← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 174 OF 208

Sashe 174

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a wannan gidan" Shi kuma Aji ya ce"Kada ki damu Hajiya ke ma ai sai na gina miki wani gidan wanda ya ninka wannan kyau da tsaruwa." Hajiya ta ce"Shike nan kuwa an raba gardama." Haka suka zauna suna ta hira xuciyan hajiya kamar farar takarda saboda jin da in ganin Mimi na zaune lafiya da mijinta. Hana ta tafiya suka yi har dare sai da Mimi ta gama dinner suka ci sannan suka maida ta gida a tare Ranar litini Mimi ta fara fita aiki da motar ta in yana da morning traning wani lokacin ma ya na riganta fita, ko kuma su fita a tare, megadin su wani matashi ne daga can anguwan Arawa Auwalu ya samo shi, an san gidan su ba shi da matsala shi ya sa in Mimi ta yi abinci Aji ya ce ta ri a zuba masa amman fa bai amince ta ri a fita da kanta tana ba shi ba sai dai ta ijiye in ya dawo ya auka ya kai masa. Kashedi iri iri Mimi ta sha shi da za ta koma wajen aiki.Kada ta ri a mgana da maza ba ya son ta je ana haskata a gidan Tibi tana dariya kada ta manta ita matar aure ce, matar ma matar Aji. Ta san halin shi da mugun kishinsa na bala'i aikin ma ba domin Inna ta yi mgana ba da tuni ya rabata da shi, ita kuma saboda tana son aikinta ya sa take tsaka tsantaan. Tuni faman ta daina saka mayafi in za ta je wajen aiki sai dai hijabi, in kuma za ta saka mayafi sai in suna tare irin za su fita gidan Hajiya ko gidan Inna, shima sai ta masa yar shagwa a ta ce daga mota fa sai gida wane ne zai ganta ballantana ya ce wani abu, to in ta ce haka sai ya barta amman bayan haka sun zame mata kaya na ajiya kawai. Kimanin sati uku da tarewarsu. Ya auko Inna ta zo itama ta ga gida ta yi ta saka albarka Baba Danjuma ya zo tare da su Baba Sani da suka ji zai zo su ka ce suma za su zo, Mimi kuma ta yi ta hidima da su sai da suka ci suka oshi, sannan Aji ya auke su a mota ya maida su gida iyakarsa kuma daga Kofar gida shi tunda Inna ta bar gidan bai ara taka kafa cikin gidan ba Magajiyar ne baya son gani daman Inna ke kaawo shi kuma yanzu ba ta a gidan ba shi da abun auka a gidan kuma, ya auka sai ya shekara bai taka kafarsa a cikin gidan ba amman dalilin Magajiya ba ta da lafiya zazzabi da ulcer suka kwantar da ita har a gadon asibiti Inna Meri ta kira shi ta fa a masa ya bar Mimi su je dubiya tare da su Bintu ya ce a'a, ta bari in zai je sai su tafi tare daman kuma Bintu ba ta matsa ma kanta ba sau aya ta je ta duba ta gwara ma su Yaya Amina sun je sau biyu Inna kuma kullum sai ta je kuma ta yi abincin ta tafi da shi wazai hana ta? Ko an hana ta ba za ta ji ba shi ya sa yayan nata suka saka mata na mujiya. Kwanan ta uku a asibitin a ka sallamo ta, Kuma duk Aji ne ya yi hidima asibitin anta nata da take ganin ba kamar su ba su da shi gwara ma kowa ma da Saddiqu duk ya wani susuce. Lagos in ma tunda ya dawo bai koma ba, matan kuma daman duk a wahale suke Manssor din dai da Mu'azzam su ne nauyin gidan nan, Washegarin ranar da aka sallami Magajiya da daddare ya auko Mimi suka zo gaisheta shima ko asibitin bai je ba amman dai ya tura ma Auwalu 20k, Sun iske har su Zuwaira a gidan da Saddiqu da matarsa, Mimi daman ta yo abincin ta zo da shi bai hana ta ba saboda ba zai iya hanata aikin alheri ba. Amman in da ba ta ce za ta zo da abincin ba, ba zai ta a matsa mata ba, a hanya ta kuma saka shi ya siya kayan marmari ta ce ai ba za su je hannu rabbana ba. Ai ko duk sai suka yi tsuru tsuru sai ga Magajiya na amsa gaisuwan Aji da Mimi cikin rawan baki. Baba baya nan lokacin shi ya sa ba su wani da e ba. Mimi ta tura kyakyawan kulan abincin da ta zo da shi tare da ledan kayan marmarin gaban Magajiya, Saddiqu daman suna shigowa ya fice ko kallo bai ishi Aji ba. Tun bayan abin da ya faru ko ara ganinsa bai yi ba sai yau. Sai ga Zuwaira na godiya Magajiya ma na kwance tana fa in" Na gode Allah ya ji an mahaifa." Mimi ta amsa da Amin Amin dama tun shigowarsu sun gaisa da su Zuwaira. Har Maeesha na ce mata hala aiki ne ya hana ta zuwa asibiti sai ta amsa mata da cewa wallahi, har yarinyar sai da ta auka kafin su tafi, ta fahimci Maeeshan na so ta kara shige mata ne tunda har ofar gida suka rako su ita da zuwaira. Suna shirin tafiya sai ga su Baba anjuma da an'uwasa Baba anlami ya ce ya kamata Mimi ta shiga ta gaida su Gaje ai Baba Baba anjuma ne ka ai uban mijinta ba. Shi ya sa Mimin ta shiga gidan ta gaida su Gaje sun kuma ji da i kwarai duk da ba ta wani da e ba,.Suna hanyar komawa gida yaron Gwaggo Yalwa ya kira wayar Aji ya na gaya masa jikin Gwaggon ya ta shi kwana biyu, a tunanin Mansoor Inna ma ba ta sani ba saboda bai ji ta yi masa mganar ba sai kawai suka biya daga nan wajen Inna ya gaya mata halin da ake ciki sai ta ce daman ta kwana biyu ba ta je ba ya kamata ta shirya ta je ta duba ta, Aji dai ya ce ba zai samu halin zuwa ba amman ya na tunanin in ya samu sarari sai su tafi tare da Mimi tun da ba ta ta a zuwa ba. Haka ko a ka yi, Inna ya yi ma shirin tafiya da ku in mota da abin da za ta je da shi, ita ka ai ta tafi, Walida ka ai aka bari a gida da farko har Mimi ta ce ta dawo gidansu ta zauna kafin Innar ta dawo. Gogan ya ce a'a bai gama cin amarcinsa ba. Ko ta koma gidan Bintu ko kuma a nemi wata mafitar to sai ga shi ma Mariya ta ce za ta zo ta ya ta zama har Inna ta dawo tunda jikin Magajiyar da sauki, shike nan sai a ka samu mafita Inna Meri kuma ta je ta iske jikin Yalwa sai a hankali daga kwana hu u sai ga ta ta yi sati amman tana waya da ayanta suna jin halin da ake ciki. Ta ce za ta an kwana biyu saboda ta kula da Yalwan an kaita asibitin Bauchi, Baba Yakubu ma ya taimaka, a gidansa suka sauka ana ta faman hidiman asibiti. Ganin Inna Meri sama da sati biyu ba ta nan ya sa suka yi magana da Mu'azzam gwara ya je Bauchin ya duba su, sun shirya tafiya tare da Mimi amman kuma sai zuwan su Mommy ya sa tafiyar da ita bai yu yu ba, shima a ranar bai tafin ba sun yi Meeting sai a washegari amman a daran sun je gidan Hajiya sun gaida Mommy da Inna Zainaba kano ta fara sauka shi ne suka ariso gamobe tare. Mimi ta yi mamakin ganin yadda Aji ya zauna suna ta hira da Mommy kamar ba shi ba daman Dr shima ya gaya mata suna waya sosai, balle Daddy da sai dai ta ji ya ce mun yi mgana da Daddy ya ce ya na gaishe ki. Washegari ya kama hanyar Bauchi tare da Yaya Halima da ta tambayi izini a ka barta sun je sun iske jikin yalwa da sauki amman duk ta rame Inna da matan Baba Yakubu ke kula da ita ciwon sugar ne bai kwana ba a ranar ya juyo amman nan ya bar Yaya Halima za su dawo da Inna nan da kwana uku, tun da nan gidan Baba yakubu za'a bar Yalwa saboda tana zuwa ganin likita sai zuwa gaba in ta ara murmurewa sai ta koma tunda can Karimu ma yana fama da kansa ne, ayan Gwaggo Yalwan ma kowa na ta kanshi da iyalansa ne. ***** Bayan wata aya. 02:20AM. Suna amkame da juna, ba su da e da samun natsuwa ba, sun yi wanka sun tsarkake jikinsu saboda babu kyau zama cikin najasa, sun lullu e jikinsu da bargo har zuwa cikin su, kansu na kan matashi guda aya sun kuma juya suna fuskantar juna bayan sun kamkame juna kamar za'a raba su, Mimi nata wasa da suman kan Aji ba tare da ta yi mgana ba amman sun taru sun yi shuru suna jin bugun numfashin juna akin ya yi duhu amman akwai iskar fanka ka an ka an yana hurasu lokaci aya yana yawo da labulen window in bedroom in Aji. Kitso Mimi take yi masa sai ta yi sai ya warware duk ta yamutsa masa gashin kai, da ya gaji ya ri e mata hannuwa lokaci aya yana fa in" Yarinya ta ga gashi ba irin na ta ba." Dariya ta yi masa ta na shafa kitson dake kanta a wajen aiki Aisha Farida ta yi mata da kuma ta ce a wajen aiki aka yi mata sai ta tuna diraman da suka kwasa tsakanin da Aji fa a ya fara yi mata me ya sa ta je ta bu e gashinta gaban maza, an ta a yin wani kitso ne a wajen aiki ban da wulakancin? Ta yi masa bayanin a wani ke antattacen waje ne maza ma basa shigowa amman ya kasa ganewa amman ya garga eta kada ta sake yin irin haka baya so, dole ta koma tana ban hakuri domin ta manta waye take aure shi ya sa ta ba shi wannan labarin. Hannunsa
Chapter 174 · 0% Book details