fa a kenan ta ce in nesa zai yi ka da ya fita da shi, Shi dai ai na shi ban hakuri ne sai dai ya je ya yi yawo da shi cikin Camp in su, Ko kuma ya yi yawo da shi acikin mota ya na siya masa kayan kwalama da kuma kayan wasa. Ya so cikin satin da zai shiga ya je Kano duk da baya samun wayar Mimin amman hakan bai samu ba baya samun shima lokacin kansa, wani girma ne Allah ya ba shi a sanadin wannan kwallon kafa. Matasa matasa dake Gombe da zagayenta suna yawan zuwa wajen sa neman karin bayani ko wani taimako, duk da shima ya dan wallo ba ra'ayinsa ba ne sannan ba burin shi ba ne, amman tunda abin da Allah ya za a masa kenan sai ya rumgume shi hannun biyu, tunda shine komai na shi yanzu komai zai zama ko ya zama a wannan rayuwa sanadin wannan sana'ar ne a farko bai wani aukesa da wani irin Muhimmanci ba amman daga baya sai ya rike abun ya san Allah ne ya yi masa kyakyawan za i ta hanyar da bai za ta ko tsammani ba. Har satin ya are. Bai samu yanke shawara ba, a satin kuma da ya shiga suna da traninng saboda watan gaba suna da buga wasa, to duk ba ya samun zama sannan Baba ma ya kira shi kan maganar Walida da Mariya ya ce zai shigo gidan su yi mgana. Abin da ya sa ma ya yi musu shuru ba su ci Jamb ba, ya na tunanin su jira wata shekara su sake rubutawa, sai su tafi jami'ar Gombe kamar yadda ya yi ra'ayi duk da ya san Baba aure yake so su yi saboda tsarin gidan wanzamai kenan ba'a dogon karatu a gida. Suna mgana da Mu'azzam shi dai ya damu ya zo kanon nan ya yi bikon Mimin sai ya ri a nuna masa zai yi tunanin har a lokacin bai gama gaya masa ga abunda ya yanke ma ransa ba., daga baya kuma sai ya ce ko ya na son zuwa ba shi da mafita tunda wayar Mimin tana kashe ne ta ina zai iya sanin adireshin gidan yayan nata. Sai Mu'azzam ya ce ya na da lambar Dr. Sulaiman saboda tun a wajen aurin auran shi suka kar i lambar juna tun wata hira da ta shiga tsakaninsu ya gaya masa a kano ya ke aiki, to tun a lokacin ayyuka ya sa ba wanda ya neme wani a cikin su. Mamaki ya kama Aji cikin an shan kunu ya ce"Me kuka ha a da su da kake ijiyar lambobin su? Mu'azzam na dariya ya ce"Mun ha a mana, tunda Yayana na auran anwarsa ai an zama aya in sha Allahu" Uhm kawai yace domin ya ga Mu'azzam ne da Kalan dangi, har ya na cewa kada ya damu zai raka shi gidan in ya zo kanon, shi kuma ya ce bai saka shi ba, kuma ya i gaya masa ga lokacin da zai zo ya ce kuma in ya dame shi zai fasa zuwa daga nan Mu'azzam ya kama bakin shi. Bangaren su Nasir da Makama sun yi fushi sun ce in dai Aji bai ba su ha uri ba to ba za su ha ura ba. Mu'azzam ya ba su ha uri a madadin sa amman Nasir ya ce ya fita a wannan fa an ba ruwan shi, shi ko gogan ya manta da abin da ya faru suna can sun aukan ma kansu da Mu'azzam ya kara mgana sai cewa ya yi wani abu daman ya faru ne? Ya fahimci Nasir ya koya ma Makama banzan halinshi, shi yana da abubuwan da suka sha masa kai ba shi da Lokacin tunawa da abin da ya faru in kuma suna jiran ne shi ya Kira su ya ba su ha uri alhalin shi dai bai san ya yi musu laifi gaskiya su yi ta jira. Suma in fa su san halin shi kawai saka ma rai wahala ne amman Nasir na kira Mu'azzam ya ji ina aka kwana, saboda ya damu ko ya ya zai yi fushi da Aji abokatansu ba karya ba ne. Kimanin shu ewar sati biyu Sannan ya samu natsuwar kansa. Ranar Asabar da Yamma ya shiga anguwan Arawa saboda maganar da za su yi da Baba, anan ya yi sallar Mangariba da Isha'i tare da su Baba A masallaci. Su Baba Sani har suna tara shi gefe suna mai fa an zama haka ba amfani ya kamata ya ara aure, Baba Sani ya ce akwai yar abokinsa mallam mati in yana so yarinyar uwarta Jajir tunda Bafullatanace, kuma ta dauko kyan uwar ne, Baba anlami yace gwara dai ya zo ya duba a cikin anguwa in da ake ganin mutumcin ba inda ba'a ganin shi a wata tsiya ba. Duk bai katse su ba sai da su ka gama koro jawabinsu sannnan ya gyara tsayuwa yana fa in" Na gode Baba da kulawa. Amman ni ban saki matata ba, ta je gida ta huta ne amman za ta dawo soon in sha Allahu." Yasan harda ku i suke bukata a hannun shi haka ya ba su 20k kowanne suka kar a suna washe baki, duk da yana da abin da ya fi haka amman ba ya sakar musu ku i tunda yasan halinsu ba zuwa gidan suke yi su ba ma matansu a ji da i ba Sharholiyansu kawai su ke yi acikin gari shi ya sa ko kayan abinci ya gwammace ya ba ma Auwalu ya siya musu ya kai musu. A kofar gida suka samu ke ewa da Baba anjuma ya yi masa mganar Walida da Mariya ya ce zaman su ne ya ishe sa ba sun gama karatu ba? Mansoor ya ce" Eh sun gama matakin sakandiri ba, Ina so su cigaba har matakin jami'a in sha Allahu." Baba ya yi shuru kafin ya ce"A'a ni na fi son kowacce ta kama akin ta kamar sauran ayana." Mansoor ya ce"To Baba, sun samu maneman ne? Baba anjuma ya gyara zama kafin ya ce" To ban sani ba, amman abin da ya sa na kira ka kenan, ka kira