← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 208

Sashe 71

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Magajiya ma akinta akwai Jumma da Zuwaira sai dai ba su leko ba su gaje ma suna bangaren domin su ji yadda aka kwana. An shigo da katan katan in ruwa da lemu da su samosa da aka ba su acan Baba Sani masu ha ama sun kwashe kusan duka su ka bar ka an Baba anjuma bai damu ba ya ce a diba a kai ma mallam hashimu gida. An yi girki bangaren Inna Meri jallop in shinkafa kuma an aika duka sasan gidan minti dai sai daga Baya Inna tace sai ta siya ta raba duk wanda ya ganta zai gane tana farinciki yau burinta tana tunanin ya kusa cika na kusa ganin auran Baban Inna. A bangaren Mimi ma kamar hakane sai ta ga abun kamar wasa san da ta dawo gidan Hajiya ke fa a mata ta yi hamdala da godiya ga Ubangiji Mommy ta fara kira itama daman tana shirin kiranta ne ta yi mata fatan alheri sannan ta ba ta hakuri tace kada ta damu da su khadi za su sauko nan da wuri kafin lokacin bikin, har Mommy ta ba ma Asma'u su ka yi mgana Mimi tace ta na nan shigowa Abujan karshen watan da su ke ciki. Ranar ta kwana salla da nuna godiya ga Ubangiji da gaske bakinciki na saka kuka haka ma farinciki, sannan in farinciki ya yi maka yawa sai barci ya kaurace ma idanuwan ka. Ta rasa da wa za ta yi sharing farincikinta sai kawai ta tura ma Rukky sako. "Baby am Engaged" Da asuba ta tura mata sa o sai ga kiran Rukky kuma lokacin barcin da ba ta samu ta yi ba ya kwasheta Rukky ta yi ta kira ba'a auka ba arfe bakwai na Safe sai ga ta a gidan Baaba Uwani na madafi tana abun karyawa tace Hajiya na dakinta tana lazimi Mimi kuma ba ta fito ba. akin Mimi kawai ta wuce kai tsaye ta same ta kan sallaya tana barcin ta sai ji ta yi an sakar ma ta duka a cinyarta a firgice ta mike tana sosa wajen lokaci aya tana kallon Rukky. Yamutsa fuska Mimi ta yi kafin ta ce"Rukky miye haka? Cikin Jin Haushi Rukky ta ce"Ke menee gaskiyan sakon da kika turamin? Sannan ina ta kiran ki ba ki auka? Mimi ta mike tsaye tana mika kafin ta ce"Am Serious zan yi aure nan da Wattanni biyu Baby" Sai ji ta yi Rukky ta rumgumeta tana Murna fa i take yi" Am so happy for u Mimi jaheed dai ya ciri Tuta." Da Sauri Mimi ta tureta daga jikinta kafin ta ce" Wani Jaheed Sai Rukky ta tsaya kallonta kafin ta ce" bashi ba ne? To wa ye? Mimi ta ka a ido sama kafin ta ce"Da wanda ya dace mana." Rukky ta yi zuru kafin ta zaro ido ta ce " Ba dai da wannan ba in mutumin mai bakar zuciya ba? Aji ko? Ko ba haka ba ne sunan da kike kiran shi ba? Mimi ta ka a kai Lokaci aya tana zama gefen gado kafin ta ce" Shi baki ba Halittan Ubangiji ba ne? Ki kuma daina kiransa mai bakar zuciya domin baki san shi ba Rukayya." Yadda ta fa i mganar ne yasa Rukky ta yi shuru tana mamaki kafin ta koma ta zauna kusa da Mimi tana fa in"How? ta ya ya hakan ya tabbata? A gajarce Mimi ta sanar da ita komai itama idon ta zaro kafin ta ce"Ji wani mganar banza a wani gidan za ki zauna? Gidan yawa ne fa daga jin sunan gidan nasu? "Yes! And so? Rukky ta kura ma Mimi ido kafin ta ce"Mimi an ya kina da Hankali kuwa? In so hauka ne hakuri ma ai magani ne" Mimi ta ce"Ni nawa haukan son ba shi da mgani Rukky, mganin shi guda aya na auran na da Aji Aji shine maganina." Sai Rukky ta kasa mgana hmm kawai ta ce kafin ta jinjina kai ta ce" Kamar ki ace sadaki wai dubu Hamsin Mimi? " Ya yi ka an ne? Ai ni nace ma ya yi yawa ba domin ma shi sadakin ya zama dole ba da ban kar a ba." Mimi ta bata amsa a Dldakile sai Rukky ta gya a kai kafin ta ce"Ni kam me ki ka ga ni a jikin wannan ba in mutumin ne? Ni dai ban ga wani abu na musamman ba Mimi." "Daman ba ke ya dace ki san shi in na Musamman ba ne Rukayya. Ni da ya dace na sani kuma na san Aji na mussaman ne." Mimi ta katseta bayan ta ba ta amsar ta saka Rukky ta ga mganar ta koma da Zafi sai ta bar mganar ranar daman Mimi ba ta da aiki a gida za ta huta ba ta wani jima ba ta tafi, Sai dai ta leka akin Hajiya sun gaisa itama Hajiya ke kara fa a mata an saka ranar Mimin ta ce sun yi mgana da ita. Tana tafe a hanya tana tunani me ya sa Mimi ta cika taurin kai ne? Ta yi hakurin shekarun baya ma ballatana yanzu ita fa ba ta ga abun so a wajen wannan ba, ba wani abu na musamman tare da shi sai bakar zuciya da ba ar fuska. Gani take yi Mimi ta saukar da darajanta sam wannan nutumin bai dace da Ajin rayuwarta ba, ba ma ha i ko da take ganin yanzu shima yana da kudi amman ba ku in ba cancanta da nasabar za ta duba kamar Kwa on bai yi tsari ba. ****** A group insu nasu biyar Mu'azzam ya shiga ya rubuta" Guys babban shagali na tunkaro mu Aji zai yi aure" Da rana to duk suna wajen aiki sai can da yamma Nasir ya gani sun kan jima ma ba su yi mgana aciki ba. Aji ma da ba'a saka shi a lissafi ko sannu bai ta a cewa ba. Nasir da ya karanta emojin dariya ya turo kafin ya ce"Kai Mu'azzam mu fa ba abokan wasanka ba ne, Sai dai in so kake daman ka tsokani Yayan na ka." Mu'azzam ya fito ya ce" Am serious fa nan da wata biyu Nasir." Sai Nasir ya turo emojin zaro ido kafin ya ce" Wai da gaske? Ban yarda ba." Ya auka wasa ne ganin Mu'azzam bai ara mgana ba sai kawai ya tura cewa" Mu'azzam kai da Aji kila sai ya naushi bakin ka in yaga fatan da kake yi masa." To sai can dare da Misalin goma na dare Mu'azzam na gidan Mansoor suna tare ne ma a lokacin ya shiga group in sai ya ga sa on Makama da ya yi tagging in mganarsa. " To in dai da gaske ne, gidan boka ta kai sunan Aji." Ahmad ya zo ya sako emojin dariya shima Mu'azzam na gefen Mansoor shima wayar ce ke hannunsa amman ba lalle ya kunna data ba. Sai ya kunna vioce note ya fara mgana da cewa" Da gaske ne fa yau muka je aka saka rana nan da wattani biyu kun ji ma na rantse." Sai ya tura Mansoor na jinsa bai ko Juyo ba sai shine yavce"Ba ka ji ni da abokan ka ba ne? Mansoor sai ya cigaba da abunda yake yi sako yake son tura ma Mimi amman sai ya rubuta sai kuma ya goge ya yi haka ya kai sau biyar. Mu'azzam ne ya kunna Vioce sai ya ji muryan Nasir na fa in" Wai daman da gaske ne? lallai to ta maganar makama ne wannan yarinyar ya kamata a sara ma malaminta aikinsa na kama da yankan wuka." Mu'azzam ya fashe da Dariya sai ka yi ya yi typing. " Kusan ma wace ce? Mimi ce fa" Shuru ba su yi mgana ba sai kawai ya ga Nasir ya hadl a group vioce call kuma dukkansu hu un suna online ban da Aji. Mu'azzam sai ya aga ya saka a speeker yana na dariya Sai ji ya yi Nasir na Fa in "Mu'azzam ba ma yar wasa? wata Mimin? Ko dai mai irin sunanta ne? Ahmad ma ya ce" Nima ina tunanin mai irin sunanta ne." Makama kuma yace"Ni na kasa mgana ma" Mu'azzam na shirin mgana kawai Aji ya zuro jikinsa ta baya ya ce" Ku dai magulmata ne, miye kuke wani rawan jiki? Sai ya ji sun auki Ihu gaba ayansu suna kiran sunan sa. "AJI..! AJI..!" Mirmishi ya yi kafin ya ce" Abin d Mu'azzam ya fa a muku gaskiya ne, kada ku damu ba sai kun yi wani shiri ba ni aurin auran ma ku yi zaman ku, ba zan yi gayya ba." ga haka ya mike zai bar akin sai ji ya yi Nasir ya buga Ihu har da fito kafin ya ce" Ku na gidan Aji ne? Mu'azzam ya amsa masa da eh, sai ji ya yi ya na cewa ga shi nan zuwa domin ba zai iya barin sai gobe ba a ce ya ji yadda abun nan ya faru ba. Mu'azzam na ta dariya Ahmad da Makama a ka bar Mu'azzam na yi musu bayani Mansoor ya dawo akin ya shiga wanka bayan ya fito ya fita falo ya na motsa jikinsa har a lokacin ya na jin hiran Mu'azzam da su Ahmad. Ba jimawa sai ga Mu'azzam ya fito ya ce Nasir ne ya zo bari ya je ya bu e masa kofa Mansoor ya yi kasa e bai ce komai ba amman a ransa ya na jinjina shaharan Nasir a son jin gulma. *Janafty* *INZB2003* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT SHIN KINA DA LABARIN MACCE MAI GYARA DABAN TAKE GA ZUCIYA MIJIN TA, MUNA DA KAYAN MATA MASU ZAFI NA BUGAWA GA JARIDA HAJIYA TA KUDI DA KUDI AKE NEMAN SU INA MASU FAMA DA MATSALA RAMA BA GABA BA BAYA KINA ZAUNE ANA KWATANCI DAKE KINA CI BAKI KOSHI MUNA DA MAGUNGUNA DA ZUMA 3 IN 1 KIBA BRST HIPS TA CIKO MIKI KU INA KIYI FRESH MUNA DA KWAYOYI MUNA DA GARI DUK MASU CIKO JIKI NE KIYI DUM INA MASU FAMA DA MATSALA BRST KU TSUHU YAFI
Chapter 71 · 0% Book details