Sashe 48
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dukar da kai tana kuka fa i ta ke yi "Kabiru wlh ka auki hakkin wannan yaron kuma in har bai yafe maka ba sai Allah ya isar masa" Yaddiko sai salati ta ke yi ganin Yadda Sojoji su ka maida hallitar Mansoor. Alhaji Hamza kuma ya ma kasa magana bai auka rashin imanin Yayan nasa ya kai haka shahara ba, shi ko tsoron ya kashe shi ba ya yi. Hawayen Inna Meri da na Mu'azzamu na iga a saman fuskar Mansoor su suka taimaka har ya iya bu e likakkun idonsa guda aya ya na kallon iyayensa suna kuka saboda halin da ya saka su, yunkurawa yake yi kamar ya tashi amman kuma ya kasa sai da Mu'azzam ya rike shi sannan ya iya tashi zaune, amman dauriya ce shi ka ai yasan halin da yake ciki. Major Kabir kuma sai mirmishin mugunta yake yi kafin ya ce"Zan kyale yaron ku saboda Hajiya amman ba domin haka ba da sai ya raina kansa, amman ko yanzu ya san karo da Soja ba wasa ba. Sannan akwai shara in da zan kafa muku da in har ya tsallake su anan gaba sai dai shi ya mutu wlh." Inna Meri da Baba anjuma har suna karo da Juna wajen ara dukawa gaban Major Kabir, suna rawan bakin sanar da shi sun amince kuma Mansoor zai yi biyayya ga Shara in sa. Major Kabir ya nuna Mimi da yatsa kafin ya ce"Ba shi ba a ta, ko kallonta ya kara yi in na sani sai na lalata rayuwarsa, sannan ya sani kada ya kara min wannan tsaurin ido Mimi tafj karfin talaka kamarsa wanda har ubansa ya bar duniya bai shigo birni ba, Kuma ni ba zan iya aura ma ata Agolan da rayuwarsa ba ta da wata mamora ba, daga yau sai yau na raba wannan alaqar ba shi ba a ta ba rayuwata in kuma ya ki ji to Wlh a karo na biyu har ku mutu ba za ku kara ganinsa ba domin sai na atar da rayuwarsa, Kuma ba zai bar wajen nan ba sai ya duka ya nemi gafara ta kamar yadda kuka yi yanzu in kuma har yanzu bai yi laushi zan saka shi ya yi laushin." Ya fa a ya na nuna Sojojin da ke baya sun kame, Inna Meri har tana rawan baki riko hannun Mansoor ta kamkame tana fadin"Darajar haihuwar ka da nayi Mansoor ka bu e baki ka ba shi ha uri saboda ka tsira da rayuwarka." Mansoor kukan zucci ya ke yi zuciyarsa na wani irin suka, yana ji kamar ya zama asarrare mara amfani, duba yadda Mahaifiyarsa da wanda ya zame masa uba da aninsa suke kuka saboda shi, kalli yadda suke duke gaban wani hallita na Ubangiji saboda shi , yau saboda shi an kira sunan mahaifinsa an zage shi da gorin ya mutu a kauye bai taba shiga birni ba, shi ba yana kukan dukan da ya ci ba ne da dai ya ba ma wannan mugun hakuri gwara ya kashe shi, Shi ko da wani suna zai iya kiran kalmar Soyayya? Tun jiya ya ke son yaji ya tsani Mimi acikin ransa amman ya kasa, ji yake yi kamar ya mutu ba inciki da yake cikin zuciyarsa tunda ya zo duniya bai ta a tsintar kansa aciki ba. Ba shi da niyar saduda ya so ne su bar shi ya kashe shin in dan har zai iya, Sai dai Kukan Inna Meri da na Baba anjuma tare da Mu'azzam suna masa magiyan ya bashi hakuri saboda ya tsira Inna Meri ta san halin abin da ta haifa yasa a fusace ta ce"Ko ka bashi Hakuri ko na ce sai ka biyani Nonona da ka sha" Baba anjuma ya kira sunanta da karfi cikin tashin hankali. "Meramu.." Hajiya ma sai da ta kira sunanta ita kuma ta yi hakane saboda ya ba da hakurin ta san halin Baban Inna da kafiya sai yace sai dai a kashe shi. Kuma hakan da ta yi sai a ka samu masalaha domin Mu'azzam ya rike sa ya durkusa saman gwiwiyonsa tare da Iyayensa kansa na kasa ya na jin taruwan hawaye acikin idanuwansa, ko dukan da aka yi masa bai saka shi kuka irin wannan tozarcin ba muryansa ba ta fita ma sosai Saboda wahala ya furta" Ka yi hakuri..!" Yana gama fa in haka sai ya ji wasu hawaye masu zafi sun sauko masa. Nan Major Kabir ya Koma ya zauna yana Fa in"Good. za ku iya tafiya da shi amman ya kiyaye sharu ana. Inna Meri da Baba anjuma suna rawan jiki masa godiya su ka mi jiki na rawa Hajiya nauyi da kunya su ka hanata mgana Alhaji Hamza ne ya ce su tsaya mana a nema musu Jirgin komawa da sauri Baba anjuma ya ce"Mun gode da karamci ranka ya da e ya isa haka." Hajiya ta yi saurin kallon Major kafin ta ce"Kabiru ka dubi halin da Binta ke ciki Hausawa su ka ce idan An ciza a hura watarana kada ka zo kana nadamar abunda ka aikata ma wannan yaron" "Ni? Kamar ni Major Kabir My Daughter ta auri talaka Agolan da ubansu har ya mutu a can wani kauyen kurmus, uban rikonsa wanzami uwarsa yar aiki? Over my dead body Mimi za ta yi wannan auran askanci ba ta isa ba, ko za ta mutu bazan aura mata wannan talakan ba, jinin takalawa wanda bashi da wata kyakyan makoma ko anan gaba." Ya karishe fa a a fusace kamar ba da Hajiya ya ke mgana ba, kawai sai ta girgiza kai kafin ta ce"Shike nan Allah ya hana mu jin kunya watarana." Ta fa a ta na kallon yadda Idanuwan Mimi suka kumbura saboda kuka, Mommy ma sharan kwallan take haka ma Khadija kowa kuma yasan ba'a kyauta ba, amman kowa yana tsoron ya yi mgana wanda bai girmama maganar uwar da ta haifesa ba ai ba wanda kuma ya isa ya yi masa mgana ya saurare shi. Mu'azzam ya ri o sa tunda ba ya iya tsayuwa gefe kuma Baba anjuma ya kama shi za su fita daga falon da gudu Mimi ta wace daga jikin Mommy ta arisa gaban Abi cikin kuka Ta ce. "Abi ka yi hakuri Abi ina son shi don Allah kada ka raba mu da juna" Cikin tsawa Ya ce" Sai dai ki mutu, amman Wallahi tallahi ba za ki auri wannan talakan yaron nan ba, ba shi da makoma mai kyau, ina tambayan walin karatun shi Hajiya na gayamin iyakarsa Secondary school. Soja yake son zama ire iren su ma ba su da wani rabo a duniya." Mimi ta katse shi cikin gunjin kuka tana kara fa "Abi ina son shi.." "Ke yarinya ce Mimi, karatu nake so ki yi ba yanzu zan yi miki aure ba" Ya fa shima bayan ya katseta cikin kaushin Murya. "Abi Ina son shiiiii..." Ta fa a cikin wani irin karyayyen sauti kamar za ta shi "Murja ki auke min Mimi kada raina ya aci na fasa kanta da bindigata" Ya fa a ya na kokarin sarrafa fushin sa domin ji yake yi kamar ya tokareta ta fa i in ta na ha a shi da wannan antaccen yaro nan mara makoma mai kyau. Ba zai manta da wannan kukan da ta rika yi lokacin da mahaifiyarta ke rike ta ba, har gobe yana jin Sautin wannan kukan acikin kirjinsa. Ya tuna ta na mi o hannunta Mahaifiyarta da yayarta khadija suka ri e ta suka tafi da ita zuwa cikin wani aki. Yayi okarin danne abin da ke taso masa amman sai ya kasa, kafarsa ya makaleta ya kasa tafiya da ya sa su Mu'azzam su ka tsaya su na kallonsa ba su san abin da zai aikata ba da ba su barshi ya kara yin mgana ba. Sai juyawa kawai su ga ya yi ya na faman ingisa kafa idanuwansa a like ga kaya duk sun yage ba hula ba takalmi kamar wani almajiri cikin muryan da ta galabaita ya fara fa "In har ni Mansoor na haifu cikin uwata Meri da uba na Ibrahim arka ko ita ka ai ta rage a duniya nan sai dai ta mutu nima na mutu ban yi ba aure ba," Ya fa a ya na sakin numfashi Inna Meri na kokarin toshe masa baki amman sai da ya ida sa fa in abunda ke ransa a lokacin. "Nayi alkwarin toshe kunnuwana daga jin ta da ganinta na yi alkwarin sauya duniyata daga duniyar ta na yi alkwarin sauya mattacen mafarkina a kanta, na kuma gode maka da ka fahimtar dani darasin rayuwar dana da e ana ga ya min ban auka ba, na kuma fahimci akwai tazara mai kimanin kilomita tamanin tsakanina da arka, na kuma fahimci matsiyaci kamata ya yi shisshigi wajen tusa kansa in da bai dace da shi ba, yadda ka saka iyayena kuka a kaina kai ma watarana sai ka yi kuka saboda arka." Yana gama fa in haka ya juya kamar zai kifa saboda yanayin jikinta Major Kabir ya yi wani kayattacen mirmishi kafin ya ce" Ku ja ma an ku kunne, na ga alaman tsageranci na damunsa sannan ku yi masa iyaka da ata domin ruwa ba sa'an kwando ba ne, zan sake shi na yanzu amman ko kallon Mimi ya sake yi sai na aure shi da kakin jikina." Baba Danjuma bakinsa na rawa ya ce"Ba ma zai kara kallonta ba In sha Allahu ka yi hakuri." Haka su ka fita da Mansoor a rirri e da shi saboda halin da ya ke ciki, kuma ba wanda ya bi bayan su. Shima Major in mikewa ya yi a fusace ya shige cikin akinsa har yana banko kofa Hajiya ta bi shi da kallo tana Sassauta fushinta domin kada ya zama masifa ga rayuwar Kabiru. Amnan ita ta so da aka Ciza sai a Hura saboda ba'a san abunda gobe za ta haifar ba. Ko kwana ba su yi a Abuja ba Hajiya ta ce gida zata koma, Mimi kuma ta zauna wajen mahaifinta ba za ta kara amsar ta riko ba tunda ga abunda ya biyo ba, Mommy ta yi tayi Hajiya ta kwana Hajiya ta rantse ba za ta kwana ba. Hajiya na ba